13/07/2026
WASU NASARA TA ƘARA MUSU TAWALI'U... WASU KUMA TA ƘARA MUSU GIRMAN KAI!
Yayin da wasu suke jiran sai gwamnati ko wani ya yi komai, akwai mutanen da suke rubuta tarihin alheri da abin da Allah Ya h**e musu.
Hajara Ibrahim Dan Azumi daga Jihar Gombe ta nuna abin koyi mai girma ga al'ummar Musabaƙar Alƙur'ani. Ba wai kawai ta tsaya kan nata nasarar ba, ta kasance tana tallafa wa sauran 'yan Musabaƙar jiharta, tana ƙarfafa musu gwiwa tare da ba da gudummawa gwargwadon ikon da Allah Ya ba ta domin ci gaban wannan aiki mai albarka.
Bayan kammala Musabaƙar Mata ta Ƙasa ta Nana Asma'u da aka gudanar a Gombe, Hajara ta sake nuna karamci ta hanyar ba da kyaututtuka ga waɗanda s**a samu nasara. Ba girman kyautar ake dubawa ba, ana kallon girman zuciyar da ta sa aka yi ta.
Wannan aiki nata ya cancanci yabo, kuma ya zama darasi ga duk masu ruwa da tsaki a harkar Musabaƙar Alƙur'ani.
Sai dai abin takaici ne yadda a wasu lokuta ake ganin wasu daga cikin waɗanda s**a samu manyan nasarori a Musabaƙun Ƙasa, musamman daga Jihar Kano, amma bayan sun yi suna, sai ka ga sun nisanta kansu da waɗanda s**a tsaya tare da su tun farkon tafiyarsu. Wasu ba sa sake waiwayen matasa masu tasowa, ba sa ƙarfafa musu gwiwa, b***e su ɗora su a hanya kamar yadda su ma aka ɗora su a baya.
Ba ana nufin kowa haka yake ba, domin akwai masu alheri da suke taimakawa cikin sirri, Allah Ya saka musu da alheri. Amma akwai waɗanda nasara ta ƙara musu girman kai fiye da yadda ta ƙara musu tawali'u da godiya.
Darasin da Hajara Ibrahim Dan Azumi ta koyar da aikinta shi ne cewa, ainihin nasara ba ita ce ka lashe gasa ka ɗauki kofi ba; ainihin nasara ita ce ka zama haske ga waɗanda ke bayanka, ka riƙe hannun waɗanda ke tasowa, kuma ka mayar wa Alƙur'ani wani ɓangare na abin da Allah Ya ba ka saboda shi.
Muna fatan wannan aiki nata zai zama kira ga manyan 'yan Musabaƙa, musamman na Kano da sauran jihohi, su sake duba kansu. Domin al'ummar Musabaƙa ba ta buƙatar sunaye kawai, tana buƙatar jagorori masu tausayi, tawali'u da zuciyar bayarwa.
Allah Ya saka wa Hajara Ibrahim Dan Azumi da alheri mai yawa, Ya ƙara mata albarka, Ya sanya wannan aiki nata ya zama abin koyi ga duk wanda Allah Ya ɗaukaka ta hanyar Alƙur'ani.