19/10/2015
MANUFAR KAFA KUNGIYAR # IZALA A NIJERIA DA SAURAN
KASASHE!!!
Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da Sunnah.
Dandalin mu na # Jibwis # Nigeria ya dan waiwaya baya
kadan ya gutsuro muku wasu daga cikin manufofin kafuwar
kungiyar tun asali.
Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a
shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne
Alhaji Musa Maigandu Muhammad, a qarqashin kulawar
Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris
bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na
farko na kungiyar.
Wannan Kungiya ta musulunci ce, wacce musulmi s**a
kafa kuma tana da hedkwata a Jos, Jihar Pilato, Sannan
tana da liaison office a Babban birnin tarayya Abuja, inda
anan ne ofishin Shugaban ta na kasa yake a halin yanzu,
kungiyar bata da alaka ko wace iri ce, da wata kungiyar
asiri, darika ko kuma kungiyar Siyasa.
Wannan kungiya tana kan tafarkin musulunci ne wanda ta
dogara ga Qur’ani da hadisan Annabi Muhammad (SAW)
Bisa fassarar Magabata. Babu bambanci a cikin kungiya in
dai har mutum musulmine da yayi Imani da ‘Allah’ kamar
yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar. Kungiya na
maraba da irin wannan mutum da kuma shawarwarinsa
masu amfani wadanda s**a dace da musulunci.
Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin
musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da
daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da
wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu
ginshiqan # MANUFOFI da take so ta cimma domin kai wa
Ga gaci.
Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada
da:
- Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi
wa al’umma katutu.
- Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da
Sunnar Manzon Allah (SAW),
- Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran
addini, domin a gudu tare a tsira tare.
- Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu
miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.
- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da
sakon Allah (SWT).
- Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya
cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to
wannan zunzurutun makaryaci ne.
- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.
- Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk
wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba
zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da
zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”
- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah
Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).
Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun Hada da:
Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe
daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da
kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa.
Kadan daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:
- Kwamitin Da’awah.
- Kwamitin Ayyuka.
- Kwamitin Kula da Marayu
- Kwamitin Ilimi.
- Kwamitin Sulhu da fatawa da ladabtarwa.
- Kwamitin Taimakon Gaggawa.
-Kwamitin Masallatai.
-Kwamitin MANARA.
-Kwamitin yanar Gizo.
-kwamitin yada labarai
Da Sauran wasu kwamitoci.
Shugaban kungiyar IZALA na kasa a wannan lokaci shi ne
Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a
sashin Shugabancin kungiyar tun bayan kafa ta, wanda
tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne bayan rasuwar
Marigayi Sheikh Imam Ikara, duk a lokacin zamanin
shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad,
kuma ya gaji shugabancin kungiyar ne bayan rasuwar
Shugaba Musa Maigandu Muhammad.
- Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe: Mataimakin
Shugaban Kungiya Na Kasa na daya.
-Sheikh Abbas Muhammad Jega: Mataimakin Shugaban
Kungiya na kasa na biyu.
- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban
Magatakardan kungiyar na kasa.
- Sheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar
Malamai na kasa.
- Sheik Barrister Ibrahim Sabi'u Jibia: Mataimakin Shugaban
Majalisar Malamai na Kasa.
- Engineer Mustapha Imam Sitti: Shugaban Rundunar Yan
Agaji na Kasa
- Alhaji Muhammad Kabir Sa'id Gusau: Mataimakin
Shugaban Rundunar Yan Agaji na kasa a bangaren (Training
and operation)
-Alhaji Abdullahi A. Diggi: Mataimakin Shugaban Rundunar
Yan Agaji na kasa a bangaren (Admin and Finance)
kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya.
A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da
birnin tarayya Abuja. Haka kuma saboda irin yadda
kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa
har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su;
Kasar Saudi Arabia, Amurka, Ingila, Nijer, kotonu, Mali,
Senegal, Togo, Kamaru, Chadi, Burkina faso, Gini, da
sauransu.
Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali
wajen yin su, sun hada da:
- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da
bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.
- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.
- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni Uku ko hudu
don tunatar da mutane abin da s**a manta ko kuma lokutan
da s**a dace.
- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko,
da sauran fannonin ilimi.
- Kai Ziyara Zuwa gidajen marayu, fursina da asibitoci,
domin tallafawa musulmai marasa galihu.
- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar
hakan ta taso.
kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa
wadanda s**a sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki
daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon
tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.
Dan haka nema kungiyar take rubuta "LAA ƊAA'ATA
LIMAKHLUƘIN FII MA'ASIYATIL KHALIƘI." A dukkan
kadarorinta data Mallaka, irin su motoci da sauran su, Tun
farkon kafa kungiyar har zuwa yau dinnan kungiyar bata
chanza ba.
Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo dogo ko
gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da
marigayi Sheikh Isma'ila Idris Ibn Zakariyya (Shugaban
Majalisar Malamai na farko) ya bayar dan kafuwar wannan
kungiya mai albarka ba, da irin Su Marigayi Sheikh
Abubakar Mahmud Gumi, Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa
Maishinkafa, Marigayi Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Marigayi
Sheikh Adam Mai Shafi, Marigayi Sheikh Abubakar Imam
Ikara, Marigayi Sheikh Musa Maigandu Muhammad da
Marigayi Alhaji Ali Ibrahim Tofa (Tsohon Shugaban yan
agaji na kasa), koda Kuwa ba manufarmu mu zayyana
sunan kowa ba.
Suma sauran Matasan Malaman da a baya s**a bada
Gudunmawar su dan kungiyar ta cimma manufofinta,
wanda a yanzu sun zama Dattawa, a farkon tafiya gashin
su baki ne, amma yanzu ya rikide ya zama fari sol, kuma
ba'a daina yin wa'azin ba, irin su Sheikh Dr. Alhassan Sa'id
Adam jos, wanda shine Alaramman kungiyar na farko mai
jan baki a bisa mimbari yayin wa'azi, da Sheikh Yakubu
Musa Hassan Katsina, wanda a farkon tafiya shine
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na biyu, Sheikh
Rabi'u Aliyu Daura, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe,
Sheikh Abbas Muhammad Jega, Alaramma Abubakar Adam
Katsina da da Sheikh Habibu Yahaya Kaura wanda ake
masa lakabi da dan autan masu wa'azi, sabo da kankantar
sa, gashi yanzu shekaru sun cimmasa, da sauran wadanda
suke raye ake fafatawa da su a halin yanzu.
Daga karshe Muna addu'a ga dukkan wadanda s**a
sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan
harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan
Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira. Amin.