02/04/2024
GA MASU NEMAN DAUKAKAR DUNIYA DA LAHIRA….
Ya zama tilas a bautawa Allah, sannann a kyautatawa iyaye, saboda kyautatawa iyaye biyayya ne ga umarnin Allah, sanan kyautata musu yana kawo wa mutum cigaba a rayuwarsa, kuma yana da kyau mutum ya rinƙa yi wa iyayen sa addu’a a koda yaushe tare da kyautatawa ’yan uwansu da abokansu da sadar da zumunci a tsakanin su, sawawun iyayen naka suna raye ko basa raye.
Idan mutum ba ya kyautatawa iyayensa, duk abin da ya ke nema a rayuwarsa ba zai taɓa samu ba, zai rinƙa shan wahalar banza ne kawai a rayuwarsa, kuma duk abin da ka yi wa iyayen ka, kai ma sai an yi maka kwatankwacinsa koma ninkinsa, don haka brother shimfidawa iyayenka fuka-fukan rahama, kaima Allah zai shimfida maka rahamarsa.
Ubangiji ka jiqan iyayenmu da rahama da gafara, kasanya haske da sanyi da kwanciyar hankali tare da aminci a cikin makwancinsu, ka kyautata namu qarshe bayan nasu Ya Hayyu Ya Qayyum.
Professor Isa Ali Pantami
Abdussamad Tijjani Sani✍️