25/04/2026
Jerin wasu daga Daliban Sheik Dr. Abduljabbar (H) da suke gabatar da Karatuttuka a Fadin Nigeria.
Ya k**ata Al'umma musamman masu goyawa Azzalumai baya su fahimci Sheik Abduljabbar (H) Zinare ne a wannan Kasa ba abin wulakantawa bane.
Human Rights Watch
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Abba Kabir Yusuf
25/04/2026
Alhamdulillah!
Malam dai ya hannata case a hannun wannan lauya da Kotu ta bashi shawarar ya hannatawa mutum ne me Amana sai yan makaranta a shagala da ruwan Hasbunallahu wani'imal wakilu da cigaba da kaiwa Allah kuka.
25/04/2026
SOURCE: Mujamma'u Ashabul Kahfi warraqeem
23/04/2026
CIKAKKEN RAHOTON SHARI’A | Zaman Kotun Ɗaukaka Ƙara kan Shari’ar Sheikh Abduljabbar
RANA: 23 Afrilu, 2026
WURI: Kotun Ɗaukaka Ƙara (Court of Appeal), Kano
TAƘAITACCEN BAYANI (Executive Summary)
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta gudanar da zama domin sauraron ƙorafin da Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara ya shigar. Bayan nazari kan ƙa’idojin shari’a da tsarin doka, kotu ta mayar da hankali kan ingancin ɗaukaka ƙarar da kuma bin matakan doka kafin sauraron muhimman hujjoji. A ƙarshe, kotu ta sallami ƙarar tare da bada umarnin a mayar da shari’ar zuwa kotun ƙasa domin ci gaba da sauraron shari’ar bisa doka da oda.
CIKAKKEN RAHOTO NA ZAMAN KOTU
1. Bayyanar ɓangarori a gaban kotu:
Kotun ta fara da tambayar mai ɗaukaka ƙara ko yana da lauya. Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara (Appellant) ya bayyana cewa yana kare kansa ba tare da wakilcin lauya ba.
A ɓangaren gwamnati kuwa, Barrister Bashir ya bayyana kansa a matsayin lauya mai kare martanin Gwamnatin Jihar Kano (Respondent), tare da gabatar da abokin aikinsa.
2. Matsayin kotu da huruminta:
Mai shari’a (Presiding Justice) ya jaddada cewa wannan babbar kotu ce mai hurumin sauraron ɗaukaka ƙara daga kotunan ƙasa, kuma aikin kotun shi ne duba hukuncin da aka yanke a ƙananan kotuna bisa tsarin doka.
3. Batun gabatar da ƙara da takardu (Record of Appeal):
Kotun ta tunatar da mai ɗaukaka ƙara cewa duk wani ƙorafi dole ne ya kasance cikin tsarin da doka ta tanada, wato ta hanyar takardun ɗaukaka ƙara (Record of Appeal).
Kotu ta bayyana cewa:
a) Takardun ƙara su ne tushen shari’a a wannan mataki.
b) Ba a sauraron bayanai kai tsaye, sai an bi tsarin da doka ta tanada.
4. Ka’idojin doka kan gabatar da ƙara:
Kotun ta yi nuni da tanadin doka (Order 19 na dokokin kotun ɗaukaka ƙara), wanda ya baiwa mai ƙara ko lauyansa damar shigar da bayanai cikin ƙayyadadden lokaci, sannan a ba shi gajeren lokaci (ƙasa da mintuna 15) domin gabatar da muhimman hujjoji.
Akwai cigaba a comment ............
23/04/2026
Sheik Dr. Abduljabbar (H) yau a Kotu!
Hakika Masoya Annabi (s.a.w) suna farinciki da ganinshi tare da fatan Allah ya tabbatar da nasara ya fito da wannan Jagora mai girma.
22/04/2026
Masoya Annabi (s.a.w) mu dage da yiwa Sheik Abduljabbar (H) Addu'a.
Allah ya bashi Nasara akan Azzalumai.
22/04/2026
ALHAMDULILLAH Rahama ta sauka a Kano !
Kotu Ta Sa An Dawo Da Sheikh Abduljabbar Kano Daga Gidan Yarin Kuje
A yau Laraba ne aka tabbatar da isowar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, zuwa birnin na Dabo, biyo bayan umarnin Kotun Daukaka Kara.
An dauko malamin ne daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, inda yake tsare, domin ya samu damar bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis (gobe) don ci gaba da shari’ar da ake yi da shi.
Idan ba a manta ba, a zaman kotun da ya gabata a makon nan, Sheikh Abduljabbar ta bakin wakilan sa ya nemi kotun da ta ba shi damar kare kansa da kansa tare da bayyana a gaban alkalai don gabatar da hujjojinsa, k**ar yadda dokar kasa ta tanada.
Bayan duba bukatar tasa, Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Kano ta ba da umarnin a kawo shi kusa, domin ba shi damar gudanar da kare kansa yadda ya k**ata ba tare da wani tsaiko ba.
Ana sa ran cewa zaman na gobe Alhamis zai dauki hankalin jama'a da dama, ganin cewa wannan ne karon farko da Sheikh Abduljabbar zai sake bayyana a gaban kotu a Kano tun bayan yanke masa hukunci da wata kotu tayi a 2022.
13/04/2026
13/04/2026
TAKARDAR TUNI AKAN TAKARDAR ME TAKEN "LETTER OF FURTHER COMPLAINT REGARDING THE APPEAL NO. CA/KN/01/2025. SUIT NO. K/93CA/2022. BETWEEN ABDULJABBAR SHEIKH NASIR KABARA — APPELLANT AND KANO STATE GOVERNMENT — RESPONDENT"
~Maulana Ameerul Wa'izeena (H)
Abba Kabir Yusuf
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
28/02/2026
A Jiya ne Mahaifiyar Jagora Sheik Dr. Abduljabbar (Hafizahullah) ta cika Shekaru 11 da rasuwa.
Allah ya Jadadda Rahama agareta 🙏
26/02/2026
BUDADDIYAR WASIKA
ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO DA KWAMISHINAN SHARI’A
Zuwa ga:
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano:
Alhaji Abba Kabir Yusuf
Da kuma
Mai Girma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano:
Barr. Abdulkarim Kabiru Maude SAN
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Muna mika wannan budaddiyar wasika gare ku ne cikin ladabi, girmamawa da biyayya, a madadinmu na daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, domin bayyana damuwa mai zurfi kan halin da ake ciki dangane da shari’arsa da tsarewar da ya shafe lokaci mai tsawo yana ciki.
Mai girma shugabanni, ba bu wata shakka cewa kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya da dokokin kasa sun tanadi hakkin kowane dan kasa da ake tuhuma da laifi na a yi masa shari’a cikin adalci, gaskiya, da kuma ba tare da jinkiri mara dalili ba. Wannan hakki ba wata alfarma ba ce daga hannun gwamnati, illa hakki ne na doka da ya wajaba a kiyaye shi a kowane lokaci.
Tsawaita tsare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ba tare da kammala shari’arsa ko bayar da cikakken damar kare kansa a gaban kotu ba, na ci gaba da haifar da damuwa, tambayoyi da rashin fahimta a zukatan al’umma, musamman ma mu dalibansa da masoyansa da ke kallon ku a matsayin shugabanni masu kishin adalci, gaskiya da bin doka.
Muna son a fahimce mu karara cewa ba wata alfarma muke nema ba. Abin da muke nema shi ne:
Idan akwai tuhuma a kansa, a ba shi cikakkiyar dama ya kare kansa cikin tsari na doka;
Idan kuma babu isasshiyar hujja, a yi abin da doka ta tanada cikin gaggawa.
A matsayinku na shugabanni da aka damka wa amanar rayuka da hakkin al’umma, muna rokon ku da ku duba wannan al’amari da idon basira, adalci da tsoron Allah, domin tarihi yana rubuta dukkan matakan da shugabanni ke dauka, kuma al’umma na kallon yadda ake tafiyar da shari’a da adalci.
Har ila yau, muna so mu ja hankalinku cewa rashin samun adalci na gaskiya na iya haifar da takaici, yanke kauna da rashin amincewa a zukatan matasa da al’umma gaba daya. Mu a matsayinmu na dalibai da masu goyon bayan Sheikh Abduduljabbar, muna nan kan tafarkin doka, zaman lafiya da biyayya ga hukumomi. Amma kuma muna da hakkin dimokuradiyya na bayyana ra’ayinmu ta hanyar da doka ta amince da ita.
Muna fatan ba za a kai ga wani yanayi na nuna rashin amincewa ta hanyoyin siyasa a nan gaba ba sak**akon jin an tauye adalci. Abin da yafi dacewa shi ne a tabbatar da gaskiya da adalci sun yi rinjaye tun yanzu, domin hakan shi ne ginshikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba ku ikon yin abin da ya dace, Ya kuma shiryar da mu baki daya zuwa ga gaskiya, adalci da zaman lafiya.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Sa hannu:
Daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
(Ta hannun As’habul Kahfi Multimedia)
Rana:
26 Fabrairu, 2026
Amnesty International
Amnesty International Nigeria
Human Rights Campaign
26/02/2026
OPEN LETTER
TO THE EXECUTIVE GOVERNOR OF KANO STATE AND THE HONOURABLE COMMISSIONER OF JUSTICE
To His Excellency, the Executive Governor of Kano State
Alhaji Abba Kabir Yusuf And The Honourable Commissioner for Justice, Kano State
Barr. Abdulkarim Kabiru Maude, SAN
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
We respectfully present this open letter to you, with utmost courtesy, respect and obedience, on behalf of ourselves, the students of Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, in order to express deep concern over the current situation regarding his trial and the prolonged detention he has been subjected to. Your Excellencies, there is no doubt that the Constitution of the Federal Republic of Nigeria and the laws of the land guarantee the right of every citizen accused of an offence to be tried with justice, fairness, and without undue or unjustified delay. This right is not a favour granted by the government, but a legal entitlement that must be upheld at all times.The continued detention of Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, without the conclusion of his trial or the full opportunity for him to defend himself before a court of law, continues to generate concern, questions, and confusion in the minds of the public, especially among us, his students and followers, who regard you as leaders committed to justice, fairness and respect for the rule of law. We wish to make it absolutely clear that we are not asking for any special privilege. What we are asking for is simply this:If there are charges against him, he should be given full and unfettered opportunity to defend himself within the framework of the law;And if there is no sufficient evidence, then the law should be allowed to take its proper course without delay.In your capacity as leaders entrusted with the protection of lives and the rights of the people, we appeal to you to look into this matter with insight, a sense of justice and fear of Allah, for history records every step taken by leaders. and the public is watching how justice and the rule of law are being administered Furthermore, we wish to draw your attention to the fact that the absence of true and visible justice can breed frustration, despair, and loss of confidence in the hearts of the youth and the general populace. We, as students and supporters of Sheikh Abduljabbar, remain firmly committed to the path of lawfulness, peace, and obedience to constituted authorities. However, we also have a democratic right to express our views through lawful means recognised by the law.We hope that we will not reach a situation where political expressions of dissatisfaction may arise in the future as a result of a perceived denial of justice. What is more appropriate is to ensure that truth and justice prevail from now, as this is the foundation of peace and stability.We pray that Allah, the Most High, grants you the ability to do what is right, and guides all of us towards truth, justice and peaceful coexistence.Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.Signed:
Students of Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara
(Through As’habul Kahfi Multimedia)Date:
26 February, 2026
Human Rights Watch
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Abba Kabir Yusuf
04/02/2024
Yau Shekara 4 kenan da Kulle mana Masallaci Karkashin Azzalumar Gwamnatin data gabata.
4/2/2021 itace ranar da Gwamnatin Kano ta bayar da Umarnin rufe mana masallacin da muke gudanar da ibadar mu gwargwadon fahimtar mu wacce dokar kasa ta bamu yancin yin hakan.
Ta dakatar da Malamin mu da karantar damu Addinin mu yadda muka gamsu da muyi shi kuma dokar kasa ta bamu dama Amman Gwamnatin Kano ta haramta mana.
Idan baku manta ba Gwamnatin Kano karkashin ganduje ta jagoranci rufe mana masallaci ne badan lefin komai ba sai dan kiran da Malamin mu yayi a shekarar 2019 lokacin zaɓe akan kada Ganduje ya bari a kunnawa Kano wuta ya faɗi zabe ya hakura ya faɗi kada da sunan Inconclusive ya bari ya tarwatsa Kano.
Wannan shine lefin Malamin mu a wajen Gwamnatin Kano ta wannan lokaci.
Daga karshen wasan abunda muke son sanar daku shine bayan da Ganduje ya bawa sarki yola umarnin karɓar dukkan Masallatan mu da niyar in gawuna yazo ya dankawa wani mutum dake zaune a unguwar kabara da sunan Masallatan na Qadiriyya ne a yanzu haka sanadiyar karɓar Masallatan da hanamu tasarrufi dasu an samu wasu yan iska mara mutunci sun shiga sun sace dukkan wani abu na amfani acikin waɗannan Masallatai k**a ga sifiku,solar,fankoki da dukkan wasu abubuwan masallatan.
Gidan Malamin mu dake jami'ur rasul kuwa ko cokali basu bari acikinsa ba, haka zalika a yanzu haka akwai wani mara imani da yake gini a filin masallacin jami'ur rasul kuma yanzu haka Gwamnatin Kano da kotun data karɓe wajen suna gani basu ɗauki wani mataki a kai ba.
Muna rokon Allah duk me Hannu a rufe waɗannan wurare dama zaluncin da ake ɗan-ɗana mana Allah ya rufe masa kofofin samun Rahamar sa da dukkan wata kulawa tasa.
~Mujamma'u Ashabul kahfi warraqeem Nigeria
4/02/2024