10/01/2024
SANARWA GA ƊALIBAN ƘARAMAR HUKUMAR GUMEL MASU SHIRIN ZANA JARABAWAR SHARE FAGEN SHIGA JAMI'A (JAMB) ta 2024.
Muna sanar da dukkanin ɗaliban ƙaramar hukumar Gumel masu shirin zana JAMB ta wannan shekarar cewa:
Gwamnatin Jihar Jigawa a ƙarƙashin ofishin Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin da s**a shafi ɗalibai Amb Muhammad Salisu Seeker ta kammala shirin ba ɗalibai ƴan asalin Jihar Jigawa kyautar PIN na JAMB tare da basu horo na tsawon watanni biyu kan yadda za su tunkari Jarrabawar don ganin sun samu sakamako mai kyau. Waɗanda za su ci gajiyar shirin sun haɗar da; ɗaliban da suke shekarar ƙarshe (awaiting result) da kuma waɗanda suke da sakamakonsu na SSCE a hannu.
Don haka muke sanar da duk wani ɗalibin da ke da niyyar zana Jarrabawar ta JAMB cewa za'a gudanar da Jarrabawar gwaji (TEST) ranar 14/01/2024 misalin ƙarfe 10 na safe a Jigawa State College of Education (J.S.C.O.E) Gumel, a Lecture Theatre Six (LT-6).
Ana buƙatar duk ɗalibin da yake da shirin zana wannan Jarrabawa da ya kawo bayanansa kamar haka:
1.Sunan ɗalibi.
2.Lambar waya
3.Katin ɗan ƙasa
4.Takardar shaidar ɗan asalin ƙaramar hukuma (Indigene).
5.Sakamakon shaida gama makaranta (SSCE).
•Duk ɗalibin da ya ci kashi hamsin cikin ɗari (50%) na Jarrabawar, za'a bashi JAMB PIN kyauta.
•Daliban da s**a samu nasara da ma waɗanda ba su samu nasara ba, za'a basu horo a kan dabarun amsa Jarrabawar kamar yadda za'a baiwa waɗanda s**a samu nasara har na tsawon watanni biyu.
Domin bayar da bayanan ɗalibai, za'a iya tuntuɓar ɗaya daga cikin waɗannan mutane:
1.Usmania Cafe, No.2 Sule Lamiɗo Plaza, Lautai Road, 08166125461.
2.Ibrahim M. Ibrahim, Zaburan Quarters, 07041024405.
3.Aliyu B.Maina, Round-about, B/Kasuwa 09037400265.