An karbo daga Dan mas'udu ukubata dan amru al'ansariyyu al'badariyyu; (Allah ya kara masa yarda) yace, manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) yace, yana daga cikin abunda mutane s**a riska na daga annabawan farko, cewa, idan baka jin kunya,! To, kayi abunda kaga dama.!
Buhari da muslim ne s**a ruwaito shi.
Hayatul Islam Mando
hayatul islam students association of nigeria
Alhamdulillah
20/01/2021
Sakon Zuciya Ta official trailer its true life story it trou life love story maitashi tv
09/11/2020
Sonduniyyar dantsako - YouTube Arewa maitashi tv madobi ne gargajiya tv 24
27/10/2020
Sirrin kyau episode 14 comment zamuje hutu Arewa maitashi tv masoya madobi
ASSALAMU ALAIKUM
Ramadan Kareem
MADARASATUL HAYATIL ISLAM
No. R13 Musa Umar Street, Mando Kaduna
Tana Farin Cikin Gayyatar kowa Da kowa Zuwa Wajen Saukan Al' Qur'ani...
Wannan Makaranta mai Suna a sama, tana farin cikin Yaye Daliban ta Karo Na Takwas (8)...
Wanda za'ayi kamar haka
Rana: Asabar 5th December 2015
Lokaci: 9:00am (Na safe)
wuri: Harabar makaranta
Don Karin Bayani
08037862937
08028565826
08028193965
Sanarwa Daga Hukumar makaranta.
Allah ya bada ikon zuwa Ameen.......
LUWADI (HOMO) DA ILLOLINSA DA HUKUNCINSA
*****************************************************
Luwadi da Madigo yanzu awannan zamanin sun zama kamar ruwan dare atsakanin Matasa maza da mata. Sun biye ma sha'awar irin ta shaitanci wacce ta mamaye zukatansu, Sun afka cikin mafi Qazantar laifin da aka taba aikatawa adoron Qasa.
Don haka muka zakulo wata nasiha wacce muka taba rubuta ma wani matashi anan zauren fiqhu aranar 7-Jan-2015. (Karkashin tambaya ta 1477).
Gata nan kamar haka:
Hakika aduk cikin nau'o'in zina da dangoginta, Luwadi shine mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani:
"KA TUNA ANNABI LUUT LOKACIN DA YACE MA MUTANENSA "ME YASA KUKE YIN (IRIN WANNAN) ALFASHAR? BABU WANI WANDA YA RIGAKU (AIKATAWA) DAGA CIKIN TALIKAI (HALITTU BAKI DAYA)".
"KU KUNA ZUWA MA MAZAJE TA FANNIN SHA'AWARKU MAIMAKON MATAYE, BARI DAI KU MUTANE NE MASU MUTUKAR 'BARNA".
(A'araf ayah ta 80).
Kuma saboda munin laifinsu shi yasa Allah yayi musu azabar da bai taba yima kowa kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku s**a ciccibe garin zuwa sama, s**a watsa narkon azaba sannan s**a Kifar dasu.
Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:
"YAYIN DA AL'AMARINMU YAZO, SAI MUKA SANYA SAMAN BIRNIN YA ZAMA KASANTA, (WATO MUKA KIFAR DA BIRNIN) SANNAN MUKAYI MUSU RUWAN DUWATSUN WUTA NA SIJJEEL".
Kamar yadda Allah (SWT) yake cewa :
"SAI MUKAYI RUWAN (DUWATSUN AZABA) AKANSU, LALLAI RUWAN DUWATSUN AZABAR NAN TA WADANDA AKAYI MUSU GARGADI YAYI MUNI KWARAI"
(suratun Namli ayah ta 58).
Saboda tsananin bala'in da yake cikin wannan aika-aikar, Manzon Allah (saww) yace:
"MAFI GIRMAN ABINDA NAKE TSORACE MA AL'UMMAH-TA, SHINE IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT".
(Tirmizy ya ruwaitoshi acikin Sunanu, hadisi na 1,457. Ibnu Maajah acikin Sunanu, hadisi na 2,563).
Awani Hadisin kuma, Manzon Allah (saww) yana cewa :
"TSINANNE NE DUK WANDA YAYI JIMA'I DA DABBA, KUMA TSINANNE NE DUK WANDA YA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT".
(Imam Ahmad ne ya ruwaitoshi acikin Musnad, Hadisi na 1878).
Acikin wani hadisin kuma, Manzon Allah (saww) ya fadi irin hukuncin da Shari'ar Musulunci ta tanadar ma masu Luwadi. yana cewa:
"DUK WANDA KUKA TARAR DASHI YANA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT, TO KU KASHE MAI AIKATAWAR DA KUMA WANDA AKE AIKATA MASA"
(aduba Sunanut Tirmizy hadisi na 1,456. da kuma Sunanu Abee Dawud, hadisi na 4,462. Da kuma Sunanu Ibn Maajah, hadisi na 2,561).
LUWADI da Madigo Mummunar Annoba ce wacce ta kauce ma Gwadaben da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai. Don koda dabbobi ba zaka iske suna yin irin wannan abun ba.
Shi yasa Annabi Luut (yas) yace ma mutanensa "KUNZO DA ALFASHA WACCE BABU WANI DAGA CIKIN HALITTU (MUTANE KO ALJANU KO DABBOBI) WANDA YA RIGAKU AIKATAWA".
Imam Ibnul Qayyim Aljawziyyah yana cewa : "Dukkansu guda biyun (wato Zina da luwadi ko Madigo) suna kunshe da mummunar ALFASHAR da ta kauce ma Fitrar Allah.
Kuma Luwadi yana Qunshe da bala'o'in da ba zasu Qidayu ba. Kuma Duk wanda akayi Luwadi dashi, zai gwammaci gara ya mutu da ace an aikata wannan fasadi dashi. Domin idan ya riga akayi dashi, to zuciyarsa zata riga tayi lalacewar da babu sauran tsammanin daidaituwarsa ko kuma dawowarsa kan hanya.
Kuma ba zai sake jin wata sauran kunya ba, ko awajen Allah, ko awajen halittunsa.
Kuma ruwan Maniyyin da Mai Luwadin ya zuba masa, ya zama kamar guba ne ajikinsa da kuma ruhinsa. (Shi yasa yana da wuya su iya yin cikakkiyar tuba wacce Allah yake so. Kuma duk lokacin da abun ya motsa musu sai sunje sunyi, Ko kuma anyi dasu).
Ibnul Qayyim Aljawziyyah yaci gaba da cewa : "Malamai sunyi sabani akan cewa SHIN 'YAN LUWADI ZASU SHIGA ALJANNAH, KO KUMA HAR ABADA BA ZASU SHIGARTA BA?"
Na taba jin Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah yana bayanin ra'ayin Malamai akan haka"
(Aduba Aljawabul Kaafiy, Shafi na 115).
Shi yasa Shari'ar Musulunci tace kashewar ita ce mafi alkhairi gareshi fiye da rayuwa cikin Qaskanci da Wulakanci da kuma rashin Imani.
Ka tuba zuwa ga Allah, ka sani cewa rahamar Allah tana da yalwa, kuma ALLAH yana son bayinsa masu tuba.
"KACE MUSU YA KU BAYINA WADANDA S**A YIMA KANSU 'BARNA!! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA GAFARTA DUKKAN ZUNUBAI BAKI DAYA, SHI SHINE MAI GAFARA KUMA MAI JIN-QAI"
(Suratuz Zumar ayah ta 53).
Ka nisanci Miyagun abokai. Manzon Allah (saww) yana cewa : "MUTUM YANA BIN ADDININ ABOKINSA NE. DON HAKA KOWANENKU YA KULA DA WANDA ZAI YI ABOTA"
(Sunanut Tirmizy, Hadisi na 2,378).
Ka rika zama cikin mutanen Kirki, kuma ka kula da Sallolinka na farillah da nafilfili. ka yawaita zikirin Allah ako yaushe.
Ka nisanci kalle kallen haramun azahiri ko acikin Wayar salularka. Ka sani cewa Allah ya baka amanar dukkan gabobin jikinka ne. Kuma akwai ranar da zai tambayeka.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (2)
Sallah ix approching, tyt ur belt and prepare 4 the best......
Alhamdulillah............
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Website
Address
Musa Umar Street Mando Kaduna
Kaduna