Madarasatul shamsuddini imamu malik islamiyya gandun sarki

Madarasatul shamsuddini imamu malik islamiyya gandun sarki imamu malik darul qur,an wa hubbi rasurullahi S,A,W

30/11/2025

Malikiyya amana

29/08/2022

Goodday

03/02/2022

16/01/2022

YA ZARA,U FADIMA NANA...... LALE MARHABA DA ZUWANKI
Ya hayyul kudusu buwayi Allah zanasa mahalicci
Sarkin duniya da k'iyama shi yai 'Dan Adam mabuk'aci
Yauma na rik'o k'ok'ona Allah rabbana mawadaci
Lamincan ka k'ara basira zanyi yabona 'yaga ma,aiki

Rabbi kayo dad'i na salati gun abdullah 'Dan abdullah
Wadda kake tayi ba fashi gun manzo muradin kalla
Sa ahalinsa masu muhibba suda sahabihi ya Allah
Har shurafa,u suma sanya jikokin rasulu ma,aiki

Sheik tijjani na sanyashi sarkin auliya takensa
Sheik jilani al,bagadadi ,inyass ma yana aikinsa
Al,kanawi ina gaidashi maulana Sharu d'an musa
Sheik muktari jafar baba mai k'aunar rasulu ma,aiki

Azzahra salamu alaiki ya ummu sharifai Nana
Lale marhaba mad'ahura ya jika ga Nana amina
Lale marhaba ya zahra bintu rasulu ga baitina
Lale Nana fadima Zahra oyoyo batul labbaiki

Oyoyo muna furtawa murnar samuwar 'yar baba
Maulidi Nana batula sai murna bama dainaba
Shamsuddini imam malik ne yauma gamunan da marhaba
'Yan shidima ga Nana batula ne Zahra,u 'yaga ma,aiki

Sai murna da samun Nana bintu rasuluce azzahra
Ya tsoka jini ta ma,aiki mai k'aunartane yai zarra
Ya siddikiya mad'ahura ummu abiha fadima Zahra
Lale marhaba da zuwanki sirrin shugabanmu ma,aiki

Ya Zahra,u hasken dake haske jasadi da Rubin bayi
Mun d'au San zakiyya waliyya na rantse dayazarce yayi
Sune ta k'amar duk halitta Wanda yabarsu yasau layi
Nina sallamawa azima mai kyawu da halin kirki

Sayyadatun nisa,u batula 'ya gun sayyadatu khadija
Mai k'aunarki Nana batula ya dace yana fa da hujja
Wanda ya k'ita Nana batula baida abin fadi ba hujja
Ya sirrin ma,aikin allah fadima sayyada labbaiki

Tarbiyyar gidan annabta fadima babu mai kusheki
Duk mai san rasulullahi dole ya*oki har yai d'oki
Nana batula na shimmantu sai k'auna da yin baitinki
Ya assayyada mabaruka babu k**arki babu kalarki

Ya Zahra,u sirrin koyi mai halin da ayi rik'ewa
Abida ce tayo haskawa mai k'aunarta yai dacewa
Mai hak'urin zama da mijice bata fad'a bare arabawa
Fad'ima Zahra jagorace mai ha

09/11/2021

MALIKIYYA

29/10/2021

10 days more for maulidin nabi @ imamu malik islamiyya

08/10/2021

Happy maulud imamu malik

23/08/2021

AL-ISLAMIYYA IMAMU MALIK
TARBIYYA ,MU AN RENEMU DASAN
MUHAMMADU MANZANMU
Allah ya allah ubangiji
mahaliccinmu
Shi zansa fari abin nufa da
buqatunmu
Lamince allah ubangiji
mahaliccinmu
Zan yabi "yan hidima da nuna
qaunar manzanmu
Qara salatinka abun qira sarki allah
Gun za'binaka muhammadu bin
abdullah
Sa ahalinasa abun riqo manzan
allah
Harda sahabbaima kwarai suna san
manzanmu
Na gaida shehunnai garemu sun
zamto tsani
Su shehu tijjani da baye gausis
zamani
Shehu sharu musa harazimi me
tsantseni
Sheik muktar jafar imamu malik
babanmu
San manzan allah imamu maliku
ansanmu
Munyi biya kulli asan ma,aiki
gatanmu
Ku duba manyanmu ku sake duban
yaranmu
Za kuga alqibilar a*o muhammadu
manzamu
Mu "yan soyayya muke wajen
mazan allah
An kuma renemu da so da bin
mazan allah
Komai zai sauqi idan da san
manzan allah
Allah mun gode dademu qaunar
manzanmu
Wannan tarbiyyar ku gane dai
shamsuddini
Tayi fice malam a kar-kara harma
birni
Wajen ganin an ya'da so da qaunar
al'maddani
Imamu malik mun ado da qaunar
manzanmu
Al-islamiyyar muna karatun qur,ani
Harda hadisaima sabo da gyaran
addini
Da ilimi shinefa za a gane addini
Naji hadisin ya rasulu kan neman
ilmu
Mun san tarbiyya tana a sahen
addini
Addinin islam rasulu shine yai nuni
Hujja babba sai muyo karatun
addini
Mu kwa rasurullahi shi yazamto
za'binmu
soyyayar manzo mukai riko bama
raki
can wasu na haufi abun yana ban
mamaki
Qin me san manzo kasan kana
mugun aiki
Allah ya allah ka tsarkake mana
qalbinmu
Al,islamiyya imamu malik mun
samu
Qaunar manzanmu tayo gida a
zukatanmu
Tanashe komai taqara haskaka
qalbinmu
Babban burinmu a yad'a qaunar
manzanmu
"Yan shamsuddini imamu mun
gode allah
Shi ya haliccemu yabamu san
manzan allah
Allah kare "yan imamu malik du
jimla
A Qara soyayyar rasuluna me
cetanmu
Alhamdullah rabbana gwani masha
allah
Dukkan yabo da godiya gareka
muke allah
Ya me bayarwa abin qira sarki allah
"Mun gode allah abun bid'a de mun
samu
4 minutes ago · Sent from Mobile
Isah Yahaya Hadejia
{ RABIYUL AUWAL YA DAWO-
RABIYUL AUWAL YA DAWO WATA
ME TARIN AL-BARKA WATAN
MAULIDIN MANZONA }
Da sunan Allah jabbaru
Mahaliccin alam Qahharu
lamincemin zanyo shi,iru
WaQar maulidi zan rera muyo
murna da ma,aikina
Ya rabbi salati Qaqqara
Gurin mahamudu abah Zara
Alai Asahabu a jajjera
Suma Shurafa'u asanyasu jikokin
Annabina manzona
Su sheik ahmad Attijjani
Jilani da Gausis zamani
Har shehu sharu zanyo nuni
Maulana shehu sharu Musa jinin
ZAHARA "yar manzona
Ya shehu ma*oyin me makka
Qaunar manzo ita yaddauka
SHehina nina gaisheka
Shehina sheik Muktar Jafar Allah ya
tsare dan manzona
Assalamu alaika Rasurullah
Assalamu alaika Nabiyullah
Assalamu alaika Aminullah
Lale lale Nurullahi haske daga rabbi
maqagina
Watan maulidi ya k**a
Ma*oya annabi mi shimma
A qaunar annabi mi azama
Miyo hidima domin murnar-murnar
maulidin manzona
Abun koyin dai manzone
ZA'BI daga Rabbi maqagi ne
Mai kyan asali a halittu ne
Yazo a rabiyul Awwalne ran
shabiyu SIRA tainuna
Shekarar kuma anyi Qira nata
Amul FIL nema takenta
Lamari ya faru gabaninta
Wani sarkine yazzo MAKKA akayo
bashi dan manzona
Zababbe me birnin makka
Nurullah me shafe shirka
Rahamar bayi babbar taska
Qauna ta Rasurullah NURA itace
mafita Ya dangina
Ya al,maddani manzan "yanci
Ahmad mai rushe zalunci
Mai kyauta me yaye kunci
Ya Al,muktari abun koyi me tsarkin
Qalbi manzona
Rabo me girma munsamu
Muna soyayyar manzanmu
Za'ba'b'ben Rabbi maqaginmu
Dukkan al-kairi ma samu muyo
soyayyar manzona
Shamsuddini islamiya
San annabi Qara dubun niyya
Lamari na ma,aki ba bu'ya
Shamsuddini-shamsuddini an
sanmu da Qaunar manzona
Murna yau ranar maulidi
Mufito tamkar ranar idi
Ranarnan ranar maulidi
Tsafta da ado mufito layi munata
yabo gun manzona
Qiran dana kewa al,umma
San annabi ai shine girma
Mubi koyarwa tai al,umma
Musamu rabo gun Allahu mutashi a
tutar manzona
Ga "yan hidima nan zan gaida
"Yan kaunar annabi mun sheda
Malam umar haka zan gaida
SAYYADI BABA barka-barka me
begen daha ma*oyina
Malam Babangida sannunka
Malam Sale na gaisheka
Har malam Baffa na sanyaka
Malam Aminu imam malik
shamsuddini san manzona
Har malam ALI na sanyama
Hassan malori akwai HIMMA
Shu'aibu da ISAH LALE ma
Har dukkan "yan shamsuddini ban
ware ma*oya manzona
Tammat Sarki mulki Allah
kaine kanufa na biya jimla
Alhamdullah sarki Allah
Isah yahaya nan zan huta kumin
afuwa dan manzona

19/08/2021

''YA MAHAMUDU ABIN YABONA SANKA NAKE , YA ANNABINA ''.(S.A.W).

07/07/2021

SAYYADA FADIMA "YAR ANNABI KENA KEWA YABO ME GIRMA
Assalamun alaiki batula nana "yar mujtaba
Assalamun alaiki abar qaunar nabi shugaba
Assalamun alaiki abar faharinmu har ran gaba
Assalamun alaiki azima sayyada fadima ma,asuma

Abidatun nabi siddiqa fadima shugaba
Sanki ma wajibi koda ansofa al,mujtaba
Wanda duk baya san zara bayaga al,mujtaba
Ya cikar san ma,aiki na gaisheki al,alima me girma

Rayuwata kwarai fansa a gareki "yar shayabo
Ku ku kabbawa bawa dukka halitta nana nayo yabo
Gani nazo amin dan al,hasanaini inyo yabo
Ya uwar shurafa "yar annabi kena kewa yabo me girma

Sayyada d'ahira me kyan asali diyar musdafa
NANA girmanata 'ya 'yanatane fama shurafa
Nana me kyan hali bata kyara barema kwafa
Jinjina sayyada nidai agareki na sallama miki nima

Rayuwa tayi kyawu indai harda ke sayyada
Nai riqo nida sayyayyar zahara,u ba gargada
Rayuwa tayi kyawu ba tsalle k**ar d'an gada
Hibbaki hibbaki 'yar annabi sayyada fadima me girma

Nana kairul nisa,il alam shugabar jannatu
Ya madafa matsera jikar nana aminatu
Dukka mata suyo koyi naki harsuyo himmatu
Zara haske take datake yaye dukan matsala me girma

Sayyada fadima 'yar annabi banji tamkar kiba
Kena kewa yabo naji annabi zara ke yayyaba
Ke yake cewa ummu abiha ya uwa d'ayyaba
Zauji alhaidara bege naki zanayo me cikar alfarma

Ya karima d'iya ga karimi sayyada me isa
In anama batun matsayi nata sai muyo qarqasa
Ba,a zancan isa agaresu ake bid'arma isa
Sannu ya sayyada matsayi tamkarki bama k**a fadima

Hamdulillahi ya sarki rahama gwani rahimi
Kaina sanya cikin lamurana banayin gangami
Kaika yarje nayo begen zara'u "yar hashimi
Isah me malikiyyane na shigo yaban sayyada fadima me girma

18/05/2021

RABIYUL AUWAL YA DAWO 'RABIYUL YA
DAWO WATA ME TARIN AL-BARKA WATAN MAULIDIN MANZONA

Da sunan Allah jabbaru
Mahaliccin alam Qahharu
Allah kanufeni nayo shi,iru
WaQar maulidi zan rera zuwan mahamudu ma,aikina

Ya rabbi salati Qaqqara
Gurin mahamudu abah Zara
Alai Asahabu a jajjera
Suma Shurafa'u asanyasu jikokin Annabina manzona

Su sheik ahmad Attijjani
Jilani da Gausis zamani
Har shehu sharu zanyo nuni
Maulana shehu sharu Musa tsatsan Zahara "yar manzano

Ya shehu ma*oyin me makka
Qaunar manzo ita yaddauka
Babana nina gaisheka
Shehina sheik muktar Jafar Allah ya tsare dan manzona

Assalamu alaika Rasurullah
Assalamu alaika Nabiyullah
Assalamu alaika Aminullah
Lale lale Nurullahi haske daga rabbi maqagina

Watan maulidi ya k**a
Ma*oya annabi mi shimma
A qaunar annabi mi azama
Miyo hidima ya al,umma da samun DAHA ma,aikina

Ai annabi sirrin qauna ne
Haske daga Rabbi maqagi ne
Mai kyan asali a halittu ne
Yazo a rabiyul awalne ran shabiyu SIRA tainuna

Shekarar kuma anyi qira nata
Amul FIL nema takenta
Lamari ya faru gabaninta
Wani sarkine yazzo MAKKA akayo bashi dan manzona

Zababbe me birnin makka
Nurullah me shafe shirka
Rahamar bayi babbar taska
Qauna ta Rasulullah d'a,a na k**a ta nashe raina

Rabo me girma munsamu
Muna soyayyar manzanmu
Zababben Rabbi maqaginmu
Dukkan al-kairi masamu muyo soyayyar manzona

Shamsuddini islamiya
San annabi qara dubun niyya
Lamari na ma,aki ba bu'ya
Shamsuddini shamsuddini asanku da Qaunar manzona

Murna yau ranar maulidi
Mufito tamkar ranar idi
Ranarnan ranar maulidi
Tsafta da ado mufito layi munata yabo gun manzona

Qiran dana kewa al,umma
San annabi ai shine girma
mubi duk tsari nai al,umma
Musamu rabo gun Allahu mutashi a tutar manzona

Ga "yan hidima nan zan gaida
"yan kaunar annabi mun sheda
Malam umar haka zan gaida
SAYYADI baba barka-barka me begen daha ma*oyina

Malam Babangida sannunka
Malam Sale na gaisheka
Har malam Baffa na sanyaka
Malam Aminu imam malik shamsuddini san manzona

Address

LAYIN 'DAN GASHUA, GANDUN SARKI HADEJIA
Hadejia

Telephone

+2348139470065

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madarasatul shamsuddini imamu malik islamiyya gandun sarki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Madarasatul shamsuddini imamu malik islamiyya gandun sarki:

Shortcuts

Share

Category