Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe

Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe, Tutor/Teacher, Sheikh Modibbo Tukur Zawiyyah J/fari Quarters Gombe, .

14/02/2026
13/02/2026

Jumma'a Moobaraq 🌙

Assalamu Alaikum Warahmatullah,
Yau Jumu’a ce mai albarka. Mu yawaita salati ga Manzon Allah (SAW), mu sabunta niyyarmu, mu ƙara himma a aikin alkhairi.
Ramadan na karatowa watan ibada ne, watan Al-Qur’ani da kyautatawa. Mu fara shiri tun yanzu domin mu same shi cikin karfi da tsarkakakkiyar niyya.
Allahumma Ballighna Ramadan. 🤲

Photos from Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe's post 11/02/2026

Assalamualaikum.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!.
A madadin Zawiyyar Sheikh Modibbo Tukur Gombe da Iyalen sa, suna sanar da 'yan uwa za'ayi karatun Al-QUR'ANI da ADDU'AN uku (3).
Na daya daga cikin matan Sheikh Modibbo Tukur Gombe, wato Sayyada Fatima (Hajiyah Inna).
Mahaifiyar Mal. Muntaka Tukur da Mal. Abdurrahim M Tukur
Ranar Laraba 11/02/2026.
Karfe 04:30.
A gidan Sheikh Modibbo Tukur Gombe jekada fari Jankai.
Yah Allah ka jaddada rahama a gareta Alpharman Manzon SAW 🤲😥.
Allah ya bada ikon Halarta.

Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe

09/02/2026

INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN

﴿كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍ)

Cikin yarda da hukuncin Allah (SWT), muna sanar da ’yan’uwa Allah yakarbi daya daga cikin iyayenmu Sayyada Fatima Mahaifiyar Sayyadi Muntaka da Sayyadi Abdurrahim.

Za a yi jana’izarta:
📅 yau Litinin, 09 February 2026
📆 20 Sha’aban 1447H
📍 Zawiyar Modibbo Tukur, Jankai
⏰ Karfe 2:30 na rana

Allah yajikan ta da Rahma yadata da masoyinta Albarkan Manxon Allah SAW 🙏

Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe

28/11/2025

لو كانتِ الدنيا تدومُ لواحدٍ
لكانَ رسولُ اللهِ ﷺ حيًّا وباقيًا.

﴿ يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ ۝ ارْجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً ۝ فَادْخُلِي فِي عِبَادِي ۝ وَادْخُلِي جَنَّتِي ﴾

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ الْفَاتِحِ لِمَا أُغْلِقَ، وَالْخَاتِمِ لِمَا سَبَقَ، نَاصِرِ الْحَقِّ بِالْحَقِّ، وَالْهَادِي إِلَى صِرَاطِكَ الْمُسْتَقِيمِ، وَعَلَى آلِهِ حَقَّ قَدْرِهِ وَمِقْدَارِهِ الْعَظِيمِ.

21/10/2025

INNALILLAHI WAINNA ILAIR RAJIUN.

Allah Yayiwa Sayyada Halima sheikh Modibbo Tukur Gombe Rasuwa.

za'ayi Jana'iza Insha Allah kamar haka:-

Rana : Yau Talata 21/10/2025.

Lokaci: 02:30pm Na Rana.

Wuri: A Zangayar maulanmu sheikh Modibbo Tukur Yamma Da Gombe Division Gombe.

Allah yabada Ikon Halarta Ameen,

Duk wanda Baisamu Halartaba Muna Buqatar Adduarsa.

12/10/2025

Public Announcement

Modibbo Tukur College for Arabic and Islamic Studies (MOTCAIS) wishes to inform the general public that the sales of admission forms have commenced for:

JIS One

SS One

Forms are available at the school premises, located within Zawiyat Sheikh Modibbo Tukur, Gombe.

We warmly welcome all interested candidates who wish to pursue quality education in both Islamic and Western studies, with sound moral upbringing.

May Allah grant success to all applicants.
For Enquires:07033104047/08034237956

03/10/2025

Innalillahi waInna'alaihi raji'un

Allah Ubangiji Ya jaddada rahama ga Babban Shehinmu, Sheikh Alhaji Umar Bojude, wanda yau ya cika kwana 40 da wafatinsa. Allah Ya ba mu albarkarsa, Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Ameen.

30/09/2025

🎄🎄Happy Maulud 🎊🎉

Wasiyyar da Maulanmu Sheikh Mahmud (Khalifa) yayi Mana yayin Khatmar Maulidin Bana 2025

Yace Alhamdulillah Waton Ala'ayyi Halin Ina Muku Wasiyya da tsoron Allah, Bin Umurnin sa Taba-raka Wata'ala da Haninsa, Bin Umurnin Manzon Allah da Haninsa, Bin Umurnin Shehu Tijjani Shehu Ibrahim da Haninsu, da Sauran Sadatu, Kamar yanda Aka dauramu A kai Ayi Riqo da wannan.

Sannan Ayi Riqo da Fara'ilu da Nawa-filu da Ainihin Sunan Kamar yanda Shehu yake cewa, Sallan nan a tabbatar Ana yinta cikin Lokaci da Kyauta ta Rukunnanta Shine tsaida Sallah, Sannan Lazimi da Wazifa Zikirin Juma'a Akan lokaci, Wazifa Zikirin Juma'a A jam'i Ayi Iya kacin Koqarin Kiyaye su, Dan Lazimi da Wazifa Zikirin jumma'a Sune Sirrin Dariqar nan Sune Kaman foundation Su zaka taka Kaje duk In da Kake Son Zuwa, Wazifa Cikin Jama'a Shehu yace In da Uzuri Amma Uzuri In babu Uzuri ba'ama Uzuri ba ba'a so Ayi Kwana 3 Ba'ayita A Jam'i ba Annabi S. A. W Yace Duk Wanda yabar Jumma'a 3 Tawuce sa To Yajefar da Igiya ta Musulunci Tabayan Bayan Ka To Haka Shehu yafada A Wazifa ma duk Mai Wasa da ita Zai Jefar da Dariqarsa Abayansa Alura da Wannan.

To Sai Mu'amala A kyautata Mu'amala tsakanin Al'umma Addinin nan namu Addini ne na tausayi da tausayawa juna a taimaka wa juna, Addini ne Na'ainihin hakuri Ayi hakuri da Juna Ayi Hakuri Ayi Hakuri, Hakuri Shine Ko mai (Allah yace Watawa Saubissabari Watawa Saubilhaqqi).

Allah ya taimakemu yamana Jagora Muna Godewa kowa da kowa Al'umma daidai ku kowa da Temakon da yayi Masubada Shawara da Wanda s**a bada karfin su da Wanda Sukaba da Dukiyar su, Muna Yiwa kowa Fatan Alkairi Subhanahu Wata'ala Yabiya Buqata Yakara Arziqi da Wadata ya Kara Zumunta Al barkan Manzo Sallallahu Alaihi wasallam.

Magabatanmu Allah ya jiqansu da Rahma yakara Kusan tasu da Manzon S. A W, Mun Godewa Jama'a Mun Godewa Jama'a Allah yabiya Buqatu.

Sheikh Modibbo Tukur Gombe Zawiyya.
Happy Maulud 2025@1500
Khalifa Mahmoud Sheikh Modibbo Tukur Gombe
Ismail Abubakar
Dahiru Mahmoud Modibbo

13/09/2024

Gayyatar Karatun Maulidi daga Zawiyar Sheikh Modibbo Tukur Gombe Wanda za'a gabatar ranar Lahdi 15/09/2024

Want your school to be the top-listed School/college?

Website