01/04/2024
HUKUNCIN ƊAGA HANNU A SALLAH:
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Ina tambaya ne shin dole ne ɗaga hannu a sallah, misali kaman wurin yin sujjada da ɗagowa. ko kuwa in anyi kabbaran tada sallah shikenan?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Daga hannu a cikin sallah yayin kabbarar harama hakki ne a kan kowane musulmi yayin da ya zo yin Sallah. Haka ma sunnah ne ɗaga hannu yayin yin ruku'i da sujada.
Ya zo a hadisin Ibn Umar (r.a) cewa, Lallai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance ya na ɗaga hannunsa kusa da kafadunsa yayin da zai buɗe (fara) sallah da lokacin da zai yi kabbara don yin ruku'i da lokacin da ya ɗago daga ruku'i. Bukhary da Muslim.
Tun da kuwa har ya kasance Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam na ɗaga hannu lokacin kabbarar harama, da ruku'i da ɗagowa daga ruku'i wannan ke nuna muma hakki ne a kan mu, mu yi riko da wannan sunnah. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Ku yi sallah kamar yadda kuka ga Ina yin Sallah”
Saboda haka 'yar uwa ana ɗaga hannu a dukkan Waɗannan wuraren uku da muka ambata.
WALLAHU A'ALAM.
✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.
08166650256.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ