29/08/2017
WAJIBI NE A HALARTO SALLAN
JUMU'A IDAN TA
HADU RANA DAYA DA IDI.
::
Imamu Malik da Abu Hanifa sun
ce idan sallan
jumu'a da idi sun kasance a
rana daya shari'a
tana umurtan dukkan mutumin
da ya kai hadin
balaga da ya halarci sallan
Jumu'a da na Idi, shi
sallan Idi Sunna ne shi kuma
sallan Jumu'a
farilla ne, domin haka dayansu
ba zai yiwu ya
maye daya ba, wannan shine
asali. Lallai an
samu sabani a wajen Malaman
Mazahabobi
mafiya shahara guda hudu,
amma guda uku daga
cikinsu sun tafi akan cewa
haduwan sallan
Jumu'a da Idi rana daya bai
zamowa hanzarin da
zai saryar da Sallan Jumu'a,
Malaman da s**a
tafi a kan wannan matafiya
sune: Imamu Malik da
Imamu Shafi'i da Abu Hanifa.
babbban dalilin da
jamhurin Malamai suke kafa
hujja a kai shine:
Na farko
Ayan Alqur'ani na cikin Suratul
Jumu'ati Aya Na
09
ﻳﺄﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺀﺍﻣﻨﻮﺍ ﺇﺫﺍ ﻧﻮﺩﻱ ﻟﻠﺼﻼﺓ ﻣﻦ
ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ
ﻓﺎﺳﻌﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻠﻪ
Abun da s**a kafa hujja da shi
shine wannan aya
tana umurni ne da a tafi zuwa
Jumu'a ida aka
kira salla a ranar Jumu'a, kuma
wannan ayan
tayi umumin dukkan ranakun
Jumu'a ba tare da
ta kebance wani rana ba, don
haka bai hallata a
kebance wata rana daban ba
matukar babu wani
ingantacen dalili da ya kebance
wannan nassi
kad'i ba.
Na Biyu
Ba'a samu wani hadisi
ingantace da aka ruwaito
cewa Annabi Sallan Lahu Alaihi
Wasallam ya bar
Sallan Jumu'a saboda ta
kasance rana daya da
Idi ba. An samu hadisi ingantace
daga Nu'uman
bn Bashir yana cewa: Manzon
Allah Salla Lahu
Alaihi Wasallam ya kasance a
cikin Sallan Idi
guda biyu (karamar Sallah da
bubban Salla) da
kuma Sallan Jumu'a yana
karanta suratul A'ala
da suratul Gashiya, ya kuma
kasance idan Idi da
Jumu'a s**a hadu a rana daya
yakan karanta
wadanan surorin a cikin sallan
Idi sannan ya
kuma karantasu a Sallan
Jumu'a. Wannan dalili
ne da yake nuna cewa Annabi
Sallan Lahu Alaihi
Wasallam, yana aikata Sallan Idi
sannan ya kuma
aikata Sallan Jumu'a a rana daya
kowanne kuma
a lokacin shi, don haka duk
abinda ya saba ma
abinda Annabi Salla Lahu Alaihi
Wasallam ya ke
aikatawa ba zai zamo Sunna ba.
Lallai an samu ruhsa ga
wadanda suke zama a
kauyukan da ya wuce mil uku
daga birni, Idan
s**a halarto Idi a ranar Jumu'a
ba sai sun kuma
dawowa Sallan Jumu'a ba
saboda hadisai kamar
haka:
Na Farko:
An karbo daga Abu Hurairata
Radiyallahu Anhu,
Lalle Manzon Allah Salla lahu
Alaihi Wasallam ya
ce “Haqiqah idi biyu sun hadu a
wannan rana,
duk wanda ya so, wannan idin ta
isar masa daga
sallan juma'a, amma mu kam
(Mutanen Madina )
za mu sallaci juma'ar” (Abu
Dawud 1\281),
Na Biyu:
An karbo daga Abi Ubaid Maula
ibn Azhar ya ce
“Na halarci idi tare da Usman bn
Affan, kuma ya
kasance wannan ranar ranar
Juma'a ce, sai ya yi
sallah sannan ya yi Khudba
kuma ya ce “Ya ku
mutane Haqiqah idi biyu sun
hadu maku a
wannan rana, duk wanda yake
so ya saurari
Juma'a daga mutanen kauye ya
saurara, wanda
ya ke so ya tafi, to hakika nayi
masa izni
(Bukhari 7\134, Fathul Bary
10\29 Hadisi na 5572,
Muwatta Malik 1\190). Abin da a
ke nufi da Awali
shi ne, kauyukan da su ke gefen
Madina,
wadanda su ka kai Mil uku ko
fiye da haka.
Daga cikin Malaman
Mazhabobin nan Imamu
Ahmad ne kawai ya yi umumin
wannan ruhsan
cewa har da mutanen da suke
zama a birni ba
dole sai sun yi Sallan Jumu'a a
ranar Idi ba idan
s**a halarci Sallan Idin.
Dole ne mu mabiya Mazhaban
Imamu Maliki
mubi fatawar cewa wajibi ne Mu
halarci Sallan
Jumu'an idan ta kasance rana
daya da Idi,
saboda dalilai kamar haka:
Na Farko
Mu mutanen yamma, muna bin
Mazhaban
Malikiyya ne, kuma a Mazhaban
Malikiya
haduwan Idi da Jumu'a rana
daya bai zamowa
hanzari da zai saryar da Sallan
Jumu'a, Imamu
Khalil mai littafin mukhtasar ya
jero a cikin jerin
abubuwan da ba su zamowa
hanzari na rashin
halartan sallan jumu'a, sai ya ce:
( ﺃﻭ ﺷﻬﻮﺩ ﻋﻴﺪ ﻭﺇﻥ ﺃﺫﻥ ﺍﻹﻣﺎﻡ )
Ko halartan Idi ko da sarkin
musulmi ya yi izini
ga mutane cewa ba sai sun
halarto Idi ba.
Na Biyu
Dole ne mu halarci sallan
Jumu'a a ranar Idi
saboda Annabi Salla Lahu Alaihi
Wasallam bai
taba barin Sallan Jumu'a don ta
zamo rana daya
da Idi ba, kuma wannan al'ada
ita ce muke kanta
a wannan yanki namu, sannan
ma ni ban ga wani
gwaninta ba don mutum bai je
Jumu'a ranar Idi
ba domin ko Malaman da s**a
ce ta saraya ai
ruhsa s**a ce, don haka
halartan Jumu'an ya Fi.
ALLAH YA MUNA MANA WANNAN
RANA (IDIN BABBAN), LAFIYA YA KARAMANA SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAW),
AMEEEEEEEEN SUMMA AMEEEEEN.