21/08/2023
Yakamata mu saba da ambaton ahlin annabi idan muna yimasa salati (allahumma salli ala sayyidina muhammadin wa'ala ahlihi wasalim) 🙏🙏🙏
Bamu yarda wani ya mana post na wani abu da baidaceba
21/08/2023
Yakamata mu saba da ambaton ahlin annabi idan muna yimasa salati (allahumma salli ala sayyidina muhammadin wa'ala ahlihi wasalim) 🙏🙏🙏
19/08/2023
ABUBUWA 5 DA SUKE JANYO BALA'I ACIKIN AL'UMMA
Hadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)
Yace Watarana muna zaune sai ga Manzon Allah (S.A.W) yazo wucewa, Yace " ya ku taron muhajirai! Akwai wasu abubuwa guda 5 idan al'umma s**a Jarabtu dasu!
Ina Roƙon Allah kada ku riske wannan Lokaci.
1⃣ Duk Al'ummar da s**a bayyana Alfasha! Tabbas zasu samu kansu cikin Annoba da yaduwar sabbin cututtukan da ba'a taɓa ganin su ba!
2⃣ Duk Al'ummar da suke tauye modu da sikeli! Tabbas zasu samu kansu cikin yanayi na fari (rashin ruwan sama), Tsadar Rayuwa da cutarwa daga azzaluman Shuwagabanni.
3⃣ Duk Al'ummar da s**a hana zakkar dukiyoyinsu! Tabbas Allah zai hanasu ruwan sama! Idan kaga Ruwa, an yine kawai saboda yara da dabbobi da suke rayuwa a cikinsu.
4⃣ Duk Al'ummar da s**a saɓa alkawarin Allah da Manzon sa! Tabbas Allah zai ƙasƙantar dasu a gaban abokan gabansu.
5⃣ Duk Al'ummar da Shuwagabaninsu basu hukunci da Littafin Allah, kuma suke chanza Abinda Allah ya sauƙar! Tabbas Allah zai sanya gaba, yaƙi da ganin Aibin Junansu a tsakaninsu.
Ibn Majah ne ya Rawaito Wannan Hadisin.
Dan Girman Allah acikin Waɗannan Abubuwa 5 wanne ne ba'a aikatawa a Nigeria? A hakan kuma muke jiran ganin dai dai
Allah kashiryemu ka gyara mana zukatanmu
~ Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Allah yasa mudace amen
Maryama Muhammad Abdullahi 😘
11/06/2023
" Ya Ubangiji Ka Sauƙaƙawa Kowa akan Hanyar Neman Abincin Shi."
Duk sunan da za'a kira ka da shi, kimar sunan bai kai a ce ma MUSULMI ba.
-Sheikh Guruntum
© Ibrahim Usman
Acikin surorin Alqur'ani
114
Rubuta sunan Surah daya
saboda Girman Allah🙏
29/04/2023
Wakee'u bin Jarrah Allah ya masa rahama yake cewa "Zakkar fidda kai ga watan Ramadhan kamar Sujudus sahwi ne ga sallah, tana cikace tawayan Azumi kamar yadda sujudus sahwi take cikace tawayan sallah"
تاريخ بغداد (٥٧٦/١١)
29/04/2023
Muraja'armu ta yau: 06/10/1444 = 26/04/2023
Surah: 2- Baqarah.
Ayah: 135 - 141
Allah ya bada ikon karantawa
Mahaddacin Alqur'ani