22/07/2026
Mutane da yawa suna neman yalwar arziki da albarkar rayuwa. Amma Musulunci ya koyar da cewa albarka tana samuwa ne da biyayya ga Allah da bin koyarwar ManzonSa ﷺ. Ga wasu daga cikin manyan abubuwan da Al-Qur'ani da Sahihin Sunnah s**a nuna suna jawo albarkar rayuwa da arziki.
1. Tsoron Allah (Taqwa)
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
"Duk wanda ya ji tsoron Allah, Allah zai sanya masa mafita, kuma Ya azurta shi ta inda bai zata ba."
(Suratut Talaq: 2–3)
2. Yawaita Istighfari (Neman Gafarar Allah)
Annabi Nuhu (AS) ya ce wa mutanensa:
"Ku nemi gafarar Ubangijinku... Zai aiko muku da ruwan sama, Ya ƙara muku dukiya da 'ya'ya."
3. Kula da Sallah a Kan Lokaci
Sallah ita ce ginshiƙin addini kuma mabuɗin albarka. Annabi ﷺ ya ce:
"Ku sani mafi alherin ayyukanku shi ne Sallah."
3. Kyautatawa Iyaye
Kyautatawa iyaye na daga cikin manyan ayyukan da Allah Ya umarta, kuma tana daga cikin abubuwan da ke jawo albarka da rahama a rayuwar bawa.
4. Sadaka Ko Da Kaɗan Ce
Annabi ﷺ ya ce:
"Sadaka ba ta rage dukiya."
Abin da ka bayar saboda Allah, Allah Zai mayar maka da mafi alheri.
5. Riƙe Zumunci
Annabi ﷺ ya ce:
"Wanda yake son a ƙara masa arziki kuma a tsawaita masa rayuwa, to ya riƙe zumunci."
(Sahihul al-Bukhari da Muslim)
6. Yawaita Salati ga Annabi ﷺ
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yi wa Annabi salati..."
(Suratul Ahzab: ayah ta 56)
7. Yawaita salati yana daga cikin ayyukan da ke jawo rahama da sauƙin al'amura.
8. Dogaro na Gaskiya ga Allah (Tawakkali)
Annabi ﷺ ya ce:
"Da kun dogara ga Allah yadda ya kamata, da Allah Ya azurta ku kamar yadda Yake azurta tsuntsaye."
9.Gujewa Zunubai
Zunubi yana iya zama sanadin hana albarka da arziki. Annabi ﷺ ya ce:
"Lallai mutum yana iya hana kansa arziki saboda zunubin da ya aikata."
(Sunan Ibn Majah)
10. Yawaita Addu'a
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
"Ku roƙe Ni, Zan amsa muku."
A ƙarshe, ya kamata mu tuna cewa albarka ba wai yawan kuɗi kaɗai ba ce. Albarka na iya kasancewa cikin lafiya, kwanciyar hankali, iyali na gari, lokaci mai amfani, ilimi mai amfani, da wadatar zuciya. Duk waɗannan suna daga cikin mafi girman ni'imomin da Allah ke bai wa bayinsa.
Allah Ya sanya mu cikin bayinsa masu tsoronsa.
Abduljalil YM