01/10/2022
Ba'a❌
Ba a ☑️
Ba a❌
Ba'a☑️
Da yawa za su ce me nake nufi? A misali na farko ana rubuta ba a ne a rabe. Wato. Ba a zuwa gaban Audu Ciwake da mace.
A misali na biyu kuma ba'a, kalma ɗaya ce, wato yi wa wani ba'a. Misali: Ba'a nake yi wa Ciwake da na ce ba a zuwa da mace wurin shi.
: Misali na farko 'ba' ta zo ne domin korewa, wato a'antawa, shi ya sa ba a haɗa ta da 'a' da ta gabace ta ba.
Misali na biyu kuma, kalmar suna ce ba'a, wadda tana daga cikin rukunnan adabin Bahaushe. Misali: Kanshi kamar goruba.
Ba a yarda a shigar da labarin ba'a a cikin rubutun ba.
Mubarak Idris Jikamshi ✍️