Alhaji Yusuf Pantami Islamic Center Masjidut-taqwa, New GRA, Gombe

Alhaji Yusuf Pantami Islamic Center Masjidut-taqwa, New GRA, Gombe

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Alhaji Yusuf Pantami Islamic Center Masjidut-taqwa, New GRA, Gombe, Education Website, Alabura S. Kudi Crescent, New GRA, Gombe.

31/07/2026

Huduba daga masallacin Masjidittaqwa New g r a Gombe

24/07/2026

Mudadara Mai takin kiyayi ran Dan Adam Mai gabatarwa sheikh haruna Muhammad tukur

24/07/2026

Huduba daga masallacin Masjidittaqwa New g r a Gombe Mai gabatarwa sheikh musa Dawood

18/07/2026

Karatun littafin Minhajul Muslim malan hamma Adama Umar

26/06/2026

Huduba Mai Taken: "Haƙuri da Girman Haƙuri a Wajen Allah"
Mai gabatarwa: Sheikh Haruna Muhammad Tukur I

19/06/2026

HUDUBA: Muhimmancin Sabuwar Shekarar Musulunci 1448AH
Khutbah ta Farko
الحمد لله رب العالمين، نحمده ونستعينه ونستغفره ونتوب إليه، ونعوذ بالله من شرور أنفسنا ومن سيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له ومن يضلل فلا هادي له، وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له، وأشهد أن محمدًا عبده ورسوله.
Ya ku bayin Allah! Ina yi wa kaina da ku wasiyyar tsoron Allah, domin tsoron Allah shi ne mafificin guzuri.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ﴾
Ya ku Musulmi, mun shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH, wannan wata dama ce ta yin nazari a kan rayuwarmu, mu duba abin da muka aikata a shekarar da ta gabata, mu gode wa Allah bisa ni'imominSa, mu kuma tuba daga kura-kuranmu.
Hijirar Annabi ﷺ daga Makkah zuwa Madinah ta koyar da mu:
Haƙuri da juriya a kan addini.
Dogaro ga Allah a cikin al'amura.
Sadaukarwa domin ɗaukakar Musulunci.
Muhimmancin haɗin kai da ƙaunar juna.
Sabuwar shekara ba wai lokacin shagulgula kawai ba ne, lokaci ne na:
Tuba ta gaskiya.
Yawaita ibada.
Kyautata alaƙa da iyaye da makwabta.
Neman ilimi da aikata alheri.
Allah Ya ce:
﴿فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ﴾
Ma'ana: "Ku gudu zuwa ga Allah."
Khutbah ta Biyu
الحمد لله حمدًا كثيرًا طيبًا مباركًا فيه، وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له، وأشهد أن محمدًا عبده ورسوله.
Ya ku bayin Allah, ku yi anfani da wannan sabuwar shekara wajen gyara halaye da kusantar Allah. Ku yawaita azumin nafila, karatun Alƙur'ani, zikiri da sadaƙa.
Mu yi addu'a:
اللهم اجعل عام ١٤٤٨ هـ عام خير وبركة وأمن وإيمان، اللهم أصلح أحوال المسلمين في كل مكان، وانصر الإسلام والمسلمين، واحفظ بلادنا من الفتن ما ظهر منها وما بطن.
اللهم اغفر لنا ولوالدينا ولجميع المسلمين الأحياء منهم والميتين.
عباد الله، إن الله يأمر بالعدل والإحسان وإيتاء ذي القربى وينهى عن الفحشاء والمنكر والبغي يعظكم لعلكم تذكرون.
Aqimis-Salah.
Allah Ya sanya shekarar 1448AH ta zama shekarar alheri, zaman lafiya da ɗaukakar Musulunci. Amin.

18/03/2026

Insha Allahu za'a tsaida sallah idi karfe 7:30 a Masjid Ibadurrahman New GRA Gombe yamma da makarantar Pen resource secondary.

Wadda Sheikh Adamu Ardo shine zaija sallah insha Allahu.

Allah ya bada ikon halarta ameen.

10/03/2026

Ramadan tafseer day 21 Ramadan tafseer day 21 prof Muhammad Kabir yunus Masjidittaqwa New g r a Gombe

26/02/2026

Ramadan tafseer day 09 prof m k yunus Masjidittaqwa New g r a Gombe

Want your school to be the top-listed School/college in Gombe?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Alabura S. Kudi Crescent, New GRA
Gombe