24/03/2024
BASALAFE ( SALAFĪ )_____ A TAKAICE !
A takaice , idan kaji ance " Basalafe ( koko "Salafī " ) , to ana nufin mutumin da yake riko da Littafin Allãh al Qur'ãni da kuma Sunnah ta Manzon Allãh [ صلى الله عليه و آله وسلم ] a bisa fahimta da kuma karantarwar Magabatan mu Salaf ( Sahabbai da Tãbi'ai, da kuma Tãbi'ut Tãbi'īn , da sauran malaman Sunnah wadanda s**a biyē masu da kyautatawa).
Kuma ita da'war Salafiyyah , ba Kungiya bace , ba kuma wata Tarīqah bace. Hãsali mã ita wannan da'war , tana fada ne da ko wace irin Kungiya , ko kuma Tarīqah !
Hakanan kuma shi Salafī ( ahlus Sunnah na gaskiya ) , baya tare da duk wani malamin da aqīdar sa , ko karantarwar sa , ko kuma wani ra'ayi nasa da ya sabawa na Magabatan mu Salaf !
Ba zaka taba sãmun Salafī na gaskiya yana da wata aqīdah ko kuma wata fahimta wadda ta sabawa fahimtar Magabatan mu Salaf ba. Idan kuwa har kaga haka ta faru , to wannan sai dai akan kuskure ____ amma ba akan ganganci ba !
Dõmin da ya gane kuskuren sa , ya fahimci cewa akan kuskure yake , to in shã Allãh zaka ga yayi gaugawar dawowa zuwa ga gaskiya ____ zuwa ga abinda Magabatan mu Salaf s**a tafi akai , na aqīdah da kuma manhaji !
Shi ahlus Sunnah na gaskiya ( Salafī ) , baya "talawwuni " (watau rikida ). Baya cewa shi Salafī ne a aqīdah , amma kuma a manhaji ka same shi lkhwãnī , ko Hizbī ( tanzhīmī), ko kuma Surūrī , duk a lõkaci guda _____ dõmin irin wannan rikidar ,wani nau'i ne na nifãqah ( munafunci ) !
Shiyasa ita wannan da'war , bata yarda da dukan wani tsari , ko fahimta , ko wani ra'ayi , ko kuma wata aqīdar da ta saba mata ba. Dõmin ita wannan da'war , itace da'war Musulunci ta asali ,itace Musulunci tatacce wanda bãya da wani gauraye da duk wata aqīdah , ko kuma wani tsari na rãyuwa wanda ya saba nasa !
Shiyasa lmãm Muhammad Nãsiruddīn al Albãnī ( rahimahullãh) yake cewa :
" الدعوة السلفية هي الاسلام , بالمفهوم الصحيح " !
Watau :
"Ita da'war Salafiyyah , itace mã Musuluncin na gaskiya, a fahimta ingantacciya