22/07/2024
Zanga zangar ta Sha banban da wacce aka Saba gudanarwa a shekurun baya.
An yi tsarin cewa mutane zasu fito ne daga unguwanninsu sa'an nan su dunguma zawa gidajen duk wanda aka San ya taba taka wani matakin a hukumance tin daga matakin kansila har zuwa gwamna, mutane zasu tisa keyarsu ya kasance sune gaba gaba wajen jagorantar zanga zangar.
Sannan zanga zangar ba irin ta zuwa gidan gwamnati bace gwamna ko wani sakataran gwamnati ya fito yayiwa jama'a wani jawabi a watse, A'a za'a cigaba da zama Daram ne har se anga abin da ya torewa bozo nadi.
Sannan an bukaci ga duk wanda Allah ya horewa da ko biskit, ruwa, abinci, cincin,kulikuli, tabarmin sallah da ruwan alwala,
da duk wani nau'in Abu da ze karfafa guwwar Jama'a da ze hanasu gajiyawa.
Haka zalika an bukaci mutane da su kawar da tsoro da munafurci a zukatansu sa'an nan su nuna da'a da sanin yakamata.