Cikakken bayani akan tsarikan ajujuwan koyon Turanci na makarantar A.M.T Massive College.
A.M.T Massive College
A.M.T. MASSIVE COLLEGE is a unique learning environment where people seek for education and skills.
Let's learn the differences among: buy, bye and by.
10/11/2025
Alhamdulillah!
Cikin hotuna: taron bikin yaye dalibai kenan wato (graduation ceremony) da makarantar .M.T Massive College tayi na daliban bangaren aikin jarida wato Professional Diploma In Mass Communication.
Taron ya samu halartar manyan baki daban-daban ciki kuwa harda jagoran wannan makaranta wato Jour. Abdurrahman Muhammad Na'ibawa da mataimakinsa Comrade Usaini Rabi'u Umar (Mr. Dashing) dama ragowar kafatanin malaman sassan wannan makaranta. Muna mika ban gajiya ga kowa.
Ga masu sha'awar karantar ilimin aikin jarida (Professional Diploma In Mass Communication) yanzu haka an fara daukar sabbin dalibai, sai a tuntubi wannan lamba domin karin bayani 08025281388.
29/09/2025
Tuna Baya Taron A.M.T Massive College Na Cikarta Shekaru Hudu Da Kafuwa.
Mun fara daukar sabbin dalibai masu son karantar aikin jarida
(Professional Diploma In Mass Communication).
08025281388
22/09/2025
Alhamdulillah!
Daliban makarantar A.M.T Massive College kenan bangaren koyon aikin jarida (Mass Communication) wadanda aka tura su gidan talabijin na ARTV tare da wadanda aka tura su gidan rediyon Liberty domin neman sanin makamar aiki (SIWES).
Wadan nan hotuna an dauke su ne jim kadan bayan kammala ziyarar dubawa (supervision) da shugaban makarantar Jour. Abdurrahman Muhammad Na'ibawa tare da mataimakinsa Comrade Usaini Rabee'u Umar s**a kai musu.
Alhamdulillah daliban sun samu kyakkyawar shaida ta tarbiyya tare da jajircewa wajen koyon aiki.
Allah ya kara daukaka wannan makaranta ameen summa ameen.
20/09/2025
Wasu daga cikin daliban makarantar A.M.T Massive College kenan bangaren koyon aikin jarida wato (Mass Communication) da s**a kammala dalibar sanin makamar aiki a kafar yada labaran S. Radio dake nan Kano.
Wannan hotuna an dauke su ne jim kadan bayan kammala ziyarar dubawa (supervision) wacce jagoran makarantar Jour. Abdurrahman Muhammad Na'ibawa ya kai musu.
Allah ya kara daukaka wannan makaranta ameen.
Muna sanar da dukkan wanda yayi registration na bangaren koyon Turanci cewar gobe za'a fara karatu.
Ga masu son shiga ku tuntubi wannan lamba 08025281388.
Alhamdulillah, Abba Isah Yakasai kenan guda cikin daliban makarantar A.M.T Massive College bangaren karatun aikin jarida wato (Mass Communication) wanda yanzu haka yake aiki a Radio dake nan Kano.
Allah ya kara basira ameen.
11/07/2025
SPECIAL GET TOGETHER.......
Shortly after a special get together organized by the top most officials of AMACIAN ENGLISH CLUB a students' English practicing forum under A.M.T Massive College.
May Allah the Almighty uplift the dignity of A.M.T Massive College.
10/07/2025
A.M.T Massive College & FM Kano......
Hukumar makarantar A.M.T Massive College ta kai ziyara ta musamman ga tashar Dala FM Kano. Shugaban makarantar Jour. Abdurrahman Muhammad Na'ibawa tare da mataimakin Comrade Usaini Rabee'u Umar sune s**a jagoranci wannan ziyara tare sauran jami'an wannan makaranta.
A yayin ziyarar hukumar wannan makaranta ta samu kyakkyawar tarba daga shugabannin sassa daban-daban na wannan tasha ciki kuwa harda shugaban tashar baki daya wato Jour. Ahmad Garzali Yakubu (Baba Gaza) dama sauran ma'aikatan tashar.
Cikin hotuna: daga tsakiya shugaban tashar Dala FM Ahmad Garzali Yakubu, daga dama kuwa shugaban makarantar A.M.T Massive College Jour. Abdurrahman Muhammad Na'ibawa, a dama kuwa mataimakin shugaban makarantar Comrade Usaini Rabi'u Umar.
✍️10 July, 2025.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Website
Address
MAIN OFFICE, Unguwa Uku Zaria Road Beside Tarauni Secretariat Kano State, Nigeria. , , OTHER BRANCH, Na'ibawa Dan Hassan Road Behind First Bank Of Zaria Road
Kano