Karatun malaman sunnah

Karatun malaman sunnah

Share

wannan shafi yana yaɗa da awar malaman Sunnah zalla, Allah kasa abinda zamu karanta ko mu saurara, Yazama sanadiyar shiriyarmu' duniya da lahira🙏

Photos from Karatun malaman sunnah's post 06/05/2026

yana daga cikin mafi girman Alkhairi da Allah zai baka kyautarsa a rayuwa shine ya sanyaka mai hidimtawa addininsa.

Allah Mai yadda yaso wato ku duba yadda zango na rayuwar Malam Ja'afar ta kasance tun daga farkonta har zuwa karshenta cikin yiwa addinin Allah hidima

Allah madaukakin sarki bai sanya Malam Ja'afar a wani abu ba face a cikin yiwa addininsa hidima..... sakamakon haka Kuma sai Allah yay mai sakamako da SHAHADA. muna addu'ar Allah ya hada Fuskokin mu a Aljannatul Firdaus 🤲

25/04/2026

MUTUWA

Ya kai ɗan Adam… ka tuna cewa mutuwa gaskiya ce, kuma babu wanda zai tsira daga gare ta. Duk wanda aka haifa, to lallai zai dandani mutuwa.
Allah Maɗaukaki Ya ce:
"Kullu nafsin dhaa’iqatul maut"
Ma’ana: Kowane rai sai ya dandani mutuwa.

Mutuwa ba ta da lokaci na musamman — ba ta jiran matashi ko tsoho, ba ta jiran mai arziki ko talaka. Sau da yawa muna ganin mutane suna tare da mu yau, amma gobe sai labarin su ya koma tarihi.

Ka tambayi kanka:
Shin idan mutuwa ta zo min yanzu, ina zan tafi?
Me na tanada domin haduwa da Allah?
Ya ɗan’uwa, ka yawaita tuba, ka kyautata ayyukanka, ka guji zalunci da cutar da mutane. Domin duk abin da ka aikata, za ka tarar da shi a ranar Lahira.

Annabi ﷺ ya ce:
"Ku yawaita tuna mai yanke jin daɗi (mutuwa)."
Domin tunanin mutuwa yana sa zuciya ta lafa, ya rage son duniya, ya kuma ƙara shirya mutum ga lahira.

Kammalawa: Ka rayu a duniya kamar bako ko matafiyi. Ka yi aiki don lahira kamar wanda ba zai mutu ba, amma ka tuna cewa mutuwa na iya zuwa a kowane lokaci.

Allah Ya sa mu cika da kyakkyawan ƙarshe (Husnul Khatima) 🤲

25/04/2026

*SALLAR DARE*

Sallar dare tana daga cikin manyan ibadodi da ke kusantar da bawa ga Allah. Ita ce ibadar da bayin Allah na gari suke ɓoye wa, suna yin ta cikin nutsuwa da tsoron Allah, ba don a gani ba sai don neman yardar sa.

Allah Ya sanya mu cikin masu tsayuwar dare, masu samun rahamarSa da yardarSa 🤲

19/04/2026

AZKAR GUDA HUƊU MASU TARIN FALALA DA NAUYIN LADA A WAJEN ALLAH

1. Manzon Allah (SAW) ya ce wa Abu Musa Al-Ash'ari: "Shin ba zan nuna maka wata kalma ba wacce take taska ce daga cikin taskokin Aljanna? Ya ce:
'Ita ce La hawla wa la quwwata illa billah'."
(Sahih Al-Bukhari, 6384)

2. Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mafi soyuwar magana a wajen Allah guda huɗu ce..."Subhanallah, Walhamdulillah, Wa la ilaha illallah, Wallahu Akbar". Waɗannan kalmomi ne da suke dasa bishiyoyi a Aljanna. (Sahih Muslim, 2137)

Ko da wacce ka fara a cikinsu babu laifi.

3. Manzon Allah (SAW) ya ce: "Duk wanda yake karanta Ayatul Kursiyyu a bayan kowace sallar farilla, babu abin da zai hana shi shiga Aljanna face mutuwa." Wato idan mutum yana karanta wannan aya bayan kowace sallar farilla, mutuwa ce kawai ta rage masa ya shiga Aljannah. (Sunan An-Nasa'i, 'Amal al-Yawm wal-Laylah, 100)

4. Manzon Allah (SAW) ya ce Faɗar: "La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli sha'in qadir" sau goma. kamar wanda ya 'yanta bayi huɗu ne daga zuriyar Annabi Isma'il (A.S). (Sahih Muslim, 2693)

Ku yi sharing:
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Allah Ya haskaka fuskar mutumin da ya ji maganata, sai ya kiyaye ta, ya kuma isar da ita kamar yadda ya ji ta." (Sunan At-Tirmidhi, 2657).

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Duk wanda ya yi nuni zuwa ga alkhairi, to yana da ladan wanda ya aikata shi." (Sahih Muslim, 1893).

Abdullahi Aliyu Boza ✍️

fans

17/04/2026

Manzon Allah (s.a.w) yace " kun ga Salloli Biyar (da ku ke yi a Rana) Suna tafiyar da Zunubai, kamar yadda Ruwa yake wanke dauda"
Al- Hadith
Ibn Maja da Imam Ahmad ne, S**a fitar da hadisin.

Ma'anar SALLOLI (5) sune sallolin Farillah da Muke yi arana sau Biyar, asubahi, azahar, la'asar, magrib, lisha'i

Ma'anar TAFIYAR DA ZUNUBAI shine Wanda yayi sallolin da kyau yadda Annabi ya koyar Allah Zai ringa kankare Masa zunubansa da ya yi Tsakanin Sa da Allah kadai, banda zunubi da ya shafi haqqin wani, wan nan Sai Idan ya yafemaka.

Wallahu Ta'ala A'alam.

Ya Allah ka Gafartamana zunuban mu, ka kankare mana Laifukanmu

✍️ Yunusa Magaji (Gombe)

Photos from Karatun malaman sunnah's post 17/04/2026

Malamai Bayin Allah ! Kowa zai yi duk abinda yake so a Nigeria amma banda malamin addini. Koda kuwa halal ne ya yi. Kowa zai kashe kuɗi ya yi suruta yadda yaga dama, idan Malami ya yi sai ace son duniya gare shi. Idan yayi Gida mai kyau sai ace son duniya gare shi.

Idan ya shiga siyasa ace baya tsoran Allah SWT, ya biyewa yan duniya. amma idan lokacin campaign yayi so ake ya fadi wanda ya kamata mutane su zaba, so ake idan wani shugaba yayi kuskure ya hau mimbari ya caccake shi, amma idan ya tsaya takara sai ace yayi kuskure.

Allah ya baku hakurin zama damu malamai, Allah ya saka muku da gidan aljanna. Ameen thumma Ameen.

Bin Mu'az Fago ✍️ Graphics Da'awah

17/04/2026

ALƘAWARIN ALJANNA DAGA BAKIN FIYAYYEN HALITTA
GA WANDA YA KIYAYE WAƊANNAN ABUBUWA BIYU

Ƴan uwa masu albarka. Rayuwar duniya tana cike da jarabawowi daban-daban, amma Ubangijinmu mai rahama bai bar mu haka ba tare da ya nuna mana hanyoyin tsira ba. Akwai wani babban alƙawari mai matuƙar daraja da fiyayyen halitta Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi wa duk wani ɗan adam da zai iya bashi tabbas a kan wasu sassa guda biyu na jikinsa.
-
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana cewa: “Duk wanda ya ɗaukar min alƙawarin kiyaye abin da ke tsakanin muƙamuƙansa biyu wato harshe da kuma abin da ke tsakanin ƙafafunsa biyu wato al'aura, to na ɗaukar masa alƙawarin shiga Aljanna (Sahih Bukhari, 6474).
-
Daga cikin wannan gajeren saƙo na fiyayyen halitta, za mu iya fahimtar waɗannan muhimman darussa kamar haka.

1. Haɗarin da ke tattare da sakar wa harshe linzami. Harshe wata ƙaramar tsoka ce wadda idan mutum bai kula ba za ta iya jefa shi a cikin halaka mai girma. Kiyaye harshe da Manzon Allah ya ambata yana nufin nisantar ƙarya da gulma da zage-zage da kuma ɓata sunan bayin Allah. Mafi yawan mutane za su shiga wuta ne saboda abin da harsunansu s**a girba.

2. Kiyaye mutunci da nisantar dukkan wani aikin alfasha. Abin da ke tsakanin ƙafafu biyu yana nufin al'aura wadda kiyaye ta shi ne ainihin cikar Izzahn mace ko namiji. Wannan yana nufin kaurace wa zina da madigo ko luwaɗi da kuma duk wata hanyar da za ta kai mutum ga biyan buƙatarsa ta haramun. Mace ko namiji mai kiyaye mutuncinsa yana da daraja a idon mutane kuma yana da kyakkyawan matsayi a wajen Allah.

3. Girman matsayin wanda ya yi nasarar shawo kan waɗannan abubuwa biyu. Idan ka lura da kyau za ka ga cewa mafi yawan zunuban da muke aikatawa a yau suna da alaƙa ne da ko dai kuskuren harshe ko kuma bin son zuciyar sha'awa. Duk wanda ya yi ƙoƙarin danne waɗannan biyun ya yi nasara a kansu, to tabbas ya gama cinye mafi girman jarabawar da shaidan ke amfani da ita ....

13/04/2026

🤲 ADDU’AR MU A YAU — ALLAH KA ZAMA GATANMU.

🤲 Ya Allah…
Mun tashi a wannan safiyar Lahadi…
ba mu da wani gata sai Kai…
ba mu da wani mafita sai Kai…

Ya Allah… Ka zama gatanmu.

🤲 Ya Allah…
Idan duniya ta juya mana baya…
Kai Kada Ka juya mana baya…

Idan mutane sun manta da mu…
Kai Kada Ka manta da mu…

Domin idan Kana tare da mu…
komai zai zama da sauƙi.

🤲 Ya Allah…
Ka zama mai kula da mu a rayuwarmu…
Ka zama mai kare mu daga dukkan sharri…

Ka zama mai buɗe mana ƙofofin alheri…
Ka zama mai sauya damuwarmu zuwa farin ciki…

🤲 Ya Allah…
A yau…

Ka shiga cikin lamuranmu…
Ka gyara mana abin da ya lalace…
Ka daidaita mana abin da ya rikice…

Ka sa mu ji cewa
Kai Kake tare da mu a kowane lokaci.

🤲 Ya Allah…
Ka cire mana tsoron da ke zuciyarmu…
Ka ba mu kwanciyar hankali…

Ka sa mu rayu cikin kulawarka
ba tare da fargaba ba.

🤲 Ya Allah…
Idan muna cikin kuskure… Ka gyara mu.
Idan muna cikin rauni… Ka ƙarfafa mu.
Idan muna cikin damuwa… Ka sauƙaƙa mana.

🤲 Ya Allah…
Ka ba mu abin da zai sa mu ce:
“Hakika Allah ya yi mana.”

Ka sa wannan rana ta zama
ranar alheri a gare mu.

🤲 Ya Allah…
Duk wanda ya karanta wannan addu’a…

koda yana jin ba shi da gata…

Ka zama gatan sa.
Ka tsaya masa a inda ya kasa…
Ka ɗaga shi daga inda ya faɗi…

🤲 Ya Allah…
Duk wanda ya rubuta ko ya yaɗa wannan addu’a…

Ka zama masa gatan duniya da lahira…
Ka buɗe masa ƙofofin arziki…
Ka haɗa shi da iyayensa a Aljannah
cikin rahama da gafara.

🤲 Ameen Ya Rabbal ‘Alameen

Idan ka ji wannan addu’a ta shiga zuciyarka…
rubuta Ameen 🤲
kuma ka tura wa wani…
domin wata zuciya ta samu gata daga Allah a yau.

Addinu Annasiha

13/04/2026

JANHANKALI: 'Dan Uwa ka yi dubi izuwaga halittun Allah Mai tsarki da daukaka musamman halittar Mutum Mai cike da abin Mamaki, Wadda aka soma ta da gudan jini, har ta Kai abinda Allah ya so ta Kai, ta zamo cikakkiyar halitta Mai karfi da hankali, da ga bisani Kuma, Allah zai Sa ta koma turbaya, kafin a tashe ta domin ayi Mata Hisabi...

Fadin Allahu SWT "Lalle Kuma Zuwaga Ubangijin ka makoma take"

Allahu Akbar, Yan uwa Ya kamata ace muna fadakuwa da abinda ake bamu labarinshi na daga Al-kur'ani Mai girma, Kowa ya gyara niyyarsa ya kuma gyara alakarsa da Allah, domin akwai mutuwa gaba garemu Kowa sai mutu Kuma Kowa Sai anyi masa hisabi.

surah Al-alaq aya ta Takwas (8).

Wallahu Ta'ala A'alam

Allah kasa muyi kyakkyawan Karshe, Allah ka Gafartamana zunuban mu ka kankare mana Laifukanmu Kasa Aljannace Makomarmu da mu da iyayenmu Da Malamanmu Da zuri'ar mu Baki daya 🤲

✍️ Yunusa Magaji (Gombe)

13/04/2026

🤲 ADDU’AR MU A YAU — LOKACIN DA BEGE YA FI MAGANA ƘARFI.

🤲 Ya Allah…
Kai ne Sarkin sammai da ƙasai…
Kai ne wanda kake ɗaukaka wanda Ka so…
Ka ƙasƙantar da wanda Ka so…

Kai ne Mai jin ƙan bayinka ko da sun yi laifi…
Kai ne Mai gafara ko da zunubi ya yi yawa…

Dukkan yabo ya tabbata gare Ka…
yabon da ya cika sararin sammai da ƙasa…
yabon da ya dace da girman mulkinka…

Mun gode Maka ya Allah…
godiya da ba za mu iya kirgawa ba…
godiya bisa ni’imomi da muka sani
da waɗanda ba mu sani ba.

🤲 Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammad ﷺ…
tsira da amincinKa su tabbata ga ManzonKa…

wanda ya fito da mu daga duhu zuwa haske…
wanda ya koya mana yadda za mu roƙe Ka…

Ya Allah Ka sa mu kasance cikin masu ƙaunarsa
da masu bin tafarkinsa da gaskiya.

🤲 Ya Allah…
Mun zo gare Ka yau…
ba da yawan ibada ba…
amma da yawan buƙata.

Ba da ƙarfinmu ba…
amma da rauninmu.

Ba da hujja ba…
amma da bege a gare Ka.

🤲 Ya Allah…
A cikinmu akwai wanda ya daɗe yana jira…
Ka kawo masa sauƙi cikin gaggawa.

A cikinmu akwai wanda ya rasa hanya…
Ka nuna masa mafita.

A cikinmu akwai wanda yake son canji…
Ka sauya masa rayuwa gaba ɗaya.

🤲 Ya Allah…
Ka buɗe mana ƙofofin arziki
ta hanyar da ba mu zata ba.

Ka ba mu abin da zai sa mu manta da damuwa…
Ka sa mu ga alherinka a rayuwarmu fili.

🤲 Ya Allah…
Ka ba mu zuciya mai tsoronKa…
zuciya mai sonKa…
zuciya mai komawa gare Ka a kowane hali.

🤲 Ya Allah…
Muna roƙonKa:

Aure mai albarka…
Arziki mai yalwa…
Gida mai cike da salama…
Zuri’a ta gari…
Lafiya mai ɗorewa…

🤲 Ya Allah…
Ka rubuta sunayenmu cikin waɗanda Ka yafe musu…
Ka saka mu cikin ’yan Aljannah…

Ka tsare mu daga wuta…
mu da iyayenmu…
mu da zuriyarmu…

🤲 Ya Allah…
Ka gafarta wa waɗanda s**a riga mu…
Ka haskaka kabarinsu…
Ka sa su huta cikin rahamarka.

🤲 Ya Allah…
Duk wanda ya karanta wannan addu’a…
yana da wata buƙata a zuciyarsa…

Ka amsa masa.

Ka ba shi abin da zai sa ya ce:
“Allah ya tuna da ni.”

🤲 Ya Allah…
Duk wanda ya rubuta ko ya yaɗa wannan addu’a…

22/03/2026

Maza ankwanta dama 😭
Allah ya haɗa fuskokin Mu a gidan aljannah fiirdausii 🤲

•Sheikh Abubakar Mahmoud gumi 🤲

•Sheik albani zaria Rahimahullah 🤲

•Sheik Ja'afar Mahmud Adam Kano 🤲

• Sheikh Ahmed B.U.K 🤲

• DR IDRIS ABDUL AZIZ DUTSEN TANSHI RAHIMAHULLAH 🤲

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Makarfi Lg
Kaduna