02/07/2026
🌟 APPRECIATION MESSAGE 🌟
Alhamdulillahi Rabbil 'Alamin!
The Management of At-Tibyan Islamic Academy sincerely appreciates Almighty Allah (SWT) for granting us the opportunity and success of our recently concluded Career Day Programme.
Our heartfelt gratitude goes to our amazing pupils and students for their excellent participation, confidence, discipline, and cooperation throughout the programme.
To our esteemed parents and guardians, thank you for your unwavering support, especially for providing the beautiful career outfits that made the event colourful and memorable. Your partnership with the school remains invaluable.
We also extend our profound appreciation to our hardworking teachers and members of staff from both sections of the school. Your dedication, teamwork, and tireless efforts before, during, and after the programme made its success possible. May Allah reward you all abundantly.
Special appreciation goes to our highly respected Proprietor for providing the platform, granting approval for the programme, and for his continuous support towards the growth and development of our prestigious school.
To every stakeholder, supporter, well-wisher, and everyone who contributed in one way or another, we say thank you. Your prayers, encouragement, cooperation, and support are deeply appreciated.
We pray that everyone returned home safely after the programme. May Almighty Allah continue to protect, bless, and grant you and your families good health, peace, and a wonderful time of rest.
This is only the beginning! At-Tibyan Islamic Academy remains committed to providing more exciting, inspiring, and educational programmes for the all-round development of our learners. We therefore look forward to your continued support and maximum cooperation as we work together to build a brighter future for our children.
Thank you once again, and may Allah reward you all abundantly.
Management
At-Tibyan Islamic Academy
_________________________________________________________
🌟 SAƘON GODIYA DA BANGAJIYA 🌟
Alhamdulillahi Rabbil 'Alamin.
Mahukuntan At-Tibyan Islamic Academy suna miƙa saƙon godiya da jinjina ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda cikin rahamarsa da falalarsa Ya ba mu ikon gudanar da Shirin Ranar Sana'o'i (Career Day) cikin nasara da kwanciyar hankali.
Muna miƙa saƙon godiya na musamman ga ɗalibanmu saboda kyakkyawan ɗabi'unsu, biyayya, jajircewa, da cikakkiyar haɗin kai da s**a nuna tun daga farkon shirin har zuwa ƙarshe. Haƙiƙa kun kasance abin alfahari ga makarantar ku.
Haka kuma, muna matuƙar godiya ga iyaye da masu kula da yara bisa goyon baya da haɗin kai da s**a ba mu, musamman wajen samar wa 'ya'yansu kayan sana'o'in da s**a sanya shirin ya ƙara armashi da kayatarwa. Allah Ya saka muku da alheri, Ya ƙara ɗorewar zumunci da haɗin kai a tsakaninmu.
Muna kuma miƙa godiya ta musamman ga malamai da ma'aikatan At-Tibyan Islamic Academy na dukkan sassan makarantar. Ƙoƙarinku, sadaukarwarku, haɗin kanku, da jajircewarku kafin shirin, yayin gudanar da shi, da bayan kammalawarsa ne s**a tabbatar da nasarar da aka samu. Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka muku da mafificin alheri.
Godiya ta musamman ta tabbata ga Mai Gida kuma Shugaban Makarantar, bisa ba da dama, amincewa, da kuma ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga shirye-shiryen da ke bunƙasa ilimi da tarbiyyar ɗalibai. Muna roƙon Allah Ya ci gaba da kare shi, Ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa.
Haka nan, muna godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki, masoya makarantar, abokan arziki, da duk wanda ya ba da gudummawa ko wata irin gudunmawar haɗin kai domin tabbatar da nasarar wannan shiri. Allah Ya saka wa kowa da alheri.
Muna fatan kowa ya isa gida lafiya bayan kammala shirin. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da tsare ku da iyalanku, Ya ba ku lafiya, zaman lafiya, da hutu mai albarka.
Muna sanar da ku cewa, da yardar Allah, wannan ba shi ne ƙarshen irin waɗannan shirye-shirye ba. At-Tibyan Islamic Academy za ta ci gaba da shirya ƙarin shirye-shirye masu armashi, ilimantarwa, da tarbiyya domin cigaban ɗalibanmu ta kowane fanni.
Saboda haka, muna roƙon ci gaba da samun cikakken goyon baya, haɗin kai, da addu'o'inku daga dukkan masu ruwa da tsaki. Da haɗin kanmu ne za mu ci gaba da gina kyakkyawar makoma ga 'ya'yanmu da al'ummarmu baki ɗaya.
Mun gode ƙwarai da gaske. Allah Ya saka wa kowa da mafificin alheri.
Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Mahukuntan Makaranta
At-Tibyan Islamic Academy