15/08/2023
A wani zamani daya shude, anyi wani bawan Allah 👳 a wani gari mai tsantsan
tauhidi💥. Wanda tsabar tauhidin shima bai aminta da akwai wani sarki ba inba Allah
ba. A hakan kullum idan yazo fadar 🏡 sarkin garin zaiyi gaisuwa tashi yakeyi yace:
"Ranka shi dade, babu sarki sai Allah 🙏". Ashe hakan dayakeyi, da yalla6oi da fadawanshi 👪 duk sunajin haushin hakan, don meye a tasu wautar bayan ga sarkin
garin zai dinga cewa babu sarki sai Allah?😟
Rannan kawai sai fadawan da yalla6oi s**a shiryawa wannan bawan Allah mai tauhidin makirci. Yalla6oi yasa aka dauko wasu zobunan azurfa 🔅 a kawo fada.
Bayan wannan bawan Allah yazo yayi gaisuwa yafadi abinda yasaba na babu Sarki sai Allah🙇, sai yalla6oi yace: "ga wasu zobuna inaso nabaka ajiya domin inaga k**ar nafi
aminta dakai fiyeda kowa a wannan fadar tawa".
Wannan bawan Allah ya kar6i zobunan⭕, yaje yasamu wani kaho❗ ya dinkeshi da fata yanufi gidanshi yaje ya damkawa matarshi yace ta ajiyemar. Ashe sarkin ya
shirya masa makirci sosai, kawai sai ya aikeshi wani gari mai nisa. Tafiyarshi keda
wuya sai fadawa 👪 s**azo gidanshi s**a samu matarsa s**a loda mata kudade 💴💵💶 da zannuwa s**ace mata: "ina abinda mijinki ya baki ajiya?". Dafari ta nuna k**ar bazata basuba, sai s**a kara loda mata kudi 💷💵 kawai saita dauko ta basu tsabagen butulci da son duniya. S**a k**a hanya s**a tafi s**a kaiwa yalla6ai, ya kar6i abun ya bude yaga tabbas zobunan sunanan aciki k**ar yadda yabashi ajiya.
Sai yalla6ai yasa akaje aka jefa kahon da zobunan a cikin babban kogin garin💭💦💦. Daman a al'adar garin akanyi fishing festival lokaci bayan lokaci, sai kuwa lokacin fishing festival 🐠🐋 din ya zagayo kuma a wannan kogi da aka jefa kahon za'ayi kamun kifi. Wannan bawan Allah 👳 yana can wajen aiken yalla6ai. Kowa yana kamun kifi🐬🐠 aciki harda dan wannan
bawan Allah🚶, Allah Ya bashi sa'a yak**a wani katoton kifi.🐋 Yana isowa gida da kifin saiga Babanshi yadawo daga garinda yalla6ai ya aikeshi bayan yaje fada ya isar da sakon yadawo gida, sai yaron
ya tari baban yamar sannu da dawowa sannan yakoma yaci
gaba da yanka wannan kifi daya kamo🐋, Yana can yana yankawa sai yaji yayi karo da wani abu mai tauri acikin kifin. Babanshi yana zaune yana cin abinci🍛 sai yaron yace: "Baba naji kifinnan yayi tauri nakasa yankawa". Sai Baban yataso ya karbi wukar🔪 yana dirzawa sai yaji taurin shima, daya duba da kyau saiyaji k**ar kaho🐚, yana cirowa sai yaga ashe abunda yabawa matarshi ajiyane kifin ya hadiye, sai Bawan Allahn yace: "tabbass babu sarki sai Allah🙏". Ya ciro abun sai yacewa matarshi: "ina abinda nabaki ajiya?" Saita fara yimasa kame-kame, ya zauna yaci gaba da cin abincinshi.🍜
Yana cikin cin abinci saiga dan aike daga fada yayi sallama akan idan wannan bawan Allahn yagama cin abinci yazo sarki yana kiranshi.😫
Ya kammala cin abinci sai ya nufi fada, bayan ya shiga k**ar kullum sai yace:
"ranka shi dade, babu sarki sai Allah🙇". Sarki da fadawa s**ayi zuru sunason su kunyata wannan Bawan Allahn. Sai Sarki yace: "ina ajiyan dana baka? Fadawa sunata muzurai😳 suna eh idan bai kawoba mu fillemar kai yanxu. Take wannan Bawan Allahn ya saka hannun 👌 a aljihunshi ya ciro kahon ya damkawa yalla6oi. Sarkin yaduba yaga tabbas ga zobunan aciki. Mamaki yak**a sarki, 😲sai mutumin yakara cewa: "babu sarki sai Allah🙏". Sai sarki da kanshi shima yace: "tabbas babu sarki sai Allah👏". Nan take duk fada ta rude da babu sarki sai Allah😀😀. Daganan tauhidi yasamu zama a wannan fadar. Sai Sarkin garin ya mallakawa wannan bawan Allah rabin gari.🏠
Nima nace "Tabbas babu sarki sai Allah😀😀