Government Jiniuor Scondry School Koya Gwarzo

Government Jiniuor Scondry School Koya Gwarzo Allahu ladifu yahayyu ka taimaki wannan makaranta.

Mun yabawa da ƙoƙarin sakataren kula da makarantun secondry na jihar Kano Ksssmb Hon Rabi'u Sale Gwarzo.Allah ya cigaba ...
18/10/2025

Mun yabawa da ƙoƙarin sakataren kula da makarantun secondry na jihar Kano Ksssmb Hon Rabi'u Sale Gwarzo.
Allah ya cigaba da dafamaka.

31/10/2019

KISSA!!!

A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku s**a zo masa suna rike da wani saurayi s**a ce:
Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.

Umar: kai donme ka kashe musu uba?

Saurayi: Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifinsu, sai mahaifinsu ya bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na dauki dutsin na buge shi
ya mutu.

Umar: saboda haka zan tsaida haddi akanka.

Saurayi: ka saurara mini kwana uku, mahaifina ya mutu ya barni da kanwata da
kuma dukiya, idan ka kasheni dukiyar da yar uwata zasu tozarta.

Umar: wa zai lamunceka?

Saurayi ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".

Umar: ka lamunce masa Ya Aba Dharr?

Abu Dharri: na'am

Umar: ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.

Abu Dharr: na yarda.

Saurayi ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na so uku, saurayi bai zo ba,

Hankalin kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.

Kafin sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.

Saurayi: na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi
akaina.

Cikin mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai bayan ka sami dama da za ka
iya gudu abinka?

Saurayi: na ji tsoro, Kar a ce cika alkawari ya Kare
cikin mutane.

Umar ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce
masa?

Abu Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin
mutane.

Wannan jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, s**a ce sun yafewa
saurayi.

Umar: don me?

S**a ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.

Ni ma na isar muku da wannan labari ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwaga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Don Allah kai ma ka tura kar ace yada alheri ya qare cikin mutane.

MAI KAUNARMU ANNABINMU S.A.W
27/10/2019

MAI KAUNARMU ANNABINMU S.A.W

ANNABI MUHAMMAD {S..A..W} Yace Nan Gaba Akwai Al Ummar Da Xataxo Sunfiku Kaunata Sai Sayidina Aliyu yace

"Ya manzon Allah mune ko"? sai yace "aiku jini nane". Sai S**ace "Ya rasulullah to su waye"? sai manzon Allah (S.A.W) yace "sune wad'anda basu ganni ba, amma sunyi imani dani".Manzon Allah (S.A.W) Yace ;

"idan rayuwarku takai kuce Masu Ina Gaidasu".ALLAHU AKBAR!! Ina Haida Wad'annan Mutane!!!Ya Allah duk Wanda Ya Tura Wannan Magana Ta Manzonka, Kayi Masa Sakamako Da Aljanna Madaukakiya
*
Don soyayyarka ga ANNABI sallallahu alaihi wassalam kayi share wasu ma s**aru

Address

Gwarzo

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Government Jiniuor Scondry School Koya Gwarzo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Government Jiniuor Scondry School Koya Gwarzo:

Shortcuts

Share

Category