23/04/2023
Marital Education Program (MEP)
Cikin shekaru biyu makarantarmu ta Samaaha Institute of Training and Research tayi kokari wajen ganin ta bada gudunmawar ta wajen inganta zamantakewar iyali ta hanyar magance matsalolin aure. Bayan dogon nazari da kuma bincike Samaaha ta tabbatar da cewa matsalolin aure sun kasu kashi uku; matsalolin dake da tushe kafin aure, da matsalolin da ke faruwa bayan anyi aure da kuma matsalolin da makusanta da Yan uwa ke haifarwa ma'auratan. Dukkan wadannan matsalolin su na da rassa.
Kusan biyu cikin ukun nan kai tsaye ka iya cewa in har matsalar bata yi nisa ba takan iya gyaruwa a kuma ji dadin zamantakewa. Matsalolin ta bangarori biyu ne; bangaren iyaye mata da kuma bangaren iyaye maza. Bangaren mata na da karancin wuyar tuntuba da kuma halastar bita don magance matsalolin, wanda ta bangare daya kuma bangaren iyaye maza keda matukar wahalar tuntuba da kuma taruwa don sauraron bitar duba da uzururrukan neman abinci da kuma sabgogin rayuwa.
Dubawa da wannan kai tsaye bayan tuntubar masana da kuma shawarta magabata Samaaha ta shiga fara bada bita ta musamman ga iyaye mata, wanda cikin Ikon Allah da amincewarsa amsamu nasara a duk zanguna biyu da akayi na bitar kuma anci nasara ta hanyar magance sababin wasu matsalolin.
Yanzu bangaren iyaye maza muke so mu komo garesu don tattaunawa da kuma bada shawarwari da bita ta musamman. Bayan nazarin duk hanyoyin da ya kamata ace an tara ma'aurata maza don yin wannan bita taci tura, muna ganin zamuyi amfani da dandalin fasahar sadarwa don gudanar da bitar ga ma'aurata maza dama masu shirin yin auren, domin shiga tsarin latsa wannan link dake kasa
https://chat.whatsapp.com/EZQSmzKe6ZXDleLPMaOoT8
Fatanmu Allah ya taimakemu wajen rage da magance matsalolin da s**a addabi zamantakewar aure, wanda a lokuta da dama s**an kai ga rugujewarsa da lalacewarsa, Allah ya mana jagora.
TAMBIHI: Ta wace hanya kake ganin za'a iya magance matsalolin aure, sannan wasu hanyoyi kake ganin za'a iya bi don inganta da kuma kaucema fadawa cikin matsalolin?
WhatsApp Group Invite