Karatun alqurran daga bakin alaramma is'maila maiduguri
An-Nuur Masjid Jama'are
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from An-Nuur Masjid Jama'are, Educational Research Center, Unguwar gandu quarters jama'are, Jama'are.
22/04/2025
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN.
Cikin alhini da Damuwa Muke sanar da Rasuwar Mahaifiyar mai hidima cikin Addinin Musulunci MALAM ADAMU BELLO JMA Limamin masallacin juma'ah na ANNUR MASJID .
Za'ayi jana'izar ta da misalin Karfe 9:00 na safiyar yau talata Insha Allah, A kofar gidansa dake ung. Tsamiya tsohowa .
Muna mata Addu'ar neman Rahama da salama daga Allahu Subhanahu wata'ala ya sanya ruhinta cikin dausayin Aljannatul firdaus.
20/01/2025
WA’AZIN JIHA A GARIN AZARE!!!
Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis-Sunnah na Jihar Bauchi Prof. Sheikh Zubairu Abubakar Madaki, da Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Sulaiman Yusuf Bashir, da Daraktan Agaji Alh. Umar Jabir, a madadin kungiyar, na farin cikin gayyatar dukkan Musulmi zuwa wajen Gagarumin Wa’azin Jiha da za’ayi a Kofan Fadar Maimartaba Sarkin Katagum Dr. Umar Faruq ll a Garin Azare ranar LAHADI 26th RAJAB 1446; dai-dai da (26/01/2025) da misalin karfe 4:30pm na yamma In Sha Allah.
Malamai masu wa’azi sun hada da:
- Prof. Zubairu Abubakar Madaki
- Sheikh Sulaiman Yusuf Bashir
- Sheikh Aliyu Muhd Sa’id Gamawa
- Sheikh Muhd Manga Abba Misau
- Ustaz Magaji Bappah Sulaiman Azare
- Sheikh Abdurrahman Ibrahim Idris
- Mal. Ibrahim Haruna Dambam
- Mal. Adamu Abubakar Cheledi
- Sheikh Dr. Muhammad Rabiu Mball
- Sheikh Imam Attahir Muhammad Tilde
- Sheikh Adamu Bello Hanafari Jama'are
- Ustaz Albashir Muhammad Ningi
- Malam Anas Adamu Azare
ALARAMMOMI
- Alaramma Abubakar Usman
- Alaramma Auwal Abubakar (Biyadihi)
- Alaramma Idris Ibrahim Kolo
- Alaramma Ahmed Umar Jama’are
- Alaramma Ziya’ulhaq Iliyasu Bandas
- Alarammma Yusuf Sulaiman Jama’are
- Alaramma Nazir Abdullahi Azare
- Alaramma Salisu Musa Itas
Da sauran malamai da alarammomi.
Allah Ya bada ikon halarta, amin.
Sanarwa Daga: Malam Iliyasu Danjuma Bandas,
Sakataren JIBWIS na jihar Bauchi.
JIBWIS Social Media
Bauchi State Directorate
20th-Rajab-1446AH.
20th-January-2025
16/01/2025
GAYYATAR WALIMAR SAUKAR QUR'ANI A MASALLACIN JUMUA HAUDA JAMAARE
Assalamu alaikum
Hukumar makarantar ATTAHSEEN TAHFIZUL QUR'AN JAMA'ARE Tana farin cikin gayyatar ka/ki/ku/mu zuwa gagarumar walima ta yaye dalibai Guda 12 Wanda Allah ya basu ikon kammala saukar Alqur'ani mai girma wanda PROF. ZUBAIRU MADAKI BAUCHI zai gabatar da nasiha Insha Allah.
Za'a Gabatar ranar lahdi 19/07/1446 Daidai da 19/01/2025
Lokaci :09.00 na safe insha Allah
Allah ya bada ikon zuwa Amiin
In sha Allah Kamar yadda sanarwa ta gabata, sheik Abubakar Usman bolari daga Garin Gombe Zai cigaba da gabatar mana da darusa Kamar haka:
Muhadarar Mata a masallacin Annur, lokaci 10:00- 11:00
Maudu'i:halattacen Kishi da akasin sa
Hudubar Jumma'a a masallacin Hauda.
Nasiha a laburarin Ali bako akan illolin shaye-shaye.
Muhadara tsakanin magariba da isha'i a masallacin Hauda,Maudu'i taimake keniya tsakanin al'umma
Allah ya bada Ikon halarta Ameen
16/12/2024
GAYYATAR WA'AZIN ƘASA DA SEMINAN ‘YAN AGAJI A BAUCHI DAGA RANAR 18-22 GA DISAMBA 2024 A BAUCHI
Shugaban JIBWIS Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau da shugaban majalisar malamai Dokta Ibrahim Jalo Jalingo da daraktan ‘yan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti na farin cikin sanar da bita wato semina ta ‘yan agaji da za a gabatar a makarantar kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali wato Abubakar Tatatari Ali Polytechnic (ATAP) da ke Bauchi daga ranar 18 ga watan nan na Disamba 2024. Taken SEMINA “YAKI DA RASHIN TARBIYYA DA SAMAR DA AIKIN YI GA MATASA”
Za a kuma gudanar da gagarumin wa’azin kasa a ranar Asabar21 ga wata da dare a nan Bauchi inda washegari Lahadi 22 ga wata za a yi taron rufe bitar.
Babban bako na musamman mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR.
Mai masaukin baki mai girma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi.
Shugaban taro mai ba wa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Malam Nuhu Ribadu
Iyayen taro mai martaba sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu da mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje
Manyan baki ministan lafiya Dokta Muhammad Ali Pate
Ministan harkokin waje Malam Yusuf Tuggar
‘Yan majalisar dattawa na Bauchi Sanata Shehu Buba, Sanata Abdul Ningi da Sanata Sama’ila Kaila da dukkan ‘yan majalisar wakilai.
Babban shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPCL Mele Kyari Kolo
Sanata Muhammad Danjuma Goge da
Sanata Abdul’aziz Yari
Malamai da za su gabatar da wa’azi sun hada da:
-Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau
-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
-Sheikh (Dr) Yakubu Musa Hassan Katsina( Sautus-sunnah)
-Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna Gombe
-Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura
-Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia.
-Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Gambo kyari Maiduguri
-Sheikh Aliyu Abdullahi Telex
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos.
-Sheikh Abdulbasir Isah Unguwan Mai kawo
-Sheikh Dr. Isma'ila Kumo
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/Le
10/12/2024
SHIN KATABA BAWA DAN SOCIAL MEDIA GUDUMAWA?
Wayar salula, data, makirufo, tripod, da fitilar LED, wadannan su ne kadan daga cikin kayan aikin da masu kokari a social media ke amfani da su wajen haska muku karatuttukan, malamai, a fadin duniya.
Kayan nan kuwa, idan mutum zai mallake su, sai ya tanadi kudi kusan ₦500,000. A matsayinka na dan uwa musulmi, wace irin gudunmuwa kataba bayarwa ga wani dan social media domin a ci gaba da yada da’awa?
Ka sani, idan ka bada gudunmuwa ga wani dan social media domin tallafa masa, duk wanda ya saurari karatu ya amfana da shi, kai ma zaka samu ladan sadakatul jariya. Wannan ya nuna cewa taimakonka ba zai tsaya ga wannan duniya ba, zai ci gaba har bayan rayuwa
19/10/2024
GAYYATA GAYYATA GAYYATA
04/10/2024
Tuna Baya
Imam Yunusa Abubakar jamaare
04/10/2024
First Aid Group of JIBWIS,
National Directorate,
National Headquarters,
Berger Junction, Utako.
Abuja - Nigeria..
CAMPING/SEMINAR 2024 !!!
Daraktan Agaji na Kasa JIBWIS Nigeria,
ENGR. MUSTAPHA IMAM SITTI
Na sanar da Dukkan 'yan Agaji tarayyar NIGERIA dana Kasashen AFRICA cewa ƙarshen wannan shekarar Akwai Gagarumar Seminar/Camping ta ƙasa da ƙasa, Wanda za'a yi kamar haka :
Ranar shiga Camp : Laraba 18/December/2024 zuwa Lahdi 22/December, 2024 in Shaa Allah.
A Garin BAUCHI headquarter jihar Bauchi Nigeria.
Domin haka, a fara Shiri kafin wannan Rana.
Mun samu wannan saƙo daga mataimakin sakataren shirye-shirye na majalisar agaji ta ƙasa, Shehu Abdurrahman Gashua.
JIBWIS NIGERIA
22/09/2024
Assalamu Alaikum warahmatullah.
Muna sanar da jama'a cewa: in sha Allahu Gobe Litinin Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum zai Gabatar da karatu a Masallacin S.19 Dutsen Tanshi dake nan cikin garin Bauchi.
⭕ Maudu'i: Rafkana Cikin Mulki
Wanda ya gani ya sanar da wanda bai gani ba.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Unguwar Gandu Quarters Jama'are
Jama'are