Sheik Yusuf Abdulwahhab Yar Gaya

Sheik Yusuf Abdulwahhab Yar Gaya

Share

Domin Kawo muku karatukan Malam

27/07/2026

*RABON GADO A SAUKAKE*

*DARASIN NA 6 (25-07-2016)*

بسم الله الرحمن الرجيم

*ALHAMDULILLAH*

Muna kara godiya ga ALLAH (S. W. T) da Ya kawo mu yau don cigaba da darasin mu na Rabon gado.

```Tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu ANNABI MUHAMMAD (S.A. W) da alayensa da sahabban sa da wadanda s**a bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako```

BAYAN HAKA

Yau darasin namu,yana da matukar muhimmanci GA duk dalibin da yake son ya koyi Yadda ake rabon GADO.

Wato dai,zamu magana akan:-

*AL-ANZARUL ARBA'A*

*AL-ANZARUL ARBA'A*

Sune wasu *Ginshikai/Turaku guda hudu(4) wadda malamai ke amfani dasu wurin saukake lissafi wurin rabon gado.

*WADANNAN ABUBUWAN GUDU GUDU(4) DA ZAMU TATTAUNA/BAYANI AKANSU YAU*

Ana amfani dasu wurin gano yadda ya kamata a raba gado (asalin gado) da kuma warware matsaloli na lissafi a gadon ya yake da yawa

*A TAKAICE YAR-UWA MAI ALBARKA*

Matukar mutum ya fahimce su da kyau ya kuma iya aiki dasu to zai samu sauki matuka wurin fahimtar yadda ake rabon gado cikin sauki.

*AL-ANZARUL ARBA'A GUDA HUDU(3) NE:-*

Sune kamar haka:-

👉1- TAMAASUL

👉2- TADAAKHUL

👉3- TAWAAFUQ

👉4- TABAAYUN

*YANZU BARI MU SAUKE SU,DAYA BAYAN DAYA*

Mu yi bayani gwargwadon fahimta,idan lokaci ya isa zamu yi dukka gudun(4n),in lokaci ya kure zamu tsaya Daga baya Sai mu karasa

ALLAH YA TAIMAKE MU

*KAFIN MU FARA*

Kowannenmu ya Tino farillan da aka kaddara a AL-QUR'ANI,irinsu 1/2,1/3 DA SAURANSU.

To bayananmu zamu dinga tsakuro Bayani a kansu

👉 *1. TAMAASUL*

Tamaasul 👉 Yana nufin kamanceceniya.

*Shine a samu lambobi guda biyu ko fiye da hakan kuma su zama iri daya,a cikin kason da aka kaddara a AL-QUR'ANI.*

To anan hukuncin shine Sai mu dauki guda daya muyi aiki da ita a wajen rabo ko abunda ZAMU YI rabo da ita.

Ga misalai:

2 da 2
3 da 3
6 da 6

*YAR-UWA MAI ALBARKA*

Idan muka lura da lambobin da muka kawo a sama zamu ga cewa iri daya ne, to kawai sai muyi aiki da daya daga cikinsu

*MISALI NA 1*

Gadon da aka rasu aka bar

Miji
Shakikiya

*GA ABINDA KOWANNEN SU ZAI SAMU:*

Idan muka koma kason da AL-QUR'ANI yazo da shi,ga yadda abun yake:-

Miji=1/2
Shakikiya=1/2

Kinga kenan mun samu TAMAASUL(KAMANCECENIYA)

A tsakanin lambobin dake qasar *Farillan guda biyu (1/2 DA 1/2).*

Lambobin su ne 2 da 2.
To yanzu sai ki Dauki daya daga ciki kawai.

Sai ki raba 2,ki BAWA:-
MIJI Kaso 1
Shakikiya Kaso 1

*1+1=2*

*MISALI NA 2*

Gadon da aka rasu aka bar

Li'ummi 3
Shakikiya 2

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU*

Li'ummi 3= 👉1/3

Shakikiya 2= 👉 2/3

Yanzu Nan,yar-uwa

Kinga kenan mun samu TAMAASUL(KAMANCECENIYA) a tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin su ne 3 da 3

*YANZU SAI KI DAUKI DAYA DAGA CIKIN 3n*

Ki raba kaso 3,ki bawa:-

LI'UMMAI 3 = KASO 1

SHAKIKIYA 3 = KASO 2

*SAI KI TARE KASON WAJE DAYA*

*1+2=3*

*👉 2. TADAAKHUL*

Shine 👉 A samu lamba guda biyu ko fiye sannan kuma babu *tamaasul(Kamanceceniya)* a tsakanin su,

Amma kuma daya daga cikin Lambobin zata IYA shiga cikin dayar kuma ta fito ba tare da an samu ragowa ba.

*YAR-UWA MAI ALBARKA*

Hukuncin anan shi ne,Sai mu dauki babbar lambar sai muyi amfani da ita. Ga misalai

4 da 2
6 da 3
4 da 8

Da sauran irinsu su

*YAN-UWA*

```Idan muka lura da misalan da muka kawo a sama,zamu ga cewa a layi na farko

Tsakanin 4 da 2 babu tamaasul(Kamanceceniy),

Amman kuma 2 zata iya shiga cikin 4 ta kuma fito babu ragowa.

To wannan shi ake cewa TADAAKHUL```

*YANZU BARI MU DAN BADA MISALI*

Koda guda BIYU(2) NE:-

*MISALI NA 1*

Gadon da aka rasu aka bar:-

Miji

'Ya

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU:*

Miji= 👉 1/4

'Ya=👉 1/2

YANZU IDAN MUKA LURA DA KYAU.

Kinga kenan mun samu *TADAAKHUL(DAYA TA SHIGA CIKIN DAYA, BA'A SAMU RAGUWA BA)* Tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune *4 da 2*

*YANZU SAI MU DAUKI 4,MU YI AIKI DA ITA*

Kamar haka:-

*Za'a Raba kaso 4*

A BAWA:-

MIJI Kaso 1

Ya Kaso 2

Jimillar:-
*1+2=3*

Daya ya RAGU,Sai a Kai BAITUL MAL
4-3= 1

*MISALIN NA 2*

Gadon da aka rasu aka bar:-

Uwa
Li'ummai 2

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU,KAMAR HAKA:-*

Uwa= 👉1/6
Li'ummai 2= 👉 1/3

YANZU KENAN ZAMU DAUKI 6,SABIDA ITA CE BABBA KUMA 3 ZATA SHIGETA BA'A SAMU RAGOWA BA

*'YAR-UWA YANZU*

Kinga kenan mun samu *TADAAKHUL(WATA ZATA IYA SHIGA CIKIN WATA BA'A SAMU RAGOWA BA)* A Tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune 6 da 3.

YANZU SAI MU DAUKI 6 MU YI RABONMU DA ITA

*ZA'A KASA KASO 6*

A BAWA:-

UWA KASO 1

LI'UMMAI 2 KASO 2

Alhamdulillah
Zamu KWANA ANAN ZAMU KARASA Ragowar a DARASI NA 7

WALLAHU A'ALAM

✍️ RUBUTAWA
ADAMU KABIRU YARGAYA
25-07-2026

27/07/2026

*RABON GADO A SAUKAKE*

*DARASI NA 7 (27/07/2026)*

Assalamu Alaikum

Alhamdulillah

Muna kara godiya mara adadi da misaltuwa GA ALLAH Madaukakin Sarki

Bisa sake bamu dama,don kawowa YAU

*TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABIN RAHMA ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

Kamar yadda sanarwa ta gabata

Yau zamu dora karatunmu ne

DAGA wajen da muka kwana a darasin da ya gabata

IDAN YAN-UWA ZASU TUNA

MUN KWANA NE Muna Bayani akan:-

AL'ANZARUL ARBA'AH

Kuma mun YI BAYANI A na

1 DA 2

Yau da yaddar ALLAH

Zamu karasa Bayani akan Ragowar 2n da s**a rage

ALLAH muke roko ya saukaka mana fahimtarsu

Aamen

GA su kamar haka:-

👇👇

👉 *3. TAWAAFUK*

Tawaafuk 👉 yana nufin dacewa.

Shi ne ya kasance an samu lambobi guda biyu ko fiye sannan kuma ya zamana babu tamaasul ko tadaakhul a tsakanin su.

Amma kuma ya kasance akwai wata lamba da za ta iya shiga cikin kowanne daga cikin su ta fito kuma babu ragowa.

Wannan lambar da zata iya raba su ita ake cewa:-

*MAHALLUL ITTIFAAQ.*

Anan sai mu dauki daya daga cikin lambobin mu raba shi da MAHALLUL ITTIFAAQ

Abinda muka samu shi ne wufuqi,

Sannan SAI mu buga shi da daya lambar,

Abinda muka samu dashi za mu yi aiki.

Ga misalai
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

👉 4 da 6

👉 6 da 8

👉 4 da 10
Da sauran su

A misalin farko wato 4 da 6 , MAHALLUL ITTIFAAQ din shi ne 2.

*Yanzu Ga abinda za muyi wurin nemo lambar da za a yi amfani da shi*

Zamu CE:-

4÷2 = 2×6=12 (2 da muka samu anan bayan mun raba 4 da 2 ita ce wufuqi),

12 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani.

*Ko kuma mu ce:*

6÷2=3×4=12 (3 da muka samu bayan mun raba 6 da 2 itace wufuqi),

12 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani wajen rabo

*GA MISALAI*

👇👇👇👇

*MISALI NA 1*

Gadon da aka rasu aka bar:-

Mata

Uwa

Da

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU:-*

Uwa= 1/6

Mata= 1/8

Da= Asibci

Yanzu Kin ga kenan mun samu *TAWAAFUQ*

Tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune 6 da 8.

Sai mu nemo MAHALLUL ITTIFAAQ dake tsakanin su, shi ne 2.

*Ga abinda za mu yi*
👇👇👇

*6÷2=3×8=24* (3 anan ita ce wufuqi),

24 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani.

*KO MUCE:-*

8÷2=4×6=24 (4 anan ita ce wufuqi),

24 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani.

*MISALI NA 2*

Gadon da aka rasu aka bar:

Mata

Li'ummiya

Dan Li'abbi

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU:-*

Mata = 👉 1/4

Li'ummiya = 👉 1/6

Dan Li'abbi = 👉 Asibci

*YAR-UWA*

Yanzu kinga kenan mun samu TAWAAFUQ tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune 4 da 6.

Sai mu nemo MAHALLUL ITTIFAAQ dake tsakanin su, shi ne 2.

Ga abinda za mu yi

👇👇👇

*4÷2=2×6=12* (2 anan ita ce wufuqi),

12 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani

*KO KUMA MUCE:-*

*6÷2=3×4=12* (3 anan ita ce wufuqi),

12 kuma ita ce JUZ'UL SAHMI da ita kuma za mu yi amfani

YANZU SAI NA 4

NA KARSHE

👇👇

👉 *4. TABAAYUN*

Tabaayun 👉 shine a samu lambobi guda biyu ko fiye sannan kuma babu:-

👉 Tamaasul
ko
👉 Tadaakhul
ko
👉 Tawaafuk

*A tsakanin su, gabadaya babu wata alaka a tsakin su.*

*HUKUNCIN ANAN*

shi ne mu buga lambobin da junansu abinda muka samu dashi zamu yi amfani.

*Ga misalai:*

👉 3 da 4
👉 2 da 3
👉 3 da 8

Da sauran su

*A misalin farko*

3 da 4 ne.

To Kawai sai mu buga
*3×4= 12.*

Yanzu da 12 zamu yi aiki.

GA MISALAI

👇👇

*MISALIN NA 1*

Gadon da aka rasu aka bar

Mata
Uwa
Shakiki

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU:

Mata = 👉 1/4

Uwa =. 👉 1/3

Shakiki - Asibci

*YANZU KINGA KENAN*

Mun samu TABAAYUN tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune 4 da 3.

Sai muce 4×3=12.

*YANZU da 12 za mu yi aikin RABON*

*MISALI NA 2*

Gadon da aka rasu aka bar

Uwa

Shakikiya

Baffa

*YANZU GA ABINDA KOWANNENSU ZAI SAMU:*

Uwa = 👉 1/3

Shakikiya = 👉 1/2

Baffa = 👉 Asibci

*YAR-UWA YANZU*

Kinga kenan mun samu TABAAYIN tsakanin lambobin dake qasar farillan.

Lambobin sune *3 da 2.*

Sai muce *3×2=6.*

*Yanzu da 6 zamu yi aikin Rabon*

*ALLAH NE MAFI SANI*

ALHAMDULILLAH

WANANN SHI NE KARSHEN BAYANIN

WADANNAN ABABE GUDA 4

WATO
*AL-ANZARUL-ARBA'AH*

ALHAMDULILLAH

✍️ RUBUTAWA:-
ADAMU KABIRU YAR-GAYA
07033392057
27-07-2026

16/07/2026

Babbar shela ga sababbin manyan masoyana! Saluhu Auwal Umar, Abubakar Usman Ygy, Aliyu Bala, Hindu Yahaya Saleh, Hafsat Yusuf Abdulwahab, Abduljalal Musa Adam Yargaya, Alfazazi Sani

14/07/2026

.

YAN-UWA MASU ALBARKA,WANNAN HOTO DA MUKE GANI SHUKA CE LOKACIN DA TAKE KOKARIN FITOWA.

TAMBAYOYIN DA YA KAMATA MU YIWA KAWUNANMU SUNE NE:-

1- SHIN ABUNDA DA MUKE SHUKAWA YANA DA RAI LOKACIN DA MUKE SHUKAWA??

2- SHIN,MUN SAN LOKACIN DA AMFANIN YAKE YUNKURIN FITOWA??

3- IDAN MUN AMINCE BA SHI DA RAI,LOKACIN DA ZAMU SHUKA,TO WAYE YA TSORO DA SHI YA SANYA NASA RAI??

4- DA SHUKARMU TA FITO,SHIN SANARWAR MU CE TA KAI SHUKAR GACI HAR MUKA GIRMA,KO IKON ALLAH??

😭😭😭😭😭😭

INNALILLAHI WA'INNAH ILAHIR RAJI'UN
TABBAS ALLAH ZAI TASHEMU BAYAN MUN KOMA GARE SHI,YA ALLAH KA MANA AFUWA KA GAFARTA MANA,KA JIKAN IYAYENMU DA MALAMANMU,YA ALLAH KA AMINTAR DAMU RANAR DA ZAKA TARA MU A GABANKA RANAR BA BABU IYA YIN KOMAI SAI DA RAHMARKA,ALLAH KA MANA AFUWA.

Adamu Kabiru Yargaya
14-07-2026
7:52 a.m

10/07/2026
Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Address


Yargaya KanoState Maiduguri Road
Kano