Afri Voice

Afri Voice

Share

Muna kawo tarihin jarumai, shugabanni, da masu hangen nesa, waɗanda suka fafata domin ‘yancin Nahiyar Afirka.

Manufarmu ita ce kare tarihi, ilmantarwa, da gina sabon tunani a zukatan matasan Afirka.

15/11/2025

❓ Tambayar Yau ga ‘Yan AfriVoice:

“Wace shawara ce ta rayuwa aka taba baka da ta canza yadda kake tunani?”

Zai iya zama:

Shawara daga uwa/uba

Shawara daga malamai

Shawara daga aboki

Shawara daga wani littafi

Shawara daga wani mutum da ka hadu da shi sau daya

Muna so mu ji martanin ka domin mu tashi tare.

“Share one life advice that changed your mindset.”

“Kalmar hikima guda na iya girgiza duka makomar mutum.”

15/11/2025

Menene Identity?

A rayuwar yau, identity na nufin ainihinnyanda kake, inda ka fito, da abin da kake tsaye a kai na rayuwrka.
Kalmar Identity bata cika saida waɗannan abubuwan:

🔹 1. Asalin mutum (Origin)

Kabila, al’ada, harshenka, iyaye, garinku.
Waɗannan su ne tubalin ganinka a duniya.

🔹 2. Abin da kake yi (Purpose)

Ko kana koyon sana’a ne, karatu, kasuwanci ko aikin gwamnati.
Duk suna shiga “identity”.

🔹 3. Darajojin ka (Values)

Gaskiya, mutunci, adalci, kunya, ko biyayya.
Waɗannan su ke nuna wane irin mutum kake.

🔹 4. Abin da kake so (Interests)

Kiɗa, rubutu, coding, tailoring, sports — duk suna zama ɓangaren kai.

🔹 5. Ra’ayin ka game da duniya (Mindset)

Yadda kake kallon rayuwa, canji, aiki, da makoma.
“Identity is the combination of your roots, your values, your passion, and your mindset.
Know who you are — so you can grow into who you want to be.”
“Sani kanka shi ne ginshiƙin cigaban ka.”

01/11/2025

SIR AHMADU BELLO - SARDAUNAN SOKOTO

GABATARWA

Sir Ahmadu Bello ɗaya ne daga cikin manyan jagororin da s**a taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai da ci gaban Nijeriya. Ya kasance Sardaunan Sokoto kuma Firayim Ministan Arewacin Nijeriya kafin samun cikakken ‘yancin ƙasa. An san shi da kishin Arewa, addini, da tarbiyyar al’umma.
An haifi Ahmadu Bello a garin Rabah, a jihar Sokoto, a shekara ta 1909. Ya fito daga dangin Sarakunan Sokoto, zuriyar Shehu Usman ɗan Fodio. Ya fara karatunsa a makarantar Islamiyya, sannan ya halarci Sokoto Provincial School, daga nan ya wuce Katsina Training College inda ya sami horo a aikin koyarwa.
Bayan kammala karatu, Ahmadu Bello ya fara aiki a matsayin malami. Daga baya ya shiga cikin harkokin gwamnati a matsayin District Head a Rabah. A shekarar 1948, ya shiga siyasa kai tsaye lokacin da aka kafa Northern People’s Congress (NPC), inda daga baya ya zama shugaban jam’iyyar.
Ahmadu Bello ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Arewacin Nijeriya ta sami wakilci mai ƙarfi a lokacin tattaunawar samun ‘yancin kai. A cikin jam’iyyar NPC, ya jagoranci shirye-shiryen siyasa da s**a bai wa Arewa damar shiga tsarin mulkin Najeriya cikin fahimta da haɗin kai.
Ya yi aiki tare da Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo wajen tsara sabuwar ƙasa mai cin gashin kanta.
Ya zama Premier na Arewacin Nijeriya daga 1954 zuwa 1966, inda ya kafa manufofin ilimi, noma, da sana’o’i don habaka yanki.

AYYUKA DA MANUFOFI
1. Ya kafa Ahmadu Bello University (ABU), Zaria domin inganta ilimi a Arewa.
2. Ya fara Northern Development Corporation (NDC) don bunkasa tattalin arziki.
3. Ya karfafa haɗin kai tsakanin addinai da al’adu a Arewa.
4. Ya yi aiki wajen gyaran tsarin karatun boko tare da tabbatar da darajar ilimin addini.

MUTUWA
Sir Ahmadu Bello ya rasu a ranar 15 ga Janairu, 1966 a yayin juyin mulki na farko a Najeriya. Mutuwarsa ta bar babban gibi a siyasar ƙasar, musamman a Arewa.

TASIRI
A yau, ana tuna Sardauna a matsayin gwarzo mai hangen nesa da kishin al’umma. Jami’ar Ahmadu Bello da dama daga ayyukan sa suna ci gaba da nuna tasirinsa.
Yana daga cikin mutanen da s**a kafa ginshiƙin haɗin kan Najeriya bayan mulkin mallaka.

DARASI
Sir Ahmadu Bello ya nuna cewa shugabanci nagari yana buƙatar ilimi, tawali’u, da kishin al’umma fiye da son kai. Ya zama abin koyi ga shugabanni da matasa na yau.

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Kaduna