لماذا تتعلم اللغة العربية ؟
Bayān Arabic Academy
Founded by: Dr. Nasir Ashir (PhD in Arabic Language)
Bayān Arabic Academy
A modern Arabic learning platform dedicated to teaching Arabic language, grammar, literature, and linguistic studies in a simple, elegant, and academic way.
04/06/2026
Kalmar: صبر
Ma’anarta: Haƙuri.
A rayuwa da addini tana da muhimmanci sosai.
Ka yi comment da wata kalma da kake so.
01/06/2026
1 - Na fahimta.
2- Ina fahimta.
3- Zan fahimta.
Ya zai kasance idan ina son na ce tabbas na fahimta?
31/05/2026
The Founder & Director, Bayān Arabic Academy
Wannan kuskure ne da yawancin ɗalibai suke yi…
Suna koyon kalmomi ba tare da amfani da su a jumla ba.
Mafi kyau: Koyon kalma + sentence + practice.
Idan kana son gogewa a Larabci, toh ka gwada wannan hanyar...
Abin da yake hana mutane iya Larabci shi ne…:
Yawancin mutane suna tunanin dole sai sun haddace littattafai da kalmomi masu yawa kafin su iya Larabci.
Amma gaskiya ita ce: Ba haddacewa kaɗai ce take kawo ƙwarewa ba.
Abin da ya fi muhimmanci ga wanda ya ke son ya iya Larabci shi ne:
1- Listening kullum.
2- Practice kadan-kadan.
3- Laƙantar kalmomi masu amfani.
4- Maimaitawa yau da kullum.
Ka fara yau ba tare da jira ba.
Mutane da yawa suna rikicewa wajen sanin bambanci tsakanin: علم Da: عرف
Dukansu suna da alaƙa da sani.
Amma:
علم = ilmi mai zurfi.
عرف = sanin abu ko mutum.
Shin za ka iya sanya su a cikin jumla mai ma'ana?
TARE DA KALMOMIN ALQUR'ANI MAI GIRMA
Kalmar: تقوى
Ba wai tsoron Allah kawai take nufi ba.
Tana ɗauke da:
Tsoron Allah.
Kiyaye dokokinSa.
Nisantar saɓo.
Kusanci da Allah.
Shi ya sa wannan kalmar take da zurfin ma’ana sosai.
Shin za ka iya rubuta mana Ayar da kalmar (تقوى) ta zo a cikin Alqur'ani Mai Girma?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
BUK Road
Kano