21/09/2025
All men are born equal but only legend attend barewa college zaria..........
Ɗ𝐚𝐧 𝐀𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 ƙ𝐚𝐫𝐚𝐦𝐚𝐫 𝐇𝐮𝐤𝐚𝐦𝐚 𝐋𝐞𝐫𝐞 , 𝐅𝐚𝐫𝐟𝐞𝐬𝐚 𝐍𝐚𝐬𝐢𝐫𝐮𝐝𝐝𝐞𝐞𝐧 𝐔𝐬𝐦𝐚𝐧, 𝐘𝐚 𝐙𝐚𝐦𝐚 𝐒𝐚𝐤𝐚𝐭𝐚𝐫𝐞𝐧 Ƙ𝐚𝐬𝐚 𝐧𝐚 𝐁𝐎𝐁𝐀 𝐚 𝐓𝐚𝐫𝐨𝐧 𝐒𝐡𝐞𝐤𝐚𝐫𝐚 𝐭𝐚 𝟐𝟎𝟐𝟓
Al'umma daga sassa daban-daban na ƙasar Najeriya sun halarci babban taron shekara-shekara na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Barewa College, wato Barewa Old Boys Association (BOBA) , wanda aka gudanar a ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025.
Taron ya kasance mai cike da tarihi da girmamawa, inda aka gudanar da zaben sabbin shugabanni na ƙungiyar. Daga cikin manyan baki da s**a halarta akwai tsohon shugaban kasa yakubu Gowon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ,da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido tsohon gwabna kwara a Mulki soja ,, tare da sauran fitattun tsofaffin ɗaliban makarantar.
A cikin zaben da akaSule Lamidon zaɓi sabbin shugabanni kamar haka:
Matsayi Suna
Shugaba Janar Lawal Kazir
Sakataren Ƙasa Farfesa Nasiruddeen Usman
Sakataren Kuɗi Alkali Ahmad Talba
Mai ba da shawara (Shari’a) Muhammad Sani
Farfesa Nasiruddeen Usman, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Lere a Jihar Kaduna, ya samu nasarar zama Sakataren Ƙasa na BOBA—wannan babban matsayi ne da ke nuna irin girmamawa da amincewa da kwarewarsa a cikin ƙungiyar.
Wannan nasara ta Farfesa Nasiruddeen Usman ta haifar da farin ciki da alfahari ga al’ummar Lere, musamman ma matasa da ke kallon irin wannan ci gaba a matsayin kwarin gwiwa da kwatance.
Muna taya Farfesa murna tare da fatan Allah ya ba shi nasara da shiriya wajen tafiyar da ayyukan ƙungiyar, da kuma ci gaba da wakiltar yankin Lere da kyau a matakin ƙasa.