SHIRIN RUGA SETLEMENT
Wannan shiri da gwamnatin tarayya ta qirqiro har aka fara shirin aiwatarwa a jihar neja kafin sauran jihohi goma sha d'aya cikin goma sha biyu da s**a amince shiri ne da idan aka samu nasarar aiwatar da shi zai kawo cigaba mai alfanu ga al'ummar fulani, cigaba a yanayin kiwo a a qasarnan, cigaba a 'bangaren samar da nama mai inganci da da kuma cigaba ta fuskar tsaro a wannan yaqi na arewacin qasarnan.
Amma kash! Kwatsam sai mukaji sanarwar dakatar da wannan muhimmin shiri ta wurin mai taimakawa shugaban qasa ta 'bangaren sada zumunta wato social media, daga bisani kuma wani gwamna anan arewa ya tabbatar da ingancin sanarwar.
Haqiqa wannan sanarwa tana daga cikin sanarwar da s**a baqanta ran duk wani mai kishin qasa da kuma yankin arewa da kuma kishin zaman lafiyar arewa, sanarwa ce da ta rage wa shugabanmu qima da dajara a 'yan kwanakin nan.
Haqiqa shugaban qasa ya k**ata ya sani wallahi idan ma zanga-zanga da cecekucen mutanen kudu ne ya sanya shi d'aukar wannan mataki to wallahi sun ci shi da yaqi, domin dai su tuni kan su a ha'de yake, cigaban yankin su da al'ummarsu shine a gabansu,a yayin da mu kuma al'ummar arewa muke zaune kara-zube bamu da shugabanci, bama wakiltar yankinmu da al'ummarmu sai dai kawunamu, tunda shi ya fahimci hakan k**ata yayi duk wani shiri da ya qiraqiro wannan zai kawo mana cigaba to, duk wani kunfar baki kada ya sa ya sauka daga matsayarsa, to yin haka shine zai sa mu gano taurin kansa da tsayuwarsa ga matsayar mai anfani ne.
Mu a fahimtarmu wannan aiki na gina rugage guda shida a kowacce jiha dai dai yake da GADAR NIGER BRIDGE da akayi a yankin igbo, da kuma karrama yarbawa da akayi na maido da ranar dimokrad'iya JUNE 12 da sauran wasu manyan aiki da akayi musu a yankunasu.
Don haka 'yan'uwa mu yawaita kiraye-kiraye ga shugabanmu da ya dawo da wannan shiri har ya cigaba ba tare da tsoron kowa ba, insha Allahu kiranmu zai iya yin tasiri.
Allah ya bud'e idon shugabanmu.
Al-Ameen Abdullahi Idris.
Hisbah U/Mu'azu Da'awa Unit
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hisbah U/Mu'azu Da'awa Unit, Tutor/Teacher, Kaduna South.
DUNIYA BA MATABBATA BA CE
Kada ka miqe qafa a duniya har takai ga ka ba ta aminci da sakankancewa, domin duniya ba gida ne na aminci ba.
Idan da duniyar nan gida ne na miqe qafa ayi ta holewa, da mafificin halitta (Sallallahu Alaihi Wasallam) shine zai fi kowa yin hakan, amma yi dubi cikin yadda ya rayu, ko ka fahimci duniya kayi watsi da ita.
Haka ma d'alibansa Sahabbai (Ridhwanillahi Alaihim) basu miqe qafa ba a wannan gida, rayuwa s**a yi abar sha'awa mai ban qaye ga ma'abocin hankali da ingantaccen Imani.
Don haka d'an'uwa yi wa kanka da kanka hisabi game da yadda kake tafiyar da ragamar rayuwar ka cikin wannan gida na bandan-bandan.
**************************************
Allah ya ba mu mai kyau a duniya, da mai kyau a lahira, ya tasre mu daga azabar wuta, ya fahimtar da mu haqiqanin duniya domin cin ribar rayuwa a cikin ta.
Ameen
29/04/2018
YAYA ALAQARKA DA AL-QUR‘ANI TAKE?
Bismillahir-Rahmanir-Rahim...
Haqiqa yana da matuqar muhimmanci mu san falala da darajar Al-Qur‘ani, ta hanyar hakane zamu zamanto masu kwad‘ayin karanta shi karatu na haqiqa.
Kasancewarmu Musulmai yana da kyau mu d‘auki addininmu da matuqar Qima fiye da komai a rayuwarmu, wanda yake samun natsuwar zuci da kwanciyar hankali tare da morewa rayuwa duk ya tattara ne ga riqonmu da Addini! Ta yaya zamu kasance masu riqo da Addini? Shine ta hanyar karanta Addinin karatu na fahimta da Tadabburi!
Mu karanta Al-Qur‘ani a matsayin Ibada da kuma fahimtar ma‘anoninsa bisa fahimtar Magabata na Qwarai (Salafus-Saleh).
Lalle ne mu horar da kawunan da karatun Al-Qur‘ani.
Manzon Allah (S.A.W) yace ((“Duk wanda ya karanta Harafi d‘aya acikin littafin Allah (Al-Qur‘ani), to yana da lada d‘aya da kwatankwacin goma irinsa.
[TIRMIDHI].
Shin ni, kai shi, ita, su da mu duk a kowanne yini muna karanta Al-Qur'ani? Lallai akwai sakaci mai yawa tare da shagala, gami da nesanta kai ga rahamar Allah ga duk wanda ya nesanta kansa da Al-Qur'ani, ta hanyar koyon shi, karanta shi domin neman lada (Ta'abbudan), ko kuma Qoqarin sanin ma'a'noninsa.
Da damar mutane a yau mun mayar da karatun Al-Qur'ani yana taqaituwa ga wanda ya rasa abinda zaiyi, to sai ya d'auka ya d'an karanta. (da zaman banza, gara aikin....)
Ya za'ayi ka gane haka? Inda zaka zo ka zauna a Masallaci bayan Sallar Azahar ka d'auki Mus'haf kana karantawa, yau a ganka, gobe, jibi ma haka, sai kaji ana cewa: wane bashi da aikin yi ne? Saboda mun Qudurce karanta Al-Qur'ani sai wanda ya rasa abin yi ne yake karanta shi.
To wannan ma fa masu Qoqari kenan! Domin akwai wanda daga Ramadhana sai Ramadhana ne kawai suke karantawa, wani ko Wlh rabon shi da ya karanta Al-Qur'ani tun yana Qarami. (Wal-Iyazu Billah).
Wannan ba Qaramar asara bace! Mutum ya samu kansa cikin masu Qauracewa Al-Qur'ani.
**********************************
Allah ya sanya mu cikin masu karanta Al-Qur'ani.
'YAN'UWA MU JI TSORON ALLAH!
A duk nau'uka na wa'azi babu abinda ya fi ace maka kaji TSORON ALLAH! Duk wanda yace da kai kaji tsoron Allah ya gama yi maka wa'azi
Umar Bin Khattab (Radhiyallahu Anhu) Ya ta'ba aikawa d'ansa Abdillahi Bin Umar (Radhiyallahu Anhuma) da wasiqa.
Ga abinda yake cewa: "Bayan haka: Lallai ni ina yi maka wasiyya da kaji tsoron Allah Mai Girma da 'Daukaka, yadda al'amari yake, duk wanda ya ji tsoron Allah to sai ya kare shi, duk wanda ya ba Allah rance sai ya biya shi, duk wanda ya godewa Allah sai ya Qara mi shi.
intaha.
Haka Aliyu Bin Abi Talib (R.A) ya yi wasiyya ga wani mutum yake ce mi shi: "Ina yi maka wasiyya da kaji tsoron Allah Mai Girma da 'Daukaka, wanda yake babu makawa kana komarsa, ba ka da makoma a gare ka sa'baninshi, shine mamallakin duniya da lahira.
Duba: (KITABUL-ILMU, na Sheikh Uthaimin: shafi na 39)
'Yan'uwa nima ina yi muku da kaina wasiyya da muji tsoron Allah a dukkan al'amuranmu, Allah yana tare da mai jin tsoron shi.
*********************************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, ya sa mu cikin bayinsa masu tsoronsa a bayyane da 'boye.
Ameen
Kyautatuwar zuciya tare da nagartattun ayyukan ga'b'bai sune ke tabbatar da gaskiyar imanin mutum mai da'awar imani.
Da'awa kawai ba ta isuwa har sai ayyukan ga'b'bai sun bayyana, da haka ne kawai za'a gaskata ko a qaryata da'awar imanin mutum.
Ba ya yiwuwa ka zamo mai bayyana munana sannan ka ce ai wai ai imani a zuciya yake, tabbas gaskiya ka fad'a amma kai qarya kake yi, domin inda abinda ke zuciyar ka mai kyau ne da ayyukan bayyanen ka sun tabbatar, amma da yake mummunan ne sai mummunan ne ya bayyana.
Da yawa zaka ga mutum ya aikata wasu ayyuka marasa kyau, da zarar ka nusar da shi sai yace da kai ai "At-Taqwa Ha'huna".
Allah mai iko! Ai da taqawar ce a zuciyarka da kayi aikin dake tabbatar da taqawar.
Don haka 'yan'uwa mu tsarkake zuciyoyinmu, sannan mu inganta imaninmu, domin ta haka ne kawai zamu samu dacewa duniya da lahira.
***********
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, ya kuma azurta mu da kammalallen imani.
Ameen
DUNIYA KWANA UKU CE
Duniyar nan gaba d'ayanta kwana uku ce:
Jiya, yau sai kuma gobe.
*JIYA:
Wannan ta wuce, ya rage naka, ka ribace ta ko kuwa ka bari ta wuce haka nan.
*YAU:
Wannan kam itace kad'ai damarka, itace kawai kake da dama a cikin ta, domin ganin ka aikata ayyukan d'a'a ga Allah domin samun rabauta.
*GOBE:
Wannan gaibu ce domin ba ka da tabbacin kaiwa goben, kaga ba ka da tabbas.
Ashe mai wayo da hankali shine wanda zai yi kwad'ayi tare da jajircewa matuqa wajen ribatar yau d'insa da ayyukan d'a'a.
Lallai ne ga duk mai son rabauta a duniyar nan ya dinga yin taka-tsan-tsan cikin dukkan ayyukansa da yake aikatawa, ya kasance a kowanne lokaci cikin ayyukan d'a'a, domin dai mutum bai san yaushe ne ranar mutuwarsa ba.
'Dan'uwa ba ka san yaushe ne zaka mutu, a ina ne zaka mutu, a kan wanne aiki zaka mutu ba.
Don haka sai ka nesanci wuraren sa'bon Allah, ka nesanta kanka daga duk wani wuri da Allah bai yarda ya ganka ba, domin dai za'a tashi mutum ne akan abinda ya mutu a kansa.
*******
Allah ya kyautata qarshenmu, ya sa mu cika da kalmar: (La Ilaha-Illallah Muhammadur-Rasulullah).
Ameen
RAYUWAR DUNIYA KENAN!
A kowanne lokaci ka yi kyakkyawan tunani da nazarin wannan rayuwa to, sai ka yi tsinkaye da wani abu na wa'azi da tunatarwa.
Babu wani lokaci da zan samu natsuwa inyi kasaqe... cikin yanayin tunani da nazarin rayuwar duniyar nan, face sai na samu gamsuwar cewa lallai duniya gidan rud'u ne kawai da hayaniya, tare kuma da wahala.
Duniya dai babu yadda zakayi sai ka rayu a cikinta har zuwa cikar ajalinka, tunda ga ka dai a cikinta! Ka tasa duniya a gaba ka zamo bawanta, hajar Allah kuma ta ku'buce maka.
Ka sake ta gaba d'aya kayi asarar duniyar da kuma lahira. To, yaya zakayi kenan?
Idan ka tashi neman duniya ka neme ta k**ar zaka dawwama a cikinta (k**ar ba zaka mutu ba), to haka kuma idan ka kaje wurin bautar Allah ka bauta masa k**ar gobe ne qiyama, to da wannan insha Allah zaka rabauta.
Ma'ana:
Ka da ka zamo jajircacce wajen neman kud'i babu kasala, amma a wurin bautar Allah ka zamo koma baya baka jajircewa, kana kasala, domin wannan siffa ce ta munafukai.
A'a ka zamo mai qoqari wajen neman halal kuma mai qoqari wajen neman aljannah.
Idan ko ba haka ba, zaka rayu cikin wahala da rashin sanin mafita a rayuwa, sannan ka rayu cikin rashin walwala da hutu a rayuwa.
****************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, yasa mu bauta masa yadda yake so, ya kuma ba mu alkhairan duniya da na lahira.
Ameen
MANUFA
Manufa:
Itace mutum ya dinga gudanar da al'amuransa bisa tunani da hangen nesa gami da ilimi, tare da tafiya kaifi d'aya koda ayyuka sun banbamta.
Mutum mai manufa ba ka samunsa da kasala wajen tunkarar duk abinda ya tasa a gaba:
* Nagartacce ne shi ta kowanne 'bangar idan ka auna shi
* Zaka same shi cikin nutsuwa cikin dukkan lamuransa koda ana cikin rud'ani
* Mai bawa lokaci muhimmanci ne a duk inda ka same shi
* Yana anfanar kansa, danginsa, al'ummarsa da qasarsa.
Mai manufa baya tsoro, baya ja da baya don ya samu tasgaro.
Mutum mai manufa abin so da sha'awa ne ga kowanne nagartaccen mutum.
Mu zamo masu manufa a rayuwa domin zamowa masoya ga mahaliccinmu.
***********************************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaici.
Ameen
DUNIYA BA A BAKI AMANA
Duk wanda ya ba wa wannan mata (duniya) amana to, haqiqa zai yi nadama.
Domin ba ta da tabbas, ba ta ragawa ko ta sassautawa bawa yayin da ta yi shirin maka shi da qasa.
Ita dai mayaudariya ce, idan ka aure ta itace zata sake ka idan ma kai baka sake ta ba, nawa ta saka a idonka kana kallo d'an'uwa! To, kaima kayi taka-tsantsan da ita, shekarun da zata d'an ara maka 'yan kad'an ne, shekaru hamsin sittin ko saba'in ne, a cikin su idan kai mai wayo ne sai ka ribace wajen gina haqaiqanin gidanka na tabbas wato (gidan lahira).
Yanzu zaka had'a shekaru hamsin, sittin ko saba'in da shekaru har abada?
'Dan'uwa ka sani shekarun da zaka yi a duniyar nan na d'an jin dad'inta (idan ma kana daga cikin masu d'an jin dad'in) shekaru hamsin ne ko sittin ko kuma saba'in.
Su ma shekarun ba a gaba d'ayansu ne zaka ji dad'in ba, a'a a wasu daga cikin su ne.
Domin tun daga lokacin da aka haife ka har lokacin da balaga tazo maka ai baka san komai na gard'in duniya ba don ba ka ma da hankali.
Tun daga lokacin da ka balaga har lokacin da ka kai d'an shekaru arba'in ai ba kan wani dad'in duniya ba, domin kana cikin gwagwarmayar tara abin duniya ne domin 'ya'yanka.
Kafin ma ka kai haka! A baya kana cikin gwagwarmayar neman ilmi ne ko koyon sana'ar da zaka riqe ka rufawa kanka asiri.
Ka kammala karatun ko koyon sana'ar, ka bazama neman aiki da kafuwa a sana'ar, duka fa wannan ba'a ma samu duniyar ba gwagwarmaya kawai akeyi.
Duniyar ta samu (idan ma an dace) a lokacin da ake shirin miqe qafa a lasa sai mutuwa ta qwanqwasa qofa kuma dole a bud'e, idan ma mutuwa ba ta zo ba dole tsufa ya doka sallama (Ya Sallam).
Yanzu don Allah d'an'uwa akan wad'annan 'yan shekarun na duniya masu cike da wahalhalu da tarnaqai iri-iri zaka yi sakaci da rayuwar da bata da iyaka? (Rayuwar lahira)?.
Ai mai lafiyayyen hankali da qwaqw-Qwaran tunani ba zai yarda akan wannan gajeruwar rayuwar ya 'barar da rayuwar aljanna ba, zai dage iya wiya yaga yayi nasarar cancantar shiga wancan gida na lambu da kayan morewa rayuwa da gwangwajewa (gidan aljannah), ba zai bari ya watsarda gidan sa na din-din-din akan wannan gida wucin gadi ba.
**********************
Allah ya bamu ikon yin anfani da wannan gida na duniya wajen samun rayuwar hutu da jin dad'i na gidan aljannah, ya bamu ikon yin watsi da sha'awowi na wannan gida wad'anda ke sabbabawa bawa afkawa haramun da kusa-kurai.
Ameen
ME YAYI KYAWUN ILMIN DA AIKI NE KE QAWATA SHI...
...Rajaa'u Bin Haiwah!
A zamanin tabi'ai akwai wasu manyan malamai su uku 'yan qabilar "KINDATA", wad'anda Wani daga cikin magabata (Rahimahullahu) yake cewa game da su:
(A qabilar kindata akwai wasu mazaje uku wad'anda Allah yake saukar da ruwan sama saboda su...
Kuma yake ba da nasara akan maqiya dominsu...
Daga cikinsu akwai RAJAA'U BIN HAIWATA)
Wad'annan mazaje sun tafiyar da rayuwar su wajen hidima ga addinin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam), da ma d'aukacin muminai baki d'aya.
Wad'annan mazaje sune:
1) Muhammad Bin Siyriyn A Iraqi
2) Al-Qasim Bin Muhammad Bin Abiy Bakrin A Hijaaz
3) Sai na uku wanda muke magana a kan sa Rajaa'u Bin Haiwah A Sham.
Rajaa'u bin haiwah tabi'i ne abin buga misali a nagartacciyar rayuwa ta fuskar tsoron Allah da Ilmi, gami da kaifin hankali da basira gami da hikima.
An haifi Rajaa'u bin haiwah a wani gari da ake kira ((Biysaan)) a qasar ((Falasd'in))...
An ko haife shi ne a qarshe-qarshen Khalifancin khalifah na uku wato Uthman Bin Affan (Radhiyallahu Anhu) ko kuma wani abu mak**ancin haka.
Ya kasance ana danganta shi ne da qabilar (Kindata) daga qabilar larabawa.
Wannan bawan Allah Rajaa'u ya taso tun daga quruciyarsa ne cikin yin d'a'a ga Allah tsawon shekarun da yayi a rayuwarsa, ya kasance masoyi ga Allah kuma Allah ya sanya soyayyar shi ga halittunsa.
Shi wannan bawan Allah rajaa'u bin haiwah ya riqi ilmi da damatsan haqoransa, inda ya d'auke shi abu mafi muhimmanci a gare shi, ya sanya mafi qololuwar himmar shi shine karantawa, fahimta da aiki da littafin Allah (Al-Qur'ani), kuma yayi guzuri da hadithan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Wannan tasa fikirarsa ta d'oru akan hasken Al-Qur'ani....
Basirarsa ta haskaku da shiriyar Annabta...
Qirjinsa ya cika da wa'azuzzuka da hikima... Wanda ko duk aka ba shi hikima kai haqiqa an bashi alkhairi mai tarin yawa.
Wannan tabi'i Rajaa'u Bin Haiwah ya samu horo da gogewa ta addini da ilmi a wurin tarin Sahabbai, wad'anda s**a had'a da:
* Abu Sa'id Al-Khudriy
* Abir Darda'a
* Abu Umamah
* Ubadata Binisw-Swamit
* Mu'awiyata Bin Abiy Sufyan
* Abdullahi Bin Amru Binil Asw
* Da Nawwasi Bin Sam'an,
da wasun su.
Rajaa'u Bin Haiwah ya kasance a wani lokaci saboda kyawun wankuwar zuciyarsa, da tulin tarin shiriyarsa, da daddad'an tataccen gangariyar madarar imanin da ke gudana a tsaftatacciyar zuciyarsa yana cewa:
مَا أَحْسنَ الإِسلام يزِينُهُ الإيمان...
ومَا أَحْسنَ الإيمان يّزينُهُ التّقَى...
ومَا أَحْسنَ التُّقَى يَزِنُهُ العِلمُ...
ومَا أَحْسنَ العِلمَ يَزِينُهُ العَمَلُ...
ومَا أَحْسَنَ العِلمَ يَزِنُهُ الرِّفقُ...
Ma'ana:
Menene yayi kyawun musuluncin da imani ne ya qawata shi...
Menene yayi kyawun Imanin da taqawa (tsoron Allah) ne ya qawata shi...
Menene yayi kyawun taqawar da Ilmi ne ya qawata ta...
Menene yayi kyawun Ilmin da aiki ne ya qawata shi...
Menene yayi kyawun aikin da tsai-tsaini ne ya qawata shi...
Haqiqa wad'annan gwalagwalan kalmomi ne da ya kyautu ma a rubuta su da alqalamin zinare, yi dogon tunani cikin wad'annan kalmomi ka ga dogon tunani da tsoron Allah gami da tarin hikima ga wanda ya furta su.
Lallai wannan tabi'i Rajaa'u Bin Haiwah ya kasance tabi'i abin koyi ga duk mai fatan samun abin koyi nagari, kuma yake neman shiriya.
To haka zaka iske rayuwar dukkan Sahabbai (Radhiyallahu Anhum) da tabi'ai da atba'uhum, duk wanda ka d'auki tarihin rayuwarsa ka karanta sai ka ga wasu ababen koyi kyawawa a gare shi, tare kuma da abubuwan da zasu qara maka tsoron Allah da ganin qasqancin gidan duniyar nan.
******************************
Allah ya qara musu yarda ya shiryar da mu akan tafarkin shiriyarsu, ya tabbatar da mu akan tafarki madaidaici.
Ameen
MAGABATA NA QWARAI ABABEN
KOYI
(سلفو الصالح)
Magabata na qwarai sun buga mana misali mai girma, game da tanadin lahira na guzurin aikin alkhairi da dukkan nau'ukansa, na daga aikin zuciya ne, ko maganar harshe, ko ayyukan ga'b'bai...
Ba su bar wata qofa ta daga qofofin alkhairi ba face sun yi tserereniyar/musabaqar shiga cikinta, kuma basu bar wata qofa ta daga qofofin sharri ba face sun tsoratar da junansu da shiga cikinta...
Duka wannan fa domin su buga mana misali ne na maganar gaskiya ta Allah Subhanahu Wata'ala.
Inda Allah yake cewa:
(بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ)
(وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ) *
(الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ)
*
(وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَىٰ مَا فَعَلُوا
وَهُمْ يَعْلَمُونَ)
*
(أُولَٰئِكَ جَزَاؤُهُمْ مَغْفِرَةٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَجَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ)
(Suratu-Aali Imran: 133-136).
Ma'ana:
Kuma kuyi gaggawa zuwaga gafarar ubangijinku da wata aljannah da fad'inta ya kai sammai da qassai an tanade ta ne domin masu taqwa
* Su ne wad'anda suke ciyarwa a halin rashi da wadata kuma masu had'iye fushi masu yafiya ga mutane ٌ Allah yana son masu kyautatawa
* Kuma sune idan s**a aikata alfasha ko s**a zalunci kawunansu sai su tuna Allah su nemi gafarar zunubansu domin sun san babu mai gafarta zunubai sai Allah basa komawa su qara aikatawa alhali suna sane
* Wad'annan sak**akonsu shine gafara daga wurin ubangijinsu da aljannah wacce qorama ke gudana a qarqashinta zasu dawwama acikinta madalla da sak**akon masu aiki).
Sun kasance tanadin su na su tsinkayi Allah ne basa togacewa a 'bangaren furuci da bakunansu ke furtawa kawai ba, ba kuma a ibadar zuci ba a'a ga'b'bansu suna aikata duk abinda Allah ke so ne a halin so ko qi saboda d'a'a ga Allah.
Lisanil haal din kowannensu yana cewa:
(وَعَجِلْتُ إِلَيْكَ رَبِّ لِتَرْضَ)
Suratu-Taha: 14.
Haka zaka iske su kowannensu yana yin aiki domin Allah (Iklasw), domin sun karanta fad'in Allah:
(اَلاَ لِللَّهِ آدِّينُ آلْخَالِص)
Suratuz-Zumar: 3.
Da fad'in Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam):
"((إن الله لا يقبلُ من العمل إلا ما كان خالصًا وابْتَغِي به وخهه))
(Nasa'i: 2/25)
Ma'ana: Lallai Allah baya kar'ba daga aiki sai wanda ya kasance anyi shi don Allah (da ikhlaswi) kuma aka nufi fuskar Allah da shi.
Ibrahimut-Taymi (rahimahullah) yana cewa: Mai ikhlaswi shine wanda yake'boye kyawawan ayyukansa k**ar yadda yake'boye munana.
Aliyu Bin Abiy Dalib (radhiyallahu anhu) yana cewa: "Ku saka lahira a gaba, ku jefa duniya baya, ku zamanto daga 'ya'yan lahira, kada ku zamo cikin 'ya'yan duniya, domin yau rana ce ta aiki babu sak**ako, gobe kuwa ranar sak**ako ce babu aiki.
Don qarin bayani duba littafin: Rihlatu Ilad-Daril Akhirah: 9-13.
'Yan'uwa wad'annan magabata sune kad'ai ababen koyinmu, duk abinda bai zama addini a zamaninsu ba to, babu yadda za'ayi a yau ya kasance addini, duk wanda yayi riqo da shiriyarsu shine ya k**a dahir kuma shine haqiqanin shiryayye.
Don haka haka muyi iyakacin iyawarmu wajen ganin mun d'ora rayuwarmu akan tafarkinsu domin tsira duniya da lahira.
(فتشبهوا إن لم تكنوا مثلهم * إن التشبه بالكرم فلاح
*********************************
Allay ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, ya tabbatar da mu akan tafarkin magabata na qwarai har mutuwa, wad'anda ke'batanci a gare su kuwa Allah ya shiryar da masu rabo acikinsu.
Ameen
ٌ
MU GODEWA ALLAH AKAN NI'IMAR ZAMAN LAFIYA
Idan babu wani alkhairi da a wannan gwamnati sai tasirin samar da zaman lafiya to, ya isa abin mu yaba ba la'anta ba
'Yan'uwa mu zamanto masu godiya ga Allah ta'ala a kowanne lokaci.
A ramadhanan bara Masallatai nawa ba'a yi I'itikafi ba amma bana akeyi?
Menene ya hana ba'ayi I'itikafin ba a bara kuma me yasa bana akeyi?
Pls kada mu zamanto masu butulci ga ni'imar Allah, mu gode masa sai ya qara mana aminci da arziqi.
Allah kada ka k**a mu da abinda wawayen cikin mu suke aiakatawa, ka kar'bi ibadunmu baki d'aya domin tsarkin sunayenka.
Ameen
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Telephone
Website
Address
Kaduna South