Qur'an & Hadis

Qur'an & Hadis FEAR ALLAH WHERE EVER YOU ARE

09/05/2021

Dr jabir sani maihula Sokoto yayi wannan bidiyo domin nunawa da karantarwa da nasiha ga yan uwa musulmi akan zakkatul fitr ma’ana zakka fidda kai. Malam yayi bayyanin abinda yasa ake yin wannan zakka fiddakai ga mabukata. Wannan shine bidiyon da malam yayi ya nuna mana yadda za’a fida kai na mud...

08/05/2021
22/03/2021

Yadda za kuci Nasarar Korar Tsaka Daga Gidan ku

Kasamo tafarnuwa da gishiri saika shafe tafarnuwar da gishiri sai ka jejjefa ta akowanne bangare na gidan.
Da yardar Allah bazata sake dawowa ba.
Ina rokon duk wanda ya karanta don Allah yayi sharing saboda wasu su amfana.

21/03/2021

Wanda yaje cewa yana goge baki sau 5 sau 10 bakin baya dena wari,idan yayi magana tana fita da wari ga magani fisabilillahDomin shiga group 👉👉👉👉 https://...

17/03/2021

Sallar Nafila Lokacin Da Liman Ya Hau Minbari Ranar Jumu'ah. ~ Sheikh Jabir Sani Maihula

1) Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu'ah liman yana akan minbari, zaiyi sallah raka'ah biyu, amma ya gajarta. (Bukhari da Muslim)

2) Idan mutum ya taradda ana kiran sallah kafin a fara khutbah, zaiyi sallah lokacin da ake kira bazai jira a gama kiran sallah ba, saboda sauraron khutbah wajibi ne amma sauraron maikiran sallah Sunna ne. ( Ibn Uthaimeen)

3) Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, bazaiyi sallah ba lokacin da liman ke khutbah, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci.

4) Mutane da yawa sukanyi kuskure sai su zata akwai wasu raka'ah biyu da akeyi kafin Jumu'ah, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana khutbah. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana khutbah.

5) Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka'ah biyu kafin ya zauna. Wannan hukuncin da ranar Jumu'ah da Assabar da sau ran ranaku duka daya ne. Dalili akan hakan shine, cewar da Manzon Allah S.A.W. yayi: Idan dayanku ya shiga masallaci kada ya zauna sai yayi sallah raka'a biyu. ( Bukhari da Muslim)

Ya kamata ayi fadakarwa da mutane akan wannan hukuncin, saboda da yawa akan saba.

Address

Hadejia

Telephone

+2348030630683

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qur'an & Hadis posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share