05/08/2017
===>MUGUWAR KISHIYA PART 4 ==>Aisha tana ja da baya, shikuwa abdul yana kara kusantar ta hardai taje karshen bangon daki, abdul yayo kanta gadan- gadan, Aisha tana dubawa gefanta taga wukar da umma take amfani da ita, batayi wata-wata ba ta dasa hannu ta dauko wukar nan ta nuna abdul da ita, tace kada kamatso wallahi zan caka maka wukar nan, wanda tuni idonsa ya rufe yayo kan Aisha, ita kuwa batasan sanda ta labta masa wukar nan akai ba, abdul ya kwalla kara a zube akasa, amarya da fatima s**a jiyo karar abdul su taho aguje, ita kuwa Aisha tuni ta rude sakamakon ganin yadda jini ke zuba daga kan abdul, su amarya s**a karaso suna zuwa s**aga Aisha rike da wuka a hannu, basuyi jinkirin kiran abba ba tare da daukar abdul zuwa asibiti, Bayan sun karasa asibiti ne, likita ya fara duba abdul, su amarya da fatima suna zaune sunyi tagumi, alhaji ya shigo arude, ya nufi wajen likita, yace likita yajikin nasa likita yace da sauki, domin yanxu anyi masa duk abinda ya dace saboda haka zaku iya komawa dashi, alhaji yabiya kudin komai, sannan yadauko su a motarsa yana tafiya yana xage- xage akan Aisha, Amarya tana kara xuga shi, Ita kuwa Aisha tuni hankalinta yagama tashi domin sanin abinda zai biyo baya, tayo waje domin barin gidan kafin abba yadawo, tana zuwa kofa s**ai karo da umma, umma tace lapiya Aisha? Aisha ta fada mata duk abinda ya faru' don haka umma tayi saurin bawa Aisha kudin mota, umma tace kiyi sauri kitafi gidansu kaka idan abin ya lafa saiki dawo, Aisha tace to umma, aiko min da kayana na makaranta, umma tace to, Aisha tayi waje, kana ganinta kasan arude take, Umma tana zaune tayi tagumi, taji shigowar su alhaji ko sallama babu sai masifa yake, yashigo dakin umma yatsaya akanta, yafara magana cikin fushi, Ke ina wannan "yar iskar yar taki? Maganar tayiwa umma xafi matuka, hakan yasa mikewa cikin fushi, tace alhaji duk abinda zakai kada ka kara kiran "yata "yar iska, ga "yan iska nan kana tare dasu wannan yaron yayi kokarin yiwa "yarka fyade amma kuma sai gashi kai kake kare......... Saukar mari umma taji a fuskar ta, tana dubawa taga amarya ce ta zabga mata mari, itama batayi wata- wata ba ta daga hannu ta sharara mata mari, abba dake tsaye yana kallo tuni shima ya daga hannu zabgawa umma mari wanda sai da ya tilastawa umma dafe kumatu, umma ta fashe da kuka mai tsanani wanda duk wanda yaji dole ya tausaya mata, alhaji ya kara da cewa kuma idona idan Aisha sai na karya ta, s**a juya s**a fice daga dakin s**a bar umma tana kukan bakin ciki, Aisha bata tsaya ko ina ba sai gidan kakanninta ta fada musu duk abinda yafaru, hakan yasa kakanta yace gaskiya abin nashi cigaba yake don haka bari naje wajen malam nasanar dashi abinda yafaru, Bayan dare yayi amarya da abba suna zaune, abba yana ta lallashin amarya amma taki, sai abba yace kifadi abinda k**e so nayi miki komai wahalarsa don ki daina fushin nan, amarya tayi murmushi da alama taji dadin maganar abba, sannan tace ni abu hudu nakeso, alhaji yace fade su duka indai kudi ke yinsu kamar angama ne, amarya tace 1 inaso kadawo min da yan uwana mutum takwas gidan nan da zama 2 inaso ka cika min alkawarina na motar da kace xaka sai min 3 inaso mufita kasar waje shakatawa, na hudun kuma baxan fada ba sai mun dawo daga shakatawa,abba yace wannan duk mai sauki ne indai zaki huce, don haka gobe zan tura driver ya dauko "yan uwan naki, mota kuma muna dawowa xaki ganta, don haka wace kasa. K**e so mu tafi? Amarya tace maleyshia, abba yace to kada kidamu tawan, farin ciki ya lullube ta, Abba ya gama shirin tafiya maleyshia shida amaryarsa gida kuma ya cika da "yan uwan amarya, wanda yanxu su goma ne tara daga ciki dukkansu maza ne majiya karfi daya ce mace wato fatima, sai sharholiyar su suke kamar gidan ubansu, umma kuma bata da damar sakewa haka umma tayi ta hakuri tana lissafin dawowar danta Samar wanda kullum takeyiwa addu'a, Yaune ranar tafiyarsu abba da amarya maleyshia don haka ya tara kowa nagidan, yafara jawabi
kijira danji a gaba