16/01/2024
BA KOMAI BANE MALAMI ZAI FADA AGABAN ALMAJIRAN SA DA SAURAN GAMAGARIN MUTANE A MAHANGA TA SHARI'AR MUSULUNCI
An samo Hadisi ingantacce daga gun Sayyid na Abu Hurairah( R.A) Ya ce: Watarana muna gaban Manzon Allah (S.A.W.) muna zaune a bayan gari acikin mu akwai Sayyidna Abubakr da Sayyid na Umar Allah Ya kara Yarda da su, sai Manzon Allah S.A. W Ya mike Ya danyi tafiya kadan ya 6ace mana sai muka ji tsoro a cikin ran mu, gameda kada wani abu Ya sami Manzon Allah S.A.W, nine farkon wanda na mike bayan da naji haka a raina na fara neman Manzon Allah,S.A.W
ina ta neman Sa sai na gan shi a Harabar wata Katanga, Sai Manzon Allah S.A. W Ya ce Abu hurairah ne? na ce Eh ya Rasuulullah muna zaune ne sai muka ga ka tashi kuma har ka 6ace mana sai mu ka ji wani Abu a ran mu shine na biyo bayan Ka, Sai Manzon Allah S.A. W, Ya ba Abu hurairah Takalman Sa S.A W, Ya ce masa " Tafi da wadannan Takalman nawa,duk wadanda ka gani a bayan wannan ganuwa (Katanga) YA SHAIDA BABU ABUN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH YANA MAI YAKININ TA ACIKIN ZUCIYAR SA TO KAYI MASA BISHARA DA ALJANNAH" sai Abu huraira Ya dawo ya kamo hanyar dawowa gun Sahabbai yana zuwa bayan katangar sai ya gamu da Sayyidna Umar (R.A) sai Yace masa ya Abu hurairah me ya faru ya na ganka da Takalmi sai Ya ce masa Manzon Allah S.A. W Ya bani su Ya ce yiwa duk wanda ke bayan katangar nan Yana Shaidawa babu Abin Bauta da gaskiya sai Allah kuma yana mai yakinin haka a cikin zuciyar sa to in yi masa Albishir da Aljannah
Sai Sayidina Umar R.A Ya buki kircin Abu hurairah R.A ya tunkude shi har sai da ya fadi a kasa ya ce masa koma gun Manzon Allah S.A. W.
shine Ya mike yana fushi game da Abinda Umar Yay masa sai ya koma gun Manzon Allah S.A. W yana hawaye,sai Manzon Allah S.A.W Ya ce me ya same ka ya kai Abu hurairah? Shine Ya fada masa abinda Umar yayi masa to dama Umar ya biyo shi a baya sai Yace Ya Rasulullahi kai ne ka aiko shi da wannan Bishara sai Manzon Allah S.A.W Ya ce Eh.. sai Umar yace KYALE SU SU YI AIKI KAR SU SHANTAKE SAI MANZON ALLAH S.A W YA TO KYALE SU".
Hadithun Saheeh.
Har ila yau akwai wani Hadisi sahihi da aka samo daga gun Sayyidna Mu'az bn jabal( R.A) ya ce watarana muna bisa jaki tare da Manzon Allah S.A.W (Shi da ni) sai Ya ce ya Mu'az ka san hakkin Allah akan Bayi?kuma shin ka san hakkin Bayi ga Allah??
Sai na ce Allah da Manzon sa Sune Mafiya Sani, Sai Manzon Allah S.A. W Ya ce hakkin Allah akan bayi shi ne su bauta masa kuma kar su yi shirka da shi da komai( kar su yi tarayya da Allah da wani Abu, kada su hada Allah da wani) kuma hakkin bayi a wurin Allah shine: (Allah) ba zai Azabtar da duk wanda bai yi SHIRKA da SHI ba, sai na ce : Shin ba na yi wa mutane bishara ba kuwa? Sai Manzon Allah S.A. W Ya ce " Kar kayi musu bushara su zo su dogara (su shantakeda wannan Hadisi).
Imam Bukhari da Muslim su ka ruwaito.
Mahallus-Shahid a Topic din mu yanzu a cikin wadannan Haisan biyu shine BA KOWANE ABU AKE FADAWA MUTANE ABAININ JAMA'A BA KOMIN KYAU DA LADAN DA KE TATTARE DA WANNAN ABUN KU KALLI WADANNAN KALMOMI MASU KYAWO DA BABU IRIN SU KALMOMI NA SHIGA MUSULUNCI KALMOMIN DA ALLAH YA FI SO KALMOMIN DA ANNABAWA (A.S) AKA AIKO SU DOMIN SU KIRA MUTANE AKAI DOMIN TSIRA DUNIYA DA LAHIRA AMMA KU DUBI YANDA AKAI HIKIMA DON KADA MUTANE SU ZO SU SHANTAKE SU HALAKA,
TO INA GA KUMA MASU KOKARIN YADA FATAWAR ZINA (WAL IYAZHU BILLAH) DA SUNAN LALURA,TARE DA HUJJAR AN GANI A MAZHABA, A IRIN WANNAN ZAMANI DA MASU KIRA ZUWA GA ALFASHA S**A DAGE SUNA YAKAR ADDINI TA KOWACE HANYA KAWAI DON KAI NE DAN KANZAGIN MALAMI KAWAI SAI KAZO CIKIN JAHILAI KA FADA DON HUJJAR KA KAWAI WASU MALAMAN MAZHABA SUN RUBUTA TO AI SU BA DA WANNAN MANUFAR S**A RUBUTA BA, KUMA BASU CE A YADA BA, IJTIHADIN SU KAWAI KAYI S**A RUBUTA,KUMA KOWANE ZAMANI YANA DA IRIN YANDA AKE TAFIYAR DA FIQHUN DA'AWA ACIKIN SA DON KADA MUTANE SU BI SON RAN SU! SU HALAKA,KUMA BA KO INA AKE FADAR KOWACE MAGANA BA,
Sayyidna Mu'az bn Jabal bai fadi wannan Hadisin ba sai da Ya zo zai rasu ya fada saboda gudun kada ya sa6awa Allah akan 6oye Ilmi don duniya su anfana bayan sa Shi yasa Sahabbai da yawa basu san wannan Hadisin da Ya ruwaito ba,
Duk hakan ya faru ne saboda MASLAHA GA AL-UMMAN MUSULMI BAKI DAYA,
ALLAH YA KARA GANAR DA MU GASKIYA YA BA MU IKON BIN TA ALLAH YA KARE MANA IMANIN MU AMEEN.
WROTE BY ALIYU ABDULHAMID Abu Ihsan
3 Rajab
16-1-2024
27/09/2023
27/09/2023