17/09/2025
🌿📌 Post 20: Ciwon Daji na Mahaifa da Mama Wanda a Turanci ake Kira da (Cervical/Breast Cancer)
Cutar daji da ke shafar mahaifa ko Maman Mace. Itace babbar cutar da ta fi kashe mata a faɗin duniya.
Alamun Cancer Mahaifa (Cervical cancer):
1. Zubar jini bayan al’ada, bayan saduwa, ko bayan tsayuwar al’ada
2. Fitar ruwa mai wari daga farji
3. Zafi a ƙasan ciki da baya
Alamun Cancer Mama (Breast cancer):
1. Ƙulli mai tauri a Maman Mace
2. Canjin siffar Maman Mace
3. Fatar Maman Mace ta yi kamar "orange"
4. Fitar jini daga Maman Mace
Yadda ake gane Mace tana da Cancer:
1. Ana amfani da Pap smear da HPV test (cervical cancer) dan duba Cancer Mahaifa
2. Da kuma mammogram/ultrasound/biopsy (breast cancer) dan duba Cancer Maman Mace
In Shaa Allah zamu kawo maganin cutar.