22/12/2021
"A taƙaice!
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rayu shekara 63 a duniya. Shekara 40 kafin aiko shi a matsayin Annabi. 23 kuma a matsayin Annabi Mursali. Ya shafe Shekara goma sha uku (13) a garin Makkah. Shekara 10 a garin Madina.
Shekara Uku Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi yana kiran mutane a ɓoye, 10 kuma a bayyane a garin Makkah.
Yaƙin Badr, shekara ta 2 bayan Hijra.
Yaƙin Uhud, shekara ta 3 bayan Hijra.
Banun Nadhir, shekara ta 4 bayan Hijra.
Ahzaab, shekara ta 5 bayan Hijra.
Sulhul Hudaibiyya, shekara ta 6 bayan Hijra.
Khaibar, shekara ta 7 bayan Hijra.
Fat'hu Makka da yaƙin Hunain, shekara ta 8 bayan Hijra.
Yaƙin Tabuka, shekara ta 9 bayan Hijra.
Hajjin ƙarshe ta Ma'aiki, shekara ta 10 bayan Hijra.
Wafatin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, 11 bayan Hijra."
Sukairaj Hafiz Imam
11/12/2021
11/12/2021