03/05/2022
EID MUBARAK TO OUR ESTEEM FELLOWERS.
Taqabbalallahu minna wa minkum ❤
Much love fam ❤
MOTTO: TO OBTAIN A USEFUL KNOWLEDGE.
03/05/2022
EID MUBARAK TO OUR ESTEEM FELLOWERS.
Taqabbalallahu minna wa minkum ❤
Much love fam ❤
HAUSA VERSION
Assalamu Alaikum Masoya shirin Hannu Daya dama tashar Aminchi Radio.
Ina farin cikin sanar daku cewa na chanza sunan wannan dandali zuwa DAN LUKUTI VIDEOS sakamakon wasu shirin barkwanci dana fara shiryawa wanda yake nuna irin fadi tashi da matasa suke domin samun ingantaccen rayuwa cikin salon yaudara na zamani. Ku kasance tare dani MUSA LABARAN (Dan Lukuti) domin samun shirye shirye mu.
MUN GODE!
ENGLISH VERSION
Peace be upon you respected followers of my radio program popularly known as “HANNU DAYA” and also followers of AMINCHI RADIO.
I am very pleased to announce to you the sudden change of the page name to DAN LUKUTI VIDEOS because of the comedy videos i am producing that showcases the struggle and hustling youth engage themselves for a better living due to hardship and unemployment. Please stay tune with me MUSA LABARAN (Dan Lukuti) to get our exclusive comedy videos.
THANK YOU!
31/08/2021
AFRIKA A YAU (GHANA)
Wasu daga cikin Hausawan ƙasar Ghana sunfara ƙorafi cewa haryanzu basuga labarin ƙasarsu ta Ghana ba a shafin facebook na Aminci Radio.
To a wannan rana kuma abin yazo kanku domin mun tsallako ƙasar Ghana.
Ghana ta kasance ƙasa ta farko a Sub Sahara African da ta fara samun 'yancin kai a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1957.
Ghana dai ta kasance tana daga cikin ƙasashen da suke a yammacin nahiyar Afrika.
Musa Labaran (Dan Lukuti)
31/08/2021
AFRIKA A YAU (SENEGAL)
Wannan shi ake kira da Tafkin Retba mai abin mamaki dake ƙasar Senegal.
Ita dai ƙasar Senegal ta kasance tana Arewa maso Yammacin Afrika.
Wannan Tafki dai wani lokacin haka yake za a ganshi da kala-kala a samansa inda akwai abin da ake kira (Pink) da kuma (Lac Rose).
Daga Babban Birnin Senegal wato Dakar zuwa tafkin tafiyar Kilomita 30 ce, kuma wannan Tafki yana Arewa maso gabashin birnin na Senegal.
Musa Labaran (Dan Lukuti)
Allah ya gafarta mana zunuban mu don alfarmar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallah.
Sakon tunatarwa daga Shugaban shirye shirye na Aminchi Radio; Baffah Abubakar Abdulkadir.
10/06/2020
Aminchin Allah ya tabbata a gareku masoya mabiyan wannan shafin mu na AMINCHI RADIO/HANNU DAYA.
Nine naku MUSA LABARAN, jagora kuma mai gabatar da shirin HANNU DAYA wanda muke tattauna batutuwa wanda s**a zama ruwan dare a cikin al ummar mu.
Ana tsaka da cutar Corona virus, sai kuma ga wata annoba wacce ta zama barazana ga rayuwar mata wato . Shin menene mafita daga wannan yawan da yake faruwa a kasar mu Nigeria... RA'AYIN KU.
15/03/2020
Aminchin Allah ya tabbata a gareku.
Sunana MUSA LABARAN, jagora kuma mai gabatar da shirin "Hannu Daya" daga tashar Aminchi radio 103.9FM.
Da ruwana.....
Da ruwan ka.....
Da ruwan ki.....
Da ruwan mu.....
Da ruwan ku wajan tallafawa gwamnati....
Karfa ku manta cewa muna da rawa da zamu taka domin kawo cigaba mai daurewa a jahar mu da kuma kasar mu.
28/08/2019
Assalamu alaykum
Ku kasance da Aminchi Radio a duk ranar alhamis misalin karfe 4:00pm na yamma domin jin sabon shirin "Hannu Daya" wanda muke tattauna batutuwa da s**a zama ruwan dare tare da kungiyoyi masu tallafawa gwammati.