21/05/2026
SUBHANALLAHI: Wannan yaron da kuke gani Bahaushe ne musulmi ɗan kimanin shekaru 3, kuma an gano shi ne a hannun wata mata ’yar kabilar Igbo a unguwar Mando da ke Jihar Kaduna.
Mutane sun fara zargin matar ne bayan sun lura yaron na jin Hausa sosai, alhali matar Inyamura ce. Da farko matar ta ce daga gidan marayu a Nasarawa ta karɓo shi, amma daga baya ana zargin ta amsa cewa ta sayi yaron kan Naira miliyan 2.5.
Yanzu haka jami’an State CID sun karɓi binciken lamarin domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma asalin yaron.
Ku taya mu yaɗa wannan labarin ko za a samu wanda ya san yaron, don a mayar da shi hannun iyayensa.
11/05/2026
04/05/2026
04/09/2022