Al'ilmul Hisab Tv

Al'ilmul Hisab Tv Domin Samun Sirrika Da Fa'idoji Na Ilimin Hisabi Da Taimakon Al'umma, Daga Alqur'ani Da Tsirrai.

YAU JUMA’A - 17th July, 2026Ranar Juma'a nada tauraron Zahara (Venus) kuma sa'idin rana ce, tana da tasiri mai ƙarfi a f...
17/07/2026

YAU JUMA’A - 17th July, 2026

Ranar Juma'a nada tauraron Zahara (Venus) kuma sa'idin rana ce, tana da tasiri mai ƙarfi a fannin al-ḥubb soyayya. Wannan rana tana da ƙarfin ruhaniya (قُوَّة رُوحَانِيَّة) da ke taimakawa wajen haɓaka dangantaka tsakanin ma’aurata.

Za'a samu nasara sosai idan akayi ayyukan mallaka (ملْك) da nufin ƙarfafa soyayya da aminci tsakanin ma’aurata a wannan rana. Tauraron yana taimakawa wajen tabbatar da haɗin kai da jin daɗin zaman aure.

Haka kuma, Juma’a rana ce dake dacewa don kulla sabbin soyayya (عَلاقَات حُبّ) ko mayar da tsohon aure zuwa sabuwar fahimta da haɗin kai. Wannan tasiri yana taimaka wajen warware matsaloli da rashin jituwar ma’aurata.

Bugu da ƙari, duk wanda s**a rabu da matar sa a irin wannan rana ake zuwa biko (اِسْتِخْدام السِّحْر) na al’ada ko na ruhaniya (Asirin kiranyen ta dawo) suna iya samun tasiri a wannan rana, musamman idan ana yin su don kyautata rayuwar aure da soyayya cikin halal da nagarta, Sannan kuma dukkan aikin da za'ayi sai an haɗa sa da sadaqa mai ƙarfi,shine tasirin sa zai inganta.

ADDU'AR DA AKEYI A WANNAN RANA!

Wannan rana ta Juma'a mai tauraron Zahara da kuma albarkar wannan rana da Allah Ya ɗaukaka fiye da sauran ranaku. Wannan rana ce da ake samun haɗin kai da nasara a al’amuran soyayya, zaman lafiya, da dukkan ni’imomin rayuwa.

Bayan an kammala Sallar Juma’a ko kuma bayan Sallar Magariba, ana yin wannan wuridi. Ba a buƙatar ƙarin nafila a nan, domin manufar shi ne tsarkake zuciya da nufin samun dacewa.

Wuridin shi ne, a karanta Kalmar Shahada (لَا إِلٰهَ إِلَّا اللَّهُ مُحَمَّدٌ رَسُوْلُ اللَّهِ) kafa 1111. Wannan addu'ar tana da ƙarfi wajen buɗe ƙofin soyayya, albarka, zaman lafiya, da haɗin kai a tsakanin ma’aurata da dukkan al’umma.

Bayan an kammala karatun, sai a ɗaga hannu a yi addu’a bisa ga duk wani buƙata ta alkhairi; kamar samun ƙauna da jituwa a aure, nasarar harkokin kasuwanci, tsira daga fitina, ko samun ƙarfin zuciya da kwanciyar hankali.

Wajibi ne yin sadaqa mai ƙarfi bayan kammala sirrin, domin ita ce ke ƙarfafa tasirin wuridin da kuma jawo rahamar Allah. Duk wanda ya yi wannan a ranar Juma’a da niyya mai kyau, zai ga sakamako da yardar Allah cikin sauƙi.

Izininsa ayi Salati ga Annabi (SAW) Sannan a turawa yan'uwa su amfana.

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2347035259161

FAHIMTAR ILIMIN BURUJAI DA SAURAN ILIMAN TAURARIMalaman Falaki (علماء الفلك) suna cewa  Ilimin Taurarin Kawakibus Sayyar...
16/07/2026

FAHIMTAR ILIMIN BURUJAI DA SAURAN ILIMAN TAURARI

Malaman Falaki (علماء الفلك) suna cewa Ilimin Taurarin Kawakibus Sayyarah (الكواكب السيّارة), Ilimin Ramli (علم الرمل), Ilimin Burujai (علم البروج), da sauran iliman taurari waɗanda ake amfani da su wajen yin hasashe (تَخْمِين) ko ƙiyasi kan wasu al'amuran rayuwa. Wannan hasashen ba ya nufin tabbacin abin da zai faru, domin ilimi ne na nazari da ƙididdiga, ba sanin gaibu ba.

A cewar malaman falaki, ana iya amfani da Ilimin Burujai (علم البروج) wajen yin hasashen wasu halaye, yanayin mu'amala, ko kuma yiwuwar yadda wasu al'amura za su kasance. Haka kuma, Ilimin Taurarin Kawakibus Sayyarah (الكواكب السيّارة) na iya bayar da hasashe kan lokutan da ake ganin wasu ayyuka za su fi dacewa ko kuma su fuskanci ƙalubale gwargwadon ƙa'idodin wannan ilimi.

Haka nan, Ilimin Ramli (علم الرمل) da sauran hanyoyin nazari ana amfani da su wajen yin hasashe game da wasu tambayoyi ko al'amuran rayuwa bisa ƙa'idojin da masana s**a shimfiɗa. Duk da haka, sakamakon da ake samu ƙiyasi ne (اجتهاد), ba tabbacin abin da lallai zai faru ba.

Saboda haka, malaman falaki suna jaddada cewa waɗannan ilimai suna bayar da hasashe (ظَنّ) ne kawai, ba tabbaci (يقين) ba. Sanin gaibu cikakke yana wurin Allah (ﷻ) kaɗai, Shi ne (عَالِمُ الْغَيْبِ) wanda Ya san duk abin da ya ɓuya da abin da zai faru.

Allah Shine Mafi Sani!

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2349169020915

......???
16/07/2026

......???

SIRRIN KWANA TARA (9) DOMIN YAYE TALAUCI DA NEMAN SAMUN ARZIƘI BI'IZNILLAH Ana yin wannan aiki na tsawon kwana tara (9),...
16/07/2026

SIRRIN KWANA TARA (9) DOMIN YAYE TALAUCI DA NEMAN SAMUN ARZIƘI BI'IZNILLAH

Ana yin wannan aiki na tsawon kwana tara (9), sannan bayan an kammala a yi sadaka (صَدَقَة) da abin da ya sauwaƙa. Ana fara aikin ne a ranar Lahadi (الأحد), sannan a kammala shi a ranar Litinin ta sama, tare da cikakken tawakkali (التَّوَكُّلُ) ga Allah Maɗaukakin Sarki.

A farkon kowace rana, a fara da Miftahul Amal (مفتاح العمل), sannan a yi wuridin "Alam Nashrah" (أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ) ƙafa uku (3). Wannan wuridi na Alam Nashrah ana ci gaba da yin sa ƙafa uku a kowace rana har zuwa ƙarshen aikin.

A ranar farko ta Lahadi (الأحد), a karanta Suratul Al-Waqi'ah (سورة الواقعة) ƙafa uku (3). Daga nan kuma, a kowace rana ana ƙara karatu da ƙafa biyu (2), wato: rana ta biyu ƙafa biyar (5), rana ta uku ƙafa bakwai (7), rana ta huɗu ƙafa tara (9), har zuwa rana ta tara, inda adadin karatun zai kai ƙafa goma sha tara (19).

Duk wanda ya yi wannan sirri da niyya (النِّيَّة) ta gari, tare da ikhlasi (الإخلاص) da dogaro ga Allah, idan yana cikin talauci ko wata masifa ta rayuwa, ana fatan Allah (سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى) zai buɗe masa ƙofofin alkhairi da arziki, Ya ba shi mafita cikin ɗan lokaci, bi'iznillah.

Allah Shine Mai Biyan Buƙata!

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2349169020915

LOKACIN TAMBAYA DA TASIRINSA A ILIMIN FALAKILokacin da mutum ya gabatar da tambaya game da wata buƙata wajen wani malami...
16/07/2026

LOKACIN TAMBAYA DA TASIRINSA A ILIMIN FALAKI

Lokacin da mutum ya gabatar da tambaya game da wata buƙata wajen wani malamin falaki (عِلْمُ الْفَلَكِ) ana ɗaukar wannan lokaci a matsayin muhimmin abin lura wajen fahimtar yanayin lamarin. Masana falaki suna ganin cewa lokacin tambaya (وَقْتُ السُّؤَالِ) yana da tasiri wajen hasashen yiwuwar biyan buƙata (قَضَاءُ الْحَاجَةِ), domin kowace rana tana da sa'o'i goma sha biyu (12) na yini da kuma sa'o'i goma sha biyu (12) na dare, waɗanda ake dangantawa da jagorancin taurari guda bakwai (السَّبْعَةُ الْكَوَاكِبُ). Waɗannan taurari kuma an fi rarraba su zuwa Sa'idai (السُّعَدَاءُ), Nahisai (النُّحَسَاءُ), da Mumtajazai (المُمْتَزِجَةُ).

Idan tambaya ta zo a lokacin da tauraron Sa'idi (السَّعْدُ) yake da mulki, masana falaki suna kallon wannan a matsayin lokacin sa'a (سَاعَةُ السَّعْدِ). A irin wannan lokaci ana ganin cewa buƙata na iya samun sauƙin biya, musamman idan aka haɗa da addu'a (الدُّعَاءُ) da kuma amfani da turaren da ya dace da manufar addu'ar. A fahimtar wasu masana falaki, wannan lokaci yana daga cikin lokutan da ake ganin suna da damar sauƙaƙa hanyoyin cimma buri.

Idan kuwa tambayar ta kasance a lokacin da tauraron Nahisi (النَّحْسُ) yake da iko, ana ɗaukar wannan a matsayin lokacin tsaka-tsaki (حَالَةٌ مُتَوَسِّطَةٌ). A irin wannan yanayi ana ganin buƙata na iya fuskantar jinkiri ko ƙalubale kafin ta samu sauƙin biya. Saboda haka wasu masana falaki suna ba da shawarar dagewa wajen addu'a (الدُّعَاءُ) da sadaqa (الصَّدَقَةُ) tare da ƙoƙari (الاجْتِهَادُ) domin neman sauƙin al'amari, duk da cewa ba sa ɗaukar hakan a matsayin tabbacin samun biyan buƙata.

Lokacin Mumtajazi (المُمْتَزِجُ) kuwa ana bayyana shi a matsayin lokaci mai haɗa yiwuwar alheri da ƙalubale gwargwadon yanayin tambayar da matsayin taurarin. A irin wannan lokaci, idan aka yi amfani da hikima (الْحِكْمَةُ), addu'a (الدُّعَاءُ) da sauran hanyoyin da ake ganin sun dace, ana iya samun sakamako mai kyau. Idan kuma aka yi sakaci, ana ganin buƙatar na iya fuskantar tangarɗa. Saboda haka, wasu masana falaki suna cewa lokacin da aka yi tambaya (وَقْتُ السُّؤَالِ) na iya ba da haske game da rabin fahimtar amsar lamarin, yayin da cikakken sakamako kuma yana nan a ƙarƙashin ikon Allah.

Allah Shine Mafi Sani!

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2349169020915

SIRRIN HATIMIN KARIYA DAGA SHARRIN MUTUM DA ALJANAna rubuta Suratul Fath (سورة الفتح), wato "إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْح...
16/07/2026

SIRRIN HATIMIN KARIYA DAGA SHARRIN MUTUM DA ALJAN

Ana rubuta Suratul Fath (سورة الفتح), wato "إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْحًا مُبِينًا", zuwa sura ƙafa uku (3). Bayan kowacce aya, a rubuta. لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ الْعَلِيِّ الْعَظِيمِ

A ci gaba har sai an kammala rubutun gaba ɗaya. Bayan an gama, a rubuta wannan hatimin (خاتم) ƙafa uku a ƙarshen rubutun bisa tsarin daya dace.

Daga nan sai a wanke rubutun da ruwa mai tsafta (مَاءٌ طَاهِرٌ), sannan a sha da niyyar neman kariya (الحماية) da taimakon Allah (سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى).

Duk wanda yayi wannan sirri zai samu kariya daga sharrin mutum (شَرُّ الْإِنسِ) da na aljan (شَرُّ الْجِنِّ) bijahi Rasulillah (بِجَاهِ رَسُولِ اللَّهِ). Duk da haka, a yi cikakken yaƙini cewa kariya ta gaskiya tana hannun Allah (عَزَّ وَجَلَّ) Shi kaɗai, domin Allah (سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى) Shi ne Mafi Iko kuma Mafi Kariya.

Allah Shine Mai Biyan Buƙata!

Izininsa ayi Salati ga Annabi (SAW) Sannan a turawa yan'uwa su amfana.

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2349169020915

Allah Shine Mafi Sani!
16/07/2026

Allah Shine Mafi Sani!

YAU ALHAMIS - 16th July, 2026Ranar Alhamis, ana danganta ta da tauraron Mushtari (المُشْتَرِي), wanda ake ɗauka a matsay...
16/07/2026

YAU ALHAMIS - 16th July, 2026

Ranar Alhamis, ana danganta ta da tauraron Mushtari (المُشْتَرِي), wanda ake ɗauka a matsayin tauraro mai ɗauke da albarka da yalwar arziki (رِزْق). Wannan rana tana ɗauke da ƙarfin ruhaniya (قُوَّة رُوحَانِيَّة) da tasirin da zai iya buɗe sabbin hanyoyi ga nasara akan duk abunda ake nema.

Tauraron mushtari Sa’idi ne (سَعِيد) wato tauraro mai albarka da nuni da abu mai kyau. Tasirinsa yana kawo faɗaɗa ilimi, ci gaban dukiya (مَال), da samun kyakkyawar mu’amala (مُعَامَلَة حَسَنَة) da mutane. Wannan yasa ake ganin Alhamis a matsayin rana mai kyau ga shirye-shiryen da ke buƙatar sa’a (حَظّ) da albarka.

A irin wannan rana, ana gudanar ayi ayyukan Fatahi (فَتْح) buɗe hanyoyin arziƙi, wato neman Allah (ٱللّٰه) Ya buɗe kofofin nasara da damar rayuwa. Sannan ana yin Ludufi (لُطْف), wato neman taimako (مُسَاعَدَة) da sauƙin al’amura daga Allah, musamman idan mutum yana fuskantar ƙalubale a rayuwarsa.

Kuma, ana aiwatar da Dafa'i na rayuwa a wannan rana, wato neman kariya (حِمَايَة) daga duk wani abu mara kyau da ka iya kawo cikas a ci gaban al'amurra.

ADDU'AR DA AKEYI A WANNAN RANA!

Anayin Sallar Nafilah raka’a biyu (2) bayan sallar Asuba ko kuma bayan sallar Zuhri. A kowace raka’a, a karanta Suratul Fatiha kafa 1.

Sannan a biya da Ayatul Kursiyyu kafa 3. Wannan sallar tana daga cikin sirrikan da malaman ruhaniya s**a tabbatar tana buɗe ƙofofin albarka da nasara ga mai yin ta da niyyar neman sauƙi daga Allah. Musamman a wannan rana ta Alhamis.

Bayan kammala sallar, a yi addu’a da cewa:
اَللّٰهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ وَأَبْوَابَ رِزْقِكَ وَبَارِكْ لِي فِيمَا رَزَقْتَنِي
Allahumma iftah li abwaba rahmatika wa abwaba rizqika wa barik li fima razaqtani.

Domin ƙarin tasiri, bayan addu’ar, a karanta sunayen Allah masu tsarki:"Ya wasi'u Ya Wahabu - يَا وَاسِعُ، يَا وَهَّابُ" ƙafa 129. Bayan an gama, a yi salati ga Annabi ﷺ kafa 21 domin cikawa da albarka. Wannan wuridin zai taimaka wa mai yinsa wajen samun sauƙin al’amura, yalwa cikin arziki, da ƙarin albarka a rayuwa.

Izininsa ayi Salati ga Annabi (SAW) Sannan a turawa yan'uwa su amfana.

Moussa Alfalaky Almus'haweey
WhatsApp: +2347035259161

15/07/2026

Wasu muhinman sirrika uku acikin suratul yaseen part 4

15/07/2026

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al'ilmul Hisab Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share