Taskar Yabon Annabi

  • Home
  • Taskar Yabon Annabi

Taskar Yabon Annabi � Maraba da ku zuwa Taskar Yabon Annabi
� Inda ake yada soyayyar Manzon Allah ﷺ
� Islamic Nasheeds

ACIKIN KUNGIYOYIN YABON SHUGABA SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WACE KUNGIYA KASANI DA TAKAI SHU'ARA'U HADIN KAI ?DA DA AKWAI...
09/09/2026

ACIKIN KUNGIYOYIN YABON SHUGABA SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WACE KUNGIYA KASANI DA TAKAI SHU'ARA'U HADIN KAI ?
DA DA AKWAI DA YANZU KUN FADA
ALLAH YA SAKAWA SHARIF RABIU DAN USMANU

09/09/2026

Tsira da aminci
Su kara tabbata ga maceci

07/09/2026

Alhaji Abubakar Musa Madihi Kaduna
Shugaban jama'atu shu'ara'il Islam ta kasa

06/09/2026

Alhaji Abubakar Musa Madihi

06/09/2026

12 Rabiul auwal

Ko a rubutun suna wane suna kataba gani ya tsaru kamar sunan me gida ?
06/09/2026

Ko a rubutun suna wane suna kataba gani ya tsaru kamar sunan me gida ?

03/09/2026

Nima copy nayi
Jiya da daddare Mage ta ta fita daga gida ba tare da kowa ya kula ba, kasancewar bata fita sai dai idan ta ji an buga gida to zata zo bakin kofa ta tsaya, ana bude wa sai ta fita amma ana kiran ta za ta dawo gida, to jiya wajen karfe 8 na dare na ji an buga kofa na ce waye? da na ji mata ne sai na fada wa Madam cewa kin yi baki, sai ta je ta bude s**a shigo.

Ashe magen nan ta fita dai dai lokacin da s**a shigo, duka-duka ba su fi kamar minti 10 ba s**a tafi, bayan sun fita sai Madam ta ce ina mage? Na ce duba ina jin tana karkashin mota, aka yi ta kira shiru! Sai Almajiri na ya shigo, na ce duba waje ko mage ta fita, yana fita sai s**a dawo da wani yaro, ya ce magen ta shiga nan gidan (ya nuna gidan makwabci na) kuma sun taru sun dake ta har sun kashe ta!

Madam ta zuri hijabi ta fita da gaggawa, kawai sai na ji tana Inna lillaHi wa Inna ilayhir rajioun sun kashe ta, haka nima na mike na fita da sauri.

Kasancewar mai gidan matafiyi ne, lokaci-lokaci ya ke dawo wa, sai na kira wani yaro (an ce kanin matar mai gidan ne) na tambaye shi me yasa kuka kashe min mage, sai ya ce "wai suna tsammanin turo ta aka yi, shine yar me gidan ta tayar da aljanu ta kashe ta".

Wallahi ina jin hayaniya a gidan bayan bakin nan sun tafi, amma sai na dauka ko wasa suke yi, (kasancewar wani lokacin sai su kunna MP su saka wakar Gwanja su yi ta cashewa) ashe Madam ta ji lokacin da ake buga magen da bango ana cewa "waye ya turo ki" har shi matashin yana cewa kin kashe ta fa, haka na fita naga magen nan kwance jini ta kunne da baki.

Ai kuwa ban san lokacin da na antayo ta maguzawa na antaya mu su ba.

Na yanke shawarar shigar da kara kotu a yau, amma makwabta sun bani hakuri sosai, saboda mai gidan mutumin kirki ne, kuma baya gari s**a yi wannan kisan gillar.

Wallahi jiya kwana na yi ban yi baccin kirki ba, haka Madam kwana tayi tana kuka, Akmal ma haka yake ta kuka, yau ma ya ki cin komai idan na tambaye shi sai ya ce "a dawo min da mage ta"!

Da fitar magen nan, da shiga gidan su, da kashe ta duk ba'a fi minti 10 ba.

Sun zalunci baiwar Allah, bata zuwa ko'ina, ita dai tana matukar son waje, ana buga gida to zata fita, tayi kalle-kalle ta dawo.

Tare muke komai, muna cin abinci tana gefen mu, muna Sallah tana gefen mu, muna karatu haka, sai ta rakani kofar gida idan zan fita, haka da zarar ta ji karar mota ko mashin za ta zo bakin gate da gudu ta san na dawo.

Ni dai na hakura kamar yadda makwabta s**a nema, amma gaskiya sai Allah Ya saka mata kisan gillar da aka yi mata ba tare da hakki ba.

Don Allah wanda ya ke da Jaririyar Mage ya taimaka min ko don Akmal da Maman shi su samu sauki. Zan iya zuwa ko'ina ne a cikin garin Kano don na karba.

26/08/2026

Majalisin shabiyu ga Rabiul auwal 2026

Address

Kawo Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Yabon Annabi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Taskar Yabon Annabi:

Shortcuts

  • Want your school to be the top-listed School/college?

Share