Kundin Masoya

Kundin Masoya

Share

Ma'adanin soyayya da masoya, dan samun gamsassun bayanai, shawarwari gami da tattaunawa Discussions

02/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Bin Tukur Sardauna, Lkilima Sulaima

29/06/2024

04/08/2022

TARKON ƁERA

Daga cikin raminsa, ɗan ɓeran na kallon sa'adda maigida ke ta cuku-cukun haɗa masa tarko. Da ya gama sai ɓera ya fito ya nufi wajen zakara a firgice ya ce, "abokina ka taimake ni, an sa mini tarko a gidan nan."

Zakara ya kaɗa fiffike yai shewa ya ce, "ina ruwan maza da wankan jego? Me ya sha mini kai da tarkon da aka sa maka, ɓarnarka ce ta jawo maka."

Ɓera ya wuce wurin zomo ransa a ɓace ya ce, "ɗan uwana ka taimake ni, an ɗana mini tarko a gidan nan."

Zomo ya harare shi ya ce, "wane ne ɗan uwan naka? Kai dai nemi su jaɓa da gafiya."

Ɓera ya ce, "ko da ba jinsinmu ɗaya ba, ai dukkanmu dabbobi ne, ya k**ata mu haɗa kai mu tunkari matsalar da ta doso ɗaya daga cikinmu."

Zomo ya ce, "wuce ka ba ni wuri! Maganinka ke nan ai, ɓuruntunka ne ya jawo. Idan jifa ta wuce kaina, to ta faɗa kan kowa ma."

Cikin takaici ɓera ya nufi wajen rago ya ce masa, "ɗan uwa ka taimake ni, an haƙa mini tarko."

Rago ya yi dariya ya ce, "af, to me ya haɗa kifi da kaska kuma? Kai, ni raba ni da zancen kawai, in ka ƙi ko yanzu ina murje ka! Tafi ba ni wuri."

Ɗan ɓeran nan ya koma cikin raminsa cike da taikaicin yadda sauran dabbobi s**a baɗa masa ƙasa a ido.

Can cikin dare sai aka ji kararaf! Tarko ya k**a.

Ɗan maigidan ya zabura da sauri ya fita don ya cire gawar ɓera daga tarkon. Ashe maciji ne ya jefa wutsiyarsa ciki. Yaro na zuwa maciji ya sare shi, aka ɗauke shi k**ar tsumma sai asibiti. Ɗan nan kuwa shi ke nan, ƙwallin ƙwal, ga uban.

Da safiya ta yi, maigida ya sa aka k**a zakara aka yi wa yaro dabge.

Bayan kwana biyu kuma aka yi farfesun zomo, aka kai wa yaro ya sha lagwada.

Da aka sallami yaro daga asibiti, saboda farin ciki, uban ya sa aka murƙushe rago aka yanka, aka yi abinci aka raba wa maƙota sadaka.

Duk wannan kicimilli da aka yi a gidan, ɗan ɓeran nan na cikin raminsa kwance yana kallon ikon Allah. Ya ce a ransa, 'da sun taimake ni mun kawar da tarkon, da abin da ya faru duka bai faru ba. Matsalar da ta doshi ɗaya, za ta iya game duka.'

Bukar Mada
03/08/2022

Photos 27/02/2022

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Daga cikin Tambayoyin da muke samu daga gareku masu bibiyar wannan shafi, akwai tambaya k**ar haka:

Mahammed Musa

Rayuwar masoya akwai dadi kuma akwai wahala, amma Tambaya: Wanne Yafi Yawa..?
Amsa... yana saurare daga tamu gudunmawar.

Photos 15/09/2021
12/09/2021

MUTUWAR AURE,

RASHIN DAWO WAR MIJI GIDA DA WURI

Mutuwar aure a halin yanzu ta zama ruwan dare a tsakanin hausa fulani fiye da kowace kabila a duniya shakka-babu a kowace ranar Allah sai daruruwan ma'aurata sun rabu da jina, saboda rashin jituwa da kan shiga tare da samun gindin zama a tsakaninsu.

ME KE JAWO HAKAN?
Rashin bin ka'idojin zaman aure ne ya haddasa hakan? Ko kuma...? haka siddai, ruwa ba ya tsami banza, ya k**ata mu duba wannan lamari mu gani...
---‘Yar Uwa ki rike matsayinki: a ko ina kika samu kanki to ki tabbatar kin rike matsayinki na matar aure.
--Wasu matan yayin da s**a fita zuwa gidan biki ko suna da wuya su yi k**a da matan aure, wannan yana sa mazan banza su rika bin su, matsala inda anyi rashin sa'a matan masu kwadayi ne sai su rude ta har su kai ga aikata alfasha, Allah ya kyauta.
--Hadin gwiwa: a matsayinki na matar aure akwai wasu ayyuka da s**a k**ata ki je ki yi tare da mijinki
--Kyakkyawan zato: a duk duniya babu miji da zaki same shi dauke da duk halayen da kuke so dole a samu wadansu kina so wasu kuma ba kya so.
--So mijinki yadda yake: wasu matan sai bayan aure sai su wayi gari su ga ba irin mijinsu suke so ba ne ...wasu don a ganinsa yaana da kudi wasu kuma halayensa ne ba sa so, wanna matsala ce mai saurin kawo mutuwar aure ya k**ata ki so mutum dan Allah ba don abin hannusa ba
----A koda yaushe mijinki ya kira ki zuwa shimfidarsa, ki nuna masa farin cikinki, amma kafin ki kusance shi, ki tabbatar kina cikin tsabta wannan matsala ga mata akwai yawa
--Ko yi sana'a yawan tamnayar mijinki kudi na kulum wanna matsalace ki dinga sana'a yar'uwa

*****************************
**RASHIN DAWOWAR MAI MIJI DA WURI**
Wannan shawarwarin duniyar mallakar miji gareki ne, kula da su zasu baki garkuwar sarrafa miji yanda kika so:
---Ki sani mafi yawa daga mazaje sun fi son zaman wajen akan zaman cikin gida wannan wani abune da ya samo asali daga ainihin gundarin halayyar da namiji don haka in dai ba wani aikin asha ne yake sa shi dadewa a waje ba to kiyi hakuri ki bi shi a hankali har Allah yasa ya rage dadewa a wajen sosai
---Ki daina jin haushin mijinki saboda wannan dabi'a akan wannan dabi'a da yake da baki so matukar kina jin haushin abin kuma kina bayyanar masa da jin haushin to wanna ba zai sa ya daina ba sai dai ya kara ingiza shi ma ga alkatawa
---Kar ki runqa damunsa da mita da qorafin bai dawowa da wuri
namiji bayaso wanna
---Ki binciki kanki da yanayin zaman ku da shi bincike mai zurfi wata qila akwai wani abinda k**e mashi wanda yasa bai son zaman gida ki bincike da kyau
---Kuma kiyi hakuri, namiji sai da hakuri, zaman aure ma sai da hakuri.
Naku...
.
/Author

12/09/2021

KALU B***N MASOYA

Tun tale tale, SAMARI da YAN MATA kanyi SOYAYYA da juna, s**an FUSKANCI matsaloli DABAN DABAN, kamin su kai ga AURE, wasu kuma ba su kai ga haka ba.

To! yanzu a wannan YANAYI ko ince ZAMANI da muke ciki,
tsakanin MASOYA (MAZA ko MATA wadanne SUKAFI fuskantar MATSALAR SOYAYYA ko kuma KALU BALE?

• Ana iya MAGANCE kalu bale a SOYAYYA?

• Wane irin KALU BALE ne ka/ki ka TABA GANI na SOYAYYA, kuma TA YAYA aka WARWARE MATSALAR?

• Ina DARASI cikin wancan KALU BALE na baya?
.

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kaduna
0076