15/06/2026
🕌📖 ALHAMDULILLAH! AN KAMMALA TADRIBUL QUR'AN 📖🕌
SCHOOL FOR QUR'ANIC MEMORIZATION TRAINING.
Alhamdulillahi Rabbil 'Alamin, cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki an samu nasarar kammala shirin Tadribul Qur'an cikin nasara da kwanciyar hankali.
Muna miƙa godiya ta musamman ga malamai, ɗalibai, iyaye da dukkan waɗanda s**a bayar da gudunmawa wajen ganin wannan shiri ya gudana cikin nasara.
Allah Ya saka wa kowa da alkhairi, Ya sanya abin da aka koya ya zama hujja a gare mu ba hujja a kanmu ba, Ya ƙara mana fahimta da riƙo da Al-Qur'ani Mai Girma.
"Mafificin ku shi ne wanda ya koyi Al-Qur'ani kuma ya koyar da shi."
🤲 Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya albarkaci iliminmu, Ya sa Al-Qur'ani ya zama haske a zukatanmu.
✨ Tadrib ya ƙare, amma tafiyar koyon Al-Qur'ani ba ta ƙare ba.
📖🤍🕌 Abdurrashid M. Sh*tu Bashir Lawal fans