Imam Abubakar Malami

Imam Abubakar Malami

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Imam Abubakar Malami, Education Website, Gombe.

20/12/2024

Daily Qur'anic Recitation:

By Abubakar Malami (Imam):

Suratul Isra'i 001 (V1-8):

Episode 001:

18/6/1445 AH:

20/12/2024 CE.

09/07/2024

GWAMNA

Yan majalisu na tarayya za su iya neman kujerar gwamna su yi nasara idan s**a assasa siyasarsu a kan kyakkwan gwadabe. Aminu Waziri Tambuwul na Sakkwato da Aminu Bello Masari na Katsina da Umaru Bago na jihar Niger sun tsallaka zuwa ga kujerar gwamna ce daga majalisar wakilai. Ga fili ga mai doki ga duk Dan majalisar tarayya da ke ganin karansa ta kai tsaiko da zai iya goga 'kunji na zama gwamna.

Yan majalisu irin su Usman Bello Kumo na Akko da Ali Isa Jesi na Billiri/Balanga za su iya fara gwada sa'arsu. Amma Irin na Dukku/Nafada da Kaltungo/Shongom maganar gina tubalin siyasa ce farko. Ya yin da na Gombe/Kwami/Funakaye kuma maganar fara turanci a zauren majalisa ce mizanin farko. Irin na Yamaltu kuma hangen Dala a ka masa, b***e a fara masa zancen zama gwamna.

~ Abubakar Malami

10/06/2024

YAN CRYPTO

Kalaman Naziru Sarkin Waka sun tada hazo na "iya yawan mayinin din ka iya yawan talaucinka" inda yan crypto masu amfani da dondola wayar salula dare da rana s**a fusata. Idan masu sana'ar mayinin su na ganin riba mai na fushi? Da alama Alhaji Naziru bai san muhimmancin yin mayinin a wannan zamanin ba, ko kuma bakin ciki ya ke mana inji masu son na ɓagas. 😜 Bayan ka gama mayinin din ragonka da sauran cimakan Sallah da sulallan barka da sallah mai ya rage? Tun da an ruwaito kafun sallah za ta fashe inji Mr Crypto. 😂

Abin tausayi mutane tsoffi da mata da yara kowa ya nemi waya 'yar dondole sai dondola yatsu yake wai yana tara miliyoyi. 😥 Matasa a Jami'a ana ba su darasi su na dondola salula. Mata da yawa a gida sun rage kula da tarbiyyar yara sun dawo dondole yatsu. Tsofaffin da ya dace su rike lazimi sun fada harkar mayinin. Ko da shi ke su na yi wa sana'ar kirari iya girman wayanka iya burinka. 🤣 Mu yan Crypto mu na saurin fushi idan an soki sana'armu 😎 saboda hassada ake mana kar mu yi kudi ta hanyar Crypto. 🤣

Mai Rubutu:
Abubakar Malami
10/6/24.

24/05/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah ya yi wa Malam Muhammadu Abubakar Kafinta na garin Dadin Kowa rasuwa a yau Jumma'a a babban asibitin kwararru da ke Gombe (FTH). Za a yi jana'izarsa gobe da misalin karfe 8:00am na safe a masallancin Jumma'a na Bolari idan ilahu Ya amince. Marigayi mutum ne mai riko da addini da kyawawan dabi'u wanda ya karar da rayuwarsa wajen yi wa addini hidima.

Mu na fatan Allah Ya masa gafara da sauran mamatanmu musulmai. Allah Ya kyautata ta mu karshen!

~ Abubakar Malami

23/05/2024

HIRAR GWAMNA

A yammacin yau ne a ke sa ran mai girma Gwamna zai gabatar da hira da yan jaridu don tunawa da ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a tsawon shekaru biyar a kan karaga. Wannan tsari na hira da yan jaridu da gwamnoni ke yi wanda Malam Nasiru Elrufa'i na Kaduna ya sunnantar a shekarar 2016 tana cike da alfanu. Da za a sauya yan jaridun da s**a saba tambayoyi da an kara samun armashi wajen sauraren hirar Gwamna.

Mutane na fatan a tabo batun makomar Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kumo da wutan Dadin Kowa da aikin man fetur na Kolmani da sahihancin zaben kananan hukumomi a hirar Gwamna.

~ Abubakar Malami

14/05/2024

GANGARAN

Eh, Gangaran ne wanda ya fi Gwani kwarewa a fagen rubutu a duniyar ilmu na addini da na zamani. Tarun ilmi da basira da karfin ƙwaƙwalwa yasa wasu ke masa terere bisa manufarsu. Ina ruwan biri da gada, tun da zakaran da Rabbi Ya nufa da cara ko a na muzuru a na shaho sai ya yi. Su na jayayya da baiwar da ilahu ya yi tajallinta ga bawansa Pantami, bayan zuciyarsu ta na da yakinin masani yake na yankan shakku wanda ya riski matsayin Gangaran.

~ Abubakar Malami

20/04/2024

JAMI'AR LINCOLN

Tun a watan Maris na shekarar 2022 gwamnati ta sanya hannu tsakaninta da Jami'ar Lincoln ta kasar Malaysia don inganta Jami'ar kimiyya da fasaha da gwamnatin PDP ta gina a garin Kumo. Idan Jami'ar ta tabbata jihar za ta kara bunkasa ta fuskan ilmi da tattalin arziki. A halin yanzu an shafe shekaru biyu ba tare da an fara karatu ba, lamarin da ke bukatan sanin hakikanin halin da ake ciki kan shirin tabbatuwar Jami'ar ta Lincoln.

~ Abubakar Malami

16/04/2024

GANDUJE

Domin naman Sarki na bisa karaga, ba a hana ungulu gewaya. Hakan ce tasa tsiraru a gunduman Ganduje a karamar hukuman Dawakin Tofa ta jihar Kano dakatar da shugaban jam'iyyar ta kasa Abdullahi Umar Ganduje. Dakatarwan ke da wahala sai ga wata sabuwar sanarwa daga sama na wai ba za ta sabu ba bindiga a ruwa. Lamarin da ke k**a da wai kunama da ta harbi kasko, ta ce, “namijin duniya, ko motsi ba ka yi a batun Ganduje.

Shugabannin gunduma a karamar hukuman Etsako ta yamma ta jihar Edo sun taba dakatar da Adams Oshiomole lokacin da aka samu sabuwar dambarwa tsakaninsa da Gwamna Obasaki. Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ya fuskanci haka a gundumar Igyorov da ke karamar hukuman Gboko a jihar Benue. Hakan na alamta irin shu'umci da kujerar ke da shi a lamarin siyasa, ko da shi ke alamar rago, tana ga ‘daurin bante a dambarwan Ganduje.

Tun lokacin nada Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban jam'iyya, masana turabi na siyasa ke kallon akwai bukatar a dandale maganan zargin dala na Jaafar Jaafar gudun ka da a haifu a ragawa. Da alama shugabancin jama'iyya mai mulki za ta dauki sabon salo a daidai lokacin da talakawan kasa ke rayuwa hanu baka hanu kwarya. Babu shakka an bude sabon shafi na rikita-rikitan jam'iyya tun da ba a koyon karatu ran tukuri a batun korar Ganduje.

Mai Rubutu;
Abubakar Malami
16/4/24.

15/04/2024

ZAKIR DA PANTAMI

Manazarta na ganin Malam Zakir a matsayin mutumin da ke sahun gaba wajen samun baiwan karfin kwakwalwa da fahinta daga ilahu mai ilmi (Allah) a wannan karni musanman Anahiyar Asiya. Abin da da yawa daga cikin manazarta na ganin Pantami a matsayin wani kundi na ilmi Anahiyar Afurka. Akwai wasu kyawawan sifofi da s**a hada Malam Zakir da Malam Pantami.

1- Malaman addinin musulunci suke

2- Mahaddata kur'ani mai karamci suke

3- Masana kimiyyar zamani suke

4- Masana da rayuwarsu ke cike da albarka suke

5- Malamai masu fara'a da kyawawan dabi'u suke

6- Malamai da ilahu ya yi tajallin sunansu a wannan karni suke

7- Masoyan alheri ga al'umma suke

8- Ma'abota da'awa zuwa ga bautan Allah wahidi suke

9- Masoya juna masu manufa daya suke

10- Masana masu kaifin kwakwalwa suke

A Nahiyarmu ta Afurka idan ka dubi lamarin Malam Pantami za ka fahinci ya samu baiwan kaifin kwakwalwa da ke yawan tuno abu cikin hanzari. Lamarin kaifin kwakwalwa na Zakir a Nahiyar Asiya a bayyane ta ke ga masu bincike. Madallah da rayuwar Zakir da Pantami.

Mai Rubutu;
Abubakar Malami
15/4/2024.

Photos from Imam Abubakar Malami's post 11/04/2024

BARKA DA SALLAH

Abubakar Malami na yi wa al'umman musulmi barka da sallah. Allah Ya karba mana Ya maimaita mana.

~ Abubakar Malami

11/04/2024

~ Abubakar Malami

Want your school to be the top-listed School/college in Gombe?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Gombe