Nurul-Islam Secondary School

Nurul-Islam Secondary School

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nurul-Islam Secondary School, School, Lamurde Street, Jalingo.

Photos from Federal Ministry of Communications and Digital Economy, Nigeria's post 04/11/2021
07/10/2021

ANA NADA MATA SU JAGORANCI MATA ‘YAN’UWANSU A SALLA MA BALLANTANA A KARANTARWA:

Dr Ibrahim Jalo Jalingo ✍️

1. Shari’ar Musulunci ba ta hana a nada matasa maza domin su shugabanci matasa ‘yan’uwansu a kan lamarin wa’azi ba, haka nan ba ta hana a nada mata manya ba domin su shugabanci mata ‘yan’uwansu a lamuran wa’azi ba. Babu mai hana wannan da sunan Musulunci sai wanda jakin gidansa ya fi shi fahimta.

2. Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 592 da isnadi sahihi daga Waraqatah Bint Abdillah ((cewa Manzon Allah ya kasance yana ziyartar ta a gidanta, sannan ya nada mata ladani da zai rika kira mata salla, sannan kuma ya umurce ta da ta rika yi wa ahlin gidanta limanci)). Daraqudniy ya ruwaito athari na 1508, da Abdurrazzaq na 5082, da Ibnu Abi Shaibah na 4952 daga Hujairah Bint Husain ta ce: ((Ummu Salamah ta yi mana limanci a sallan la’asar ta tsaya a tsakiyarmu)). Baihaqiy ya ruwaito cikin Ma’arifatus Sunnan athari na 5975 daga Nana A’isha cewa ta jagoranci mata sallan la’asar, ta tsaya a tsakiyarsu)).

3. A Aljanna ma ana jagorantar da wasu mata a kan wasu mata ‘yan’uwansu; Hakim ya ruwaito hadithi na 4853, da Dabraniy na 12179 da isnadi sahihi daga Nana A’isha ta ce: na ji manzon Allah mai tsira da imincin Allah ya ce: ((Shugabannin matan Aljannah hudu ne: Maryam Bint Imran da Fadimah Bint Rasulillah da Khadijah Bint Khuwailid da A’asoyah matar Fir’aun)).

4. Haka nan matasan Aljannah ma suna da shugabanninsu, Tirmiziy ya ruwaito hadithi na 3768, da Nasa’iy na 8113, da Ibnu Majah na 118, da Ahmad na 10999, da Hakim na 4778, da Ibnu Hibban na 6960, da Dabraniy na 2598 da isnadi sahihi cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Hasan da Husain su ne shugabannin matasan Aljannah)).

5. Idan har jagorancin mata ga mata ‘yan’uwansu zai inganta cikin salla, da ma cikin Aljannah, to me zai hana ingancin jagorancinsu ga mata ‘yan’uwansu cikin wa’azi?? Haka nan idan har jagorancin matasa maza ga matasa ‘yan’uwansu zai inganta cikin Aljannah, to me zai hana shi inganta a nan duniya??

6. Muna neman tsarin Ubangijinmu daga sharrin hahilci murakkabi. Ameen.

24/08/2021

This is a person who established Nurul-Islam school Jalingo at the year 1989
In person of Alhaji Adamu Lamido Gora
May Almighty Allah grant him jannatul Firdausi as his final abode
May He forgive his pass and bless his family
And the entire Muslims Umma over the world

24/08/2021

Alhamdulillah Rabbil Alamin
The QEC program has successfully conducted
Alhamdulillah,my dearest School had be came a second position in both spelling and pronunciation (English)
Alhamdulillah Rabbil Izza
Wala haula Wala quwwata illa Billah

09/08/2021

Alhamdulillah for everything,we have done our CIVC in peace and came back to our houses normally. We pray that,may Almighty Allah bless our knowledge and put more experience in our brain

05/08/2021

Alhamdulillah Ala kulli halin
Welcome to Nurul-Islam

Want your school to be the top-listed School/college in Jalingo?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Culinary Team

Attire

Address


Lamurde Street
Jalingo