12/08/2023
BAYANIN YADDA AKE YIN ISTIKHARA IRIN WACCE ANNABI ﷺ YA KOYAR
:
Istikhara wata sallah ce da akeyi domin neman za'bin Allah madaukakin sarki game da wasu al'amura da bawa yake neman zabin Allah a cikin ɗaya daga cikinsu, misali kamar a harkar neman aure dadai sauran wasu al'amuran.
Anan zamu fahimci cewa ashe ita istikhara ibadace kuma Annabi muhammadu ﷺ shine ya koyar da yadda ake yin ta, sabida haka babu inda akace kaje ayi MAKA ita inkuma kaje daya daga cikin wannan zaayi MAKA . bugun kasa ko duban taurari ko akira aljani a tmby shi shikuma ya gaya musu karya da gaskiya sukuma su gayama Allah yabamu Samar bin abinda Manson Allah ﷺ yazo mana dashi .duk wanda yayi wata istikhara ba irin wacce manzon Allah ﷺ ya koyar ba, to ya sani ba istikhara tabbatacciya yayi ba koda ma yayi babu wani tasiri da zatayi domin Allah madaukakin sarki baya karbar duk wata ibada har sai anyita a bisa koyarwar Annabi muhammadu ﷺ .
Sahabi jabir (ra) yana cewa: *MANZON ALLAH ﷺ YA KASANCE YANA KOYA MASU ISTIKHARA A CIKIN DUKKAN AL'AMURANSU KAMAR YADDA YAKE KOYA MUSU SURA DAGA CIKIN AL'KURANI.*
hadisin yana cikin *Sahihul Bukhari*
kunga wannan yake nuna mana ashe ita itikhara annabi ne ya koyar da ita bawai kowa gaban kansa zeyi kawai yaje ya aikata abinda yaga dama a matsayin istkhara ba.
Hal ila yau dai sahabi jabir yana cewa: Annabi yace: *IDAN 'DAYANKU YAYI NUFIN YIN WANI AL'AMARI TO YAYI SALLAH RAKA'A BIYU BA SALLAR FARILLAH BA SANNAN YACE*
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ-(((( وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ ))))))– خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْ