Jibwis Guyuk Adamawa

Jibwis Guyuk Adamawa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jibwis Guyuk Adamawa, Tutor/Teacher, Guyuk, Guyuk.

12/01/2025
WA’AZIN KASA/SEMINA/DA’AWA A GARIN BAUCHI Shugaban ƙungiyar JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, Shugaban majalisar Mal...
25/02/2024

WA’AZIN KASA/SEMINA/DA’AWA A GARIN BAUCHI

Shugaban ƙungiyar JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, Shugaban majalisar Malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo da Daraktan majalisar agaji, Injiniya Mustapha Imam Sitti, a madadin Kungiyar, na farin cikin gayyatar Al'ummar musulmi zuwa Gagarumin Wa'azin kasa da Za'ayi a ranar Asabar 2/03/2024. A garin Bauchi dake Arewa maso gabashin Naijeriya.

Haka zalika Ranar laraba 28 ga watan nan na Febreru wadanda zasu wakilci jihohi zasu shigo garin Bauchi domin halartan bita ta kasa. Wannan ya shafi iya masu semina ne kadai da a ka turo sunayensu daga jahohi.

Ranar alhamis 29 ga wata masu da'awa zasu fuskanci dukkan masallatan dake kananan hukumomi 21 na jahar bauchi domin isar da sakon Allah har zuwa Ranar Asabar 2 ga watan Maris bayan sunyi wa'azin mata sannan da yamma su iso garin bauchi don wa'azin kasa da dare.

MANUFOFIN DA'AWAR SUNE:

1) Jaddada karantar da Al’uma Taqawa
2) Koyar da Dabaru na addini wajen fita daga halin kaka-nika-yi
3) Bunkasa harkar ilimi da kawar da gurbataccen tunani a tsakanin masu da’awa da daliban ilimi
4) Isar da muhimman sakwanni ga jagorori

Daga cikin Ayyukan da za'a gabatar akwai:

1. Pre- Khuduba (Wa’azi kafin zuwan Limaman Juma’a)
2. Khudubobin Jumm'a
3. Wa'azozi
4. Muhadarar Iyaye Mata
5. Lakcoci da sauran su.

Malamai masu wa’azi

✓Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau
✓Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
✓Sheikh (Dr) Yakubu Musa Hassan Katsina( Sautus-sunnah)
✓Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe
✓Sheikh Abbas Muhammad Jega
✓Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna Gombe
✓Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura
✓Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia.
✓Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan
✓Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa
✓Sheikh Gambo kyari Maiduguri
✓Sheikh Khalid Usman Khalid Jos.
✓Sheikh Abdulbasir Isah Unguwan Mai kawo
✓Sheikh Dr. Isma'ila Kumo
✓Sheikh Dr, Zubairu Abubakar Madaki
✓Sheikh Jamilu Albani Samaru Zariya
✓Sheikh Abdullahi Telex Zariya
✓Sheikh Aliyu Adarawa kwantagora
✓Sheikh Dr. Ibrahim Abdullah

Address

Guyuk
Guyuk

Telephone

+2348163768720

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Guyuk Adamawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category