04/01/2024
MANUFOFI DA KUMA KUDURE-KUDUREN KUNGIYAR GUMEL EDUCATION AND SKILLS PROGRESS ASSOCIATION (GESPA)
--------------------------------------------------------------------------------------------
Kungiyar Gumel Education And Skills Progress Association (GESPA,kungiya ce da wasu zakakuran matasa 'yan asalin ƙaramar hukumar Gumel s**a samar,an ƙirƙiri ƙungiyar Gespa a shekara ta 2020,a ƙaramar hukumar Gumel da ke jahar Jigawa,Najeriya.
Ƙungiyar Gespa,ƙungiya ce mai Rijista a matakin ƙaramar hukuma,Gespa ƙungiya ce mai zaman kanta,wadda ba ta jingina ga wani ko wata siyasa ba,amma a shirye take da ta yi tafiya da duk wani wanda zai ba ta gudunmawa kan manufofin ta,walau dan siyasa ko mai riƙe da sarautar Gargajiya,kawo yanzu,Gespa ta gabatar da babbar gasa da aka jima ba a yi irin ta ba,wadda ta saka tsakanin ɗaliban makarantun Firamaren ƙaramar hukumar Gumel.
Bayan jin taƙaitaccen tarihin Gespa,ga kuma kaɗan daga cikin manufofin ta,waɗanda su ne maƙasudin samar da ƙungiyar;
1-Ƙungiyar Gespa,ƙungiya ce da matasan s**a ƙirƙira musamman domin ta taimaki harkar ilimi a ƙaramar hukumar Gumel,musamman ilimin kimiyya da fasaha(Science and Technology).
2-Ƙungiyar Gespa,ƙungiya ce da take wayar da kan mata da matasa kan muhimmancin sana'oin hannu na dogaro da kai, tare da koyar da su abin da ya sauwaƙa gwargwadon ƙarfin ta,domin rage zaman kashe wando a ƙaramar hukumar Gumel.
3-Kungiyar Gespa,kungiya ce da take ware wasu lokuta ta shirya taron ƙara wa juna sani(Seminar)ko wayar da kai,kan harkar Ilimi,musamman ilimin kimiyya da fasaha,a ƙaramar hukumar Gumel.
4-Ƙungiya Gespa,ƙungiya ce da lokaci zuwa lokaci,ta kan shirya ta saka gasa tsakanin makarantun ƙaramar hukumar Gumel,musamman makarantun Firamare,na gaba da Firamare(Junior),da na Sakandire,domin ƙara zaburar da ɗalibai,don ci gaba da samun ingantaccen ilimi a ƙaramar hukumar Gumel.
5-Ƙungiyar Gespa,a shirye take da ta ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe da duk wani mai burin ciyar da harkar ilimi gaba a ƙaramar hukumar Gumel,jahar Jigawa da ma ƙasa baki daya.
A taƙaice,waɗannan su ne kaɗan daga cikin manufofi da kuma ƙudure-ƙuduren Gespa.
Allah ka taimaki wannan ƙungiya,ka ƙara ruƙo da hannayen shuwagabannin ta,ka kuma cika mata burikan ta kan manufofin ta.
--------
Usman Sani Usman
Publicity Secretary,Gespa
07040119941,08114962119.