29/08/2026
Lokacin da Annabi Musa (A.S) tare da mutanensa s**a isa bakin teku, alhali maƙiyansu suna biye da su a baya, sai s**a ce:
﴿إِنَّا لَمُدْرَكُونَ﴾
“Tabbas za su riske mu!”
Amma Annabi Musa (A.S) cikin cikakkiyar yarda da Allah ya ce:
﴿كَلَّا إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ﴾ 🤍
“A’a! Haƙiƙa Ubangijina yana tare da ni, kuma zai shiryar da ni (zuwa mafita).”
Wani lokaci muna kallon halin da muke ciki, sai mu rasa hanyar tsira. Amma Allah na buɗe ƙofar mafita daga inda ba mu zato.
Ya Allah! Ka azurta mu da haƙurin da ba ya ƙarewa, da yaƙinin da ba ya girgizuwa, da zuciyar da ko a mafi tsananin lokuta za ta ce:
“A’a! Haƙiƙa Ubangijina yana tare da ni, zai shiryar da ni zuwa mafita.” 🤲🏻🤍