29/10/2025
Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Muhammadu Sanusi II ya ce a baya gwamnatin Najeriya na ciwo bashi domin biyan tallafin man fetur sannan kuma ta ƙara ciwowa domin biyan kuɗin ruwa.
Ya ƙara da cewa duk da Shugaba Jonathan ya amince da janye tallafin, bai cire ba saboda matsalar rikicin Boko Haram.