20/03/2026
Sunnonin Sallar Eidul Fitr da Yakamata mu sani.
Yakai ɗan uwa mai albarka kayi ƙoƙarin domin dacewa da sunnar fiyayyen halitta Annabi Muhammad ﷺ gobe ranar Eidin Sallar Azumi ka lizimci waɗannan abubuwan domin samun ladar koyi da Annabi Muhammad ﷺ, gasu kamar hakan:
1⃣Wanka Domin Sallar Eid
(الموطأ للإمام مالک 432)
2⃣ Sanya turare, Sanya Tufafi masu kyau.
(المطالب العالیة 1:85)
3⃣Cin Abinci kafin Zuwa Sallar Eidi (Eidil Fitr)
( صحیح البخاری 953)
4⃣Tafiya Kasa Zuwa Eidi
(530 سنن الترمذی)
5⃣ Sauraron Khudubah bayan gama Sallar Eidi
( صحیح سنن ابن ماجه1073 )
6⃣Chanza Hanya yayin dawowa daga Sallar Eidi
(صحیح البخاری 986)
7⃣ Addu'o'in yayin Haduwa da mutane
" تقبل الله منا و منکم"
(مسند الإمام أحمد)
8⃣ Nuna farin ciki da Nishadi
(صحیح مسلم)
Domin samun lada daga Allah kuyi sharing ɗinsa domin ƴan uwa su amfana. Allah ya karɓa mana.
Rubutawa da gabatarwa
©️ Engr Aliyu Almustapha