19/10/2024
MUKOMA ZAMAN KOTU NA RANAR 17/3/2022
QULLIN TUHUMAR SU NA UKU , BATUN AURAN DOLE ,
Malamin yace fadin shaidarsu na biyu, murtala kenan , sanda na tambayeshi ya fitar min da sadaki a cikin abinda yazo a hadisin βYA MAIDA YANCINTA SADAKIN TAβbayan da naja masa ayar da tace baβa sadaki saida kudi ko da wani abu na kudi, anan ya fada cewa ba wanda zai lazimtawa Annabi (S.A.W.) ga yadda zaiyi, wanda a zatonsu karyatawar da Imamu Malik yayi shi ya lazimtawa Annabi, hakan wanda ko kusa ba haka bane.
Muslim yayi babi wanda yake wajabta yin baiko a aure sunan babin βBABIN NEMAN IZININ BAZAWARA HAR SAI TA FURTA CEWA TA YARDA, ITA KUMA BUDURWA KO SHIRU TAYI AKA GANE YARDA SHIKENANβ shine hadisi na 1419 a Muslim kuma malik yayi kishin maβaiki ya musa wancan hadisin nima nace Annabi baiba.
Mu koma muslim hadisi na 1365 daga zuhairu bn harbin yace, ismaβil ya zantar dani yana nufin dan ulayyata daga Anas har inda sabitu yake tambayar Anas menene sadakin Safiyya? sai yace kanta shine sadakin ta, har saida s**a zama akan hanya, sannan aka gama yi mata kwalliya, sai tai masa budar kai a cikin wannan dare, sai Annabi ya wayi gari Ango.
Malam yace To a duk masu sharhi ba wanda ya iya fitar da baiko anan don bazai fitaba.
Sannan malam ya cigaba yace ga βAL MUHALLAβ na inb Hazbin Al Andalusi juzuβI na tara shafi na 101 yana Magana kan hadisin dai 1365 na muslim yana sharhinsa yace, Abu hanifa da laisu bn saβad sun ce bai halarta ba yancin kuyanga ya zama sadakin ta ba, sanna yazo a kasa wajen maida martani yace, wanna Magana ta limaman nan itace mafi wautar maganar da kunne ya jita,
Malam yace maimakon ya kawo dalilinsa na karyata wayan can limaman , da s**ace bazeyiwu Annabi yayi sadaki da yanci ba, kawai sai yace wannan s**a ne ga Maβaiki don haka sun fita daga musulunci, malam yace mafiya yawan wadanda s**ai wanna maganar zaluntarsu akai.
Ni kuma da nabi sai naga zaluntarsu kawai yayi don bai bada wasu hujjojiba, don inda s**ayi daban inda yayi daban, daga ciki wannan hadisi na wajabcin baiko a aure bai kawoshi ba har ya gama maganarsa.
Sannan hadisin nana Aisha a Muslim wanda take tabbatar da cewa Maβaiki ya bawa duk matansa sadaki yana nan a muslim hadisi 1426 yace Abu Salama yace na tambayi Aisha yaya sadakin maβaiki yake ga Matansa? Tace sadakinsa ga matansa shine uqiyya 12 da nashshi, sai ya tambayeta meye nashshi? Tace rabin Uqiya.
Malam ya cigaba da cewa lafazin da tace duk an bawa ko wacce wannan adadi ga hujjar a cikin βMUSANNAFβ na sanβani Malamin bukhari juzuβI na 6 shafi na 142 hadisi na 10448 ga lafazin β Manzon Allah (S.A.W.) ya yiwa duka matansa sadaki na Uqiya 12 da rabin Nashshi ( Dirham 500 kenan Jimla.
Hatta zuhuri sharri sikai mai kamar yadda sheda na farko ya fada, shima ya tabbatar da cewa anyi sadaki wanda da shine na gamsu Auren Annabi (S.A.W.) duk yayi sadaki.
Kai ba Nana Aisha kawai ba har sahabbai manya dukkansu sun tabbatar Annabi (S.A.W.) ya yiwa duka matansa sadaki wanda a cikinsu akwai wanda sun bawa maβaiki yayansu kamar sayyadina Umar dan kaddabi shima yace lallai Annabi ya bawa duka matansa sadaki wannan Magana tazo a βDABAKATUL KUBRAβ na ibn saβad Albasari mujalladi na 8 shafi na 128 a babin bayar da sadaki matan Annabi (S.A.W.) ya fara da hadisin Nana Aisha wanda na kawo yanzu sanna ya karo da na sayyadina Umar da asanidu har hudu, anan sai malalm ya karanto daya daga cikin Isnadan.
Sanna malam ya ci gaba, yace kamar yadda yake abune sananne cewar Sayyadina Umar yana kin tsadar sadaki , da ya samu cewar maβaiki yayi Aure ba sadaki da ya tabbatar wa da wani yayi hakan.
Sannan yayan gidan maβaiki acikin βDabakatul kubraβ sun tabbatar maβaiki ya bada sadaki ga dukkan matansa .
Kayyasa Aiki game kareka yan maja fa sundebo ruwan dahuwar Kansu , wallahi tall ah bilhil azimu wannan hadisin na Anas na cikin muslim 1365 karyane , dud duniya baai dan daya isa yatabbatar da wannan auran a hakkin maaiki ba ,yan uwa masu neman gaskiya kukasan ce damu ,zamu kawo muku yadda sheikh Abduljabbar yayi Karatu dalla dalla gameda yadda Annabi s a w ya auri nana safiyya akotu agaban alkali, kuma sarki yola yatambayi yan maja kunada tambaya ko s**a gameda wannan bayanin s**ai tsit, wallahi jamaa duk abunda zasu fada muku karya s**e wannan shine hakikar abunda yake faruwa akotu,
KAHFI WORLD MEDIA