25/08/2025
Tsohon shugaban Nijeriya Janar Yakubu Gowon da 'ya'yansa Ibrahim (wanda saboda kaunarsa da Shiekh Ibrahim Inyass ya rada masa sunan), da Saratu. Su na tafiya a wani t**i a birnin London, ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 1975, yayin gudun hijirarsa a Birtaniya.
25/08/2025
Hoton Tijjani Wanda Akafi Sani Da (Kal'ana) Dan Gidan Maitatsine, an Dauki Hoton 1979.
Dalilin da yasa akeyi masa lakabi da Kal'ana, shi ne saboda (dan mallam yaki halin malam), a maimakon ya tsaya yayi karatu ya gaji mahaifinsa, sam shi wannan ba shi ne a gabansa ba, domin kuwa shi bariki ya sanya a gaba, har yana cewa idan malam ya mutu, sai ya tarwatsa almajiransa, shi ne yasa wasu sukeyi masa lakabi da (Kal'ana).
Maitatsine ya haifi yara da yawa, amma dukkan su ba sa wuce shekara shida a duniya Allah ya ke dauke ransu, Tijjani shi ne dansa daya, don hakan ya ke matukar sonsa sosai don haka ba abin da Kal’ana zai nema ya rasa, kudi ne ko suttura, sai wadda ya ga dama zai sa.
Hakan ta sa yaron ya fara lalacewa, shi ne bariki shaye-shayen giya nema mata da sauran kayan maye iri-iri. Maitatsine ya sangarta kal’ana, har ta kai ta kawo duk dan da aka sayawa keke sai Tijjani ya je ya samu babansa maitatsine ya ce an saya wa wane keke shi kuma maitatsine sai ya ce, ni kuma gobe babur zan saya maka, kuma ya saya masa babura iri-iri saboda gata da izzar kudi.
To ana wannan yanayi ne wata rana ya debi abokansa, s**a tafi yawon barikinsu da s**a saba, sai s**a tsokani wani kurma wanda aka fi sani da suna Sa’idu, sai wannan kurma ya buga masa wuka a wuya, ganin haka s**a dauko shi s**a kawo shi gida inda Maitatsine ya ganshi hankalinsa ya tashi ya ce a kai shi asibitin Murtala. Bayan an kai shi bai jima ba Allah ya dauki ransa.
Muhammad Cisse
25/07/2025
Wasu iyaye Mata Tare da Ya'yansu a Goye, a kusa da Masallacin Juma'a na birnin Kano a shekarar 1958 Yau Shekaru Yau Shekaru (67) Kenan.
Muhammad cisse.
25/07/2025
Ya Suma Saboda Farin Ciki: a lokacin da jami’an kiwon lafiya (Nurse), s**a gabatar masa da yan' tagwayen (Ya'ya Uku) da matarsa ta haifa masa a birnin New York na kasar Amurka 1946.
Muhammad cisse.
25/07/2025
ZIKIRIN SAFE DA MARAICE
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أَُشْهِدُكَ، وَأُشْهِدُ حَمَلَـةَ عَرْشِكَ، وَمَلائِكَتِكَ، وَجَمِيعَ خَلْقِكَ، أَنَّكَ أَنْتَ اللهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ. أَرْبَعُ مَرَّاتٍ
Allahumma innee asbahtu oshhiduk, wa-oshhidu hamalata 'arshik, wamala-ikatak, wajamee'a khalqik, annaka antal-lahu la ilaha illa ant, wahdaka la shareeka lak, wa-anna Muhammadan 'abduka warasooluka.
Ya Allah! Ni na wayi gari ina shaidawa gare Ka, kuma ina shaidawa ga (Mala'iku) masu daukan al'arshinka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai kadai, da babu abokin tarayya a gare Ka, kuma Muhammadu bawanka ne kuma Manzonka ne. (sau hudu).
Wanda ya karanta kamar yadda aka ce, Allah zai 'yanta shi daga wuta.
O Allah, I have entered a new morning and call upon You and upon the bearers of Your Throne, upon Your angels and all creation to bear witness that surely You are Allah, there is none worthy of worship but You alone. You have no partners, and that Muhammad is Your slave and Your Messenger
To be recited four times
The Prophet (SallaAllahu ‘alayhi wasallam) said that whoever recites this supplication in the morning, their sins from that day will be forgiven, and whoever recites it in the evening, their sins from that evening will be forgiven.
In another narration, the Prophet (SallaAllahu ‘alayhi wasallam) said that whoever recites this supplication once in the morning or evening, Allah will free a quarter of this person from Hellfire. Whoever recites it twice, Allah will free a half this person.
Whoever recites it three times, Allah will free three quarters of this person, and whoever recites it four times, Allah will free the whole of this person from Hellfire.
Muhammad cisse.
25/07/2025
Gari ya waye a birnin Maiduguri jihar Borno Najeriya bisa yanayi 23 a ma'aunin Celsius.
Muhammad cisse.
18/07/2025
Yadda ake yin maganin ciwon kai a karni na 18.
Muhammad cisse.