Madarasatul Ubayyu Bin Ka'ab Tahfizul Qur'an Gama

Madarasatul Ubayyu Bin Ka'ab Tahfizul Qur'an Gama Domin samun in gantaccen Ilimi

15/10/2025
13/08/2025

Ubayyu Bin Ka'ab Tahfizul Qur'an Gama *B*

12/08/2025

LOKACI SHINE RAYUWA

Shaykh Bin Bazz yace:

Duk wanda ya halakar da lokacinsa to ya halakar da rayuwarsa, wanda kuwa ya halakar da rayuwarsa zai yi nadama, kuma nadamar ba za ta amfaneshi ba.

المجموع الفتاوى:16/261

22/05/2025

_*KUSAKURAN DA AKE TAFKAWA GAME DA SALLAR JUMA'A*_

_Ranar Juma'a Rana Ce Daga Cikin Ranakun Mako, Wacce Ubangiji Ya Fifita ta Akan Dukkan Sauran Ranakun. Sannan Ya Ke6anceta Da Wasu Falaloli da Bai Sanyasu Cikin Sauran Ranakun ba._

_Daga Cikin Abubuwan da Ubangiji Ya Fifita Ranar Juma'a Akan Sauran Ranaku Akwai Kasantuwar A Cikinta Ne Aka Halicci Annabi Adam, Kuma a Cikinta Ne Aka Sauko Dashi Wannan Duniyar, Sannan Kuma a Cikinta Ne Za'ayi Tashin Alƙiyama._

_Sannan Allah Ya Fifita Yinin Juma'a da Darenta da Cewa Duk Wanda Ya Mutu a Cikinsu, Ubangiji Zai Tsareshi Daga Azabar Kabari. Kamar Yanda *Manzon Allah (ﷺ)* Yayi Bayani a Cikin Ingantaccen Hadisinsa._

_Har Ila Yau Allah Ya Ke6anci Ranar Juma'a da Sallar Juma'a, Wacce Akeyinta Raka'a Biyu a Maimakon Sallar Azahar. Wannan Sallar Tanada Ladubban da Ya Dace Dukkan Musulmi Ya Kiyayesu domin Samun Cikakken Ladan Sallatarta ba Tare da Samun Tawaya ba. Sannan Akwai Kusakurai da Ake Aikatawa da Suke Haramtawa Mutum Samun Ladanta ma Gaba Ɗaya. Daga Cikin Waɗannan Kusakuran Sun Haɗa Da:_

_*1. JINKIRIN ZUWA SALLAR JUMA'AR DA ƘIN BARIN SIYE DA SIYARWA:* Yana Daga Cikin Kusakuran da Ake Aikatawa Ranar Juma'a Shine Rashin Zuwa Sallar Cikin Lokaci, Wanda Gaggauta Zuwa Sallar Wajibi Ne Kamar Yanda Ubangiji Ya Faɗa Cikin Littafinsa:_

*(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ)*
{الجمعة: ٩}

_*“Yã Ku Waɗanda Sukayi Imani, Idan Akayi Kiran Sallah Na Ranar Juma'a Kuyi Gaggawa Zuwa ga Ambaton Allah (Sallah) Ku Bar Cinikayya; Wannan Shine Alkhairi Gareku In Kun Kasance Kuna Sani”.*_
_(Jumu'ah: 9)_

_Har Wayau Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

عنْ أَوْسِ بْنِ أَوْسٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *«مَنْ اغْتَسَلَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَبَكَّرَ وَدَنَا وَاسْتَمَعَ وَأَنْصَتَ كَانَ لَهُ بِكُلِّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا أَجْرُ سَنَةٍ صِيَامُهَا وَقِيَ

Address

Kano
GAMA

Telephone

+2348066555087

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madarasatul Ubayyu Bin Ka'ab Tahfizul Qur'an Gama posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Madarasatul Ubayyu Bin Ka'ab Tahfizul Qur'an Gama:

Shortcuts

Share

Category